Chapter 115
Chapter 115
ki ke kema?" "Lafiya lau, me ki ke anan?" Saida na b'ata rai na ce "Abin da ki ke yi." *Adam* ne yace "Daga tambayar arzik'i malama sai abu ya zama na tsiya." Hararan shi na yi na ce "Kai ni rufe min baki dallah ban sa da kai