Chapter 71
Chapter 71
Cewar Khadija, ta na shiga su ka gaisa kafin ta tambaye ta sun ci abinci ai? Eh, shine amsa da su ka bata, kallon Aziza ta yi tace "Ke ki zauna gidan to, ke sai ki tashi mu koma asibitin." Dama a shirye take, hijabi kawai ta saka suka fito tare da Hajia da ke rik'e da katin likita a hannu, "Hajia har kun fito? Gida za ku tafi ne?" "A'a." Ta fad'a kai tsaye, ganin Haseenah tare da ita ya bata mamaki, musamman da taga ta na gaba ta na binta, "Hajia lafiya kuwa? Ko ba ta da lafiya ne?" Sai kawai Hajia ta ji haushin wannan tambayar, bud'ar bakinta cewa ta yi "A'a lafiyar ta k'alau, akwai in da za mu ne." Da ido kawai ta bisu ta na mamakin kamuwar Hajia ita ma da wannan cuta ta 'ya'yan ta, ido kawai ta zuba mu su har suka dawo lokacin ta na madafa ta na girki, lokacin ne kuma 'yan uwan Haseenah da ma 'yan uwan Usman d'in suka fara zuwa ganin ta, ita dai ta na kammala girki ta fitar mu su ta bayar aka kai, sai dai ta yi niyyar ko ciwon ajali ne Haseenah keyi ba za ta je ta duba ta cikin mutane, tunda ta lura b'oyewa ake ba asa ta sani saboda tunanin wani abu. Da yamma Haseenah ta karb'i girki, amma 'yan uwan ta ne suka shigar madafar suka yi yanda su ke so, sai dare su ka bar gidan Khadija ta shiga dan samun abin da za su ci, yanda ta ga madafar abin ya bata mamaki da dariya, saida ta gyara ta sosai kafin ta samu abin da za su ci, ko da su ka kammala suka kwanta abin su. *Hummmmmmmmmm.* Tunda asuba Khadija ta shirya tare da Bilal suka yi karin kumallo, sai da ta kira Usman tace ta na si ta aje Bilal a gida, amma sai yace "Me ye haka Khadija? Gidan nan fa akwai mutane, ya ki ke so ki nunawa yaron banbanci a zahirance." "Shikenan ka yi hak'uri." Ta na fad'a ta kashe wayar ita ma, zuwa k'arfe *07:15* suka fito, saida su ka shiga d'akin Haseenah da sallama suna falo ita da Aziza ita ma ta na shiri, "Antashi lafiya?" "K'alau." Cewar Haseenah, Aziza ce tace "Ina kwana." "Lau." Cewar Khadija, kallon su ta yi tace "Dama zan tafi Tessaoua ne wajen biki, na kulle d'aki na, ga kayan Bilal idan an dawo da shi sai ya canza wannan, sai na dawo." Hannun shi ta kama su ka fita, Aziza kam cewa ta yi "Ka ji matar nan sai ka ce akwai bawanta anan d'in." "Ke kuwa miye a ciki? Bilal ai d'an mu duka, Allah dai ya kaita lafiya." Saida ta gama shiri suka karya tace"Idan na tafi zan tsaya gida na wuni, na san dai saida dare ko na dawo gida." Da haka su ka yi sallama ita ma ta tafi makaranta, Khadija ma ko da suka isa Ashir ne ya kai su makarantar duka, su kuma zuwa tara Naseer ya d'auke su suka tunkari *Tessaoua*. *Me kuma zai faru yanzun?* 16/02/2020 Γ 13:20 - πππ: ππππππππππ *KALLON KITSE* _(Ake wa rogo)_ ππππππππππ _SAMIRA HAROUNA_ *Litattafan marubuciyar* *1* _KAUSSAR_ *2* _D'AUKAR FANSA_ *3* _BA SO BANE_ *4* _AUREN HAD'I_ *5* _SANIN MASOYI_ *6* _JIHADI_ *7* _K'ANGIN RAYUWA_ *8* _ITACE K'ADDARARMU_ *9* _KAWU NA NE_ *10* _MAATA_ *11* _KALLON KITSE..._ *SADAUKARWA GA* _MATAN FARKO_ π§πΌ *(UWAYEN GIDA)* πΈπ¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S* _(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_π€π€ ```Fatan alkairi