Chapter 84
Chapter 84
ke kallo ka ke fad'a ma haka? Ko dan ka na ganin a waya ne shine ya ba ka damar fad'a min abin da ka ga dama? Lallai wuyan ka ya isa yanka Nura, har ni za ka bud'a baki ka aibata matata a gaba na a dodon kunnuwa na, to nagode, kuma ka yi hak'uri idan ran ka ya b'ace saboda kiran da na ma ka, ni dama ba aikin ka zanyi ba, na ce ka zo ne dan na baka kud'in da za ka fara shirye-shiryen bikin ka tunda an riga da an gama magana, amma tunda har ka ci mutuncin matata a gaba na ba tare da fargaba ba, to na fasa sai ka je ka samu malam saiya ma ka komai, ko kuma ka je ka fad'awa wacce ta sanya aka nemo ma ka auren ka ga saita d'auki nauyin komai." Ya na fad'a ya kashe wayar ya jefa kan kujera, zaune ta yi ta na kallon shi tace "Ya dai babban mutum na ji ka na waya haka kamar ka na fad'a? Kai da wa ne haka?" Cikin fusata yace "Ni da wannan banzan Nura fa, wai har ni zai kalli tsabar ido na ya na fad'a min magana har ya na ci mi ki mutunci, amma ba laifin shi bane laifi na ne da na sakar mu su fuska har su ke samun damar fad'a min abin da duk ya fito bakin su." Cikin ladabi tace "To me yace ma ka?" "Ki barshi kawai, ban san tunawa." Matsowa ta yi kusa da shi ta b'alle mab'allin rigar shi ta sa hannu ta na shafa k'irjin shi ta na fad'in "Na fi ka sanin cewa yan uwan ka ba sa so na, musamman yanzu da aunty Khadija ba ta gidan nan, wallahi gaba d'aya haushi na suke ji, gani su ke kawai laifi na ne ni ce silar barin ta gidan, amma ka sani ba zan tab'a damuwa da hakan ba in dai har ka na tare da ni." Rumgume ta ya yi yace "Kar ki damu Mummyn beby, babu abin da zai raba ni da ke saboda ina bala'in son ki sosai." Nura kam shi ma cikin hushi ya aje wayar shi ya ci gaba da aikin da ke gaban shi ya na balbala masifa shima, bai damu ba dan yace ba zai bashi gudummuwa ba, dan dama a shirye ya ke kafin ma ya fara maganar auren, dan haka ya yi niyyar yi wa kan shi komai ba tare da jiran taimakon wani ba, sunyi mai wuyar tunda sun nemo mi shi auren. Har ya gama abin da ya ke ya dawo gida kowa bai fad'awa abin da ya faru ba, dan Nura mutum ne mai zuciya da kuma rik'o sosai, wannan abun da ya faru ko da an yafi juna zaiyi wuya ya d'ora idon shi akan Usman ba tare da ya tuna wannan ranar ba, uwa uba kuma Haseenah da ya ke da tabbacin ita ce silar faruwar komai, har ya yi wanka ya ci abinci zai fita Hajia tace "Wai kai ya ku ka yi da Fodio da ka je gidan?" Fuska a had'e yace "Ba komai Hajia, dama wani sak'o ne zai bani na kai wani wurin." "To ai ni na d'auka ko maganar auren ta ka ce za ku tattauna." Hanyar fita ya nufa ya na fad'in "A'a ba ita bace." Har ya kusa kaiwa k'ofar fita ta sake cewa "Zo ka kira min shi a waya, ni tun yamma na ke kira ba na gane me ake fad'a, kuma har yanzu bai shigo gidan ba har dare ya yi." Dawowa ya yi ya karb'i wayar ya danna kiran lambar Usman ba tare da yace komai ba, wayar na k'ara a lokacin amma ba'a d'auka ba. Manne suke da juna basu rabu ba, sai dai ta samo mu su abu su tab'a kawai su yi sallah idan lokacin ya yi, mai gadi bawan Allah sam sun ma manta da a al'amarin shi bare a aika mi shi da abinci, sai dai ya siyo kawai ya ci amma ran shi bai mi shi dad'i ba, a haka har dare ya riske su Usman sai amsa waya ya ke musamman abokan shi na rashin ganin shi yau da ba ayi ba a waje, wani ikon Allah kuma saida su ka yi shirin kwanciya sai ciwon mara ya hana Haseenah sukuni, cikin rud'ewa ya d'auke ta su ka nufi asibitin da aka fara duba ta tun farkon rashin lafiyar ta, suna gaban likita lokacin kiran Hajia ya shigo wayar shi, kasa d'auka ya yi ya mayar da hankali kan abin da likitan ke fad'a cewa ta daina duk wani aikin wahala, in fa ba haka ba zata iya yin b'arin cikin nan, haka aka sallamo su suka dawo aka ce ta ci gaba da shan magungunan da aka bata na farko, tun cikin mota yake fad'in "Wallahi ba za ki k'ara dafa ko ruwan zafi ba a gidan nan, ke baki san yanda na ke son abin da ke cikin nan naki ba, amma bari cikin ki ya k'ara k'wari wallahi k'asar waje zan fita da ke ki haihu acan, dan ni ban ma gamsu da likitocin nan d'in ba, daga yanzu kuma zuwa lokacin zan samo mi ki yar aiki ko kuma Aziza ta dawo nan ta dinga aikin gidan." Ita dai ta na sauraren shi dafe da marar ta har suka isa gida, da kan shi ya canza mata kaya ya kwantar da ita ya bata magani tasha sannan ya rufe ta da zanin rufa, k'ura mata ido ya yi ya na kallo har bacci ya d'auke ta, wani bala'in tausayinta da kuma son ta ne ke k'ara gyauraya da jinin shi, ta yanda yake jin kamar ya mayar da cikin jikin shi saboda ta samu sauk'i, ya jima zaune kafin ya fito da wayar shi ya ga kiran Hajia, fita ya yi falo ya sake maida kira cikin sa'a kuma Hajia ta d'auka, a d'an kakkauce suka gaisa kafin ta tambaye shi ya yi aiki da magungunan nan, "Sosai ma Hajia, ai duk na yi aikin da su." Cewar Usman fa, tambayar shi ta kuma yi me ya hana shi zuwa yau? Malam ma ya bayar da ruwan addu'a a abashi amma bai zo ba, haka kawai ya tsinci kanshi ya sharara k'arya ta hanyar fad'i "Hajia ai wani abu ne ya d'an taso da ya sa dole sai da na je *katsina*, kuma sai bayan isha'i na dawo ina zuwa na gaji sosai kawai na d'an kwanta, yanzu ma ina bacci ne na farka sai kuma na ga kiran ku." Cike da gamsuwa Hajia tace "Ah to shikenan, saida safe, Allah hutar da gajiya." "Ameen Hajia, nagode, saida safen ku." Ya na fad'a ya kashe wayar ya shiga uwar d'akin shi ya canza kaya kafin ya dawo d'akin Haseenah. Washe gari da safe kafin malam ya fita saida ya sake bayar da ruwan addu'a, Hajia dai ba ta ma fad'a mi shi na jiya na nan ba kawai ta amsa, sai kuma akayi sa'a Usman ya zo gidan, shi ma kuma ya zo ne da maganar Aziza ta koma can da zama ta na taya ta aiki,
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117