masoya``` _Bismillahir rahamanir rahim_ *27* Sha biyu Ashir ya d'auko su Bilal, suna hanya Khadija ta kira shi su ka gaisa, gida aka aje shi kafin suka wuce, k'ofa mai gadi ya bud'e masa ya na fad'in "K'aramin Alhaji har an taso?" "Eh, ya aiki?" Ya fad'a da fara'a, shi ma da fara'a ya mayar masa da "Alhamdulillah." Ciki ya shiga kai tsaye kuma b'angaren Haseenah ya wuce tunda yau ita ce maman shi, sallama ya dinga rabkawa amma ya ji shiru, saida ya bud'a k'ofar falon ya shiga kad'ai ya ga takalma alamar bak'i amma kuma ba kowa a falon, kujera ya samu ya zauna ya ciro wayar shi ya na dannawa da chocolat a hannu ya na sha, minti talatin ya d'auka a falon sai dariya da shewar su Haseenah ita da Zeinab wacce daga makaranta take ita ma ta ratse nan, tashi ta yi ya nufi d'akin na ta ya k'wank'wasa k'ofa duk da bud'e take, shiru su ka yi kafin tace "Waye?" A hankali ya yaye labulen ya kalle ta yace "Aunty sannu, ni ne." Fuska a d'aure tace "To, yaushe ka shigo gidan?" "Na jima zaune a falo, yanzu ma dan na ce ku bani kaya na ne zan canza wannan." "Ka je idan na fito zan baka kayan." Ta fad'a ta na mayar da hankalin ta kan Zeinab, har ya juya zai fita tace "Kai zo nan." Dawowa ya yi jiki a sanyaye ya tsaya gaban ta, kud'i ta mik'o mi shi tace "Ka wuce maza kaje ka siyo min katin waya na airtel." "To." Ya fad'a ya na karb'ar kud'in ya fice, ta k'aramar k'ofa ya bi zai fice mai gadi yace "K'aramin Alhaji fita za ayi?" "Eh." Kawai ya fad'a a tak'aice ya na zura duka hannayen shi biyu cikin aljihun doguwar rigar shaddar shi wacce ka na gani kasan ta ji kud'i, a k'afa ya taka har ya iso bakin titi, ya jima tsaye kafin ya samu ya tsallaka saboda akwai ababen hawa sosai a wajen musamman da ya zama ranar farko ta komawa makaranta, siyowa ya yi ya dawo gidan ya kawo mata, falo ya dawo ya zauna amma bai jima ba aka fara kiran sallah, tashi ya yi ya fita a panpo na daf da shigowa gidan ya yi alwala ya tafi masallaci, daya dawo wajen mai gadi ya zauna shi ya na sauraren redio shi kuma ya na kallon hanya, tsawon lokaci ya d'auka nan zaune kafin ya ji cikin shi na neman agaji, cikin gidan ya koma ya samu su Haseenah har yanzu a d'aki amma su na cin soyayyen k'wai da indomie, ga lemu a gefe suna korawa mai sanyi, cikin muryar tausayi yace "Aunty abi..." Kallon da ta ma sa ne ya sa ya yi shiru, Bilal yaro ne miskili da bai cika magana ba, in kaji yawan maganar sa to da iyayen sa ne idan suka had'u, jin ya yi shiru ya sa tace "Me ye kuma? Kayan ka na ce ka jira ni na tashi sai na d'auko ma ka, ka gansu can gefen gado, banyi niyyar tashi ba yanzun." Juyowa ya yi ya sake fitowa daga d'akin, Zeinab ce tace "Kin bashi abincin shi?" "Wannan d'in?" Ta nuna Bilal da ya fita da yatsa, d'orawa ta yi da "Ai munafiki ne da ki ke ganin shi kamar uwar shi, ba sa cin abinci na fa, yanzu in d'auka in bashi wani abu ya faru ace ni ce, yanda duk na ke k'ok'arin jingina mata laifukan nan ai kinga kashina ya bushe, kuma wallahi ni har ga Allah ma na manta da ya na gidan." Da haka su ka ci gaba da hirar su Bilal kuma
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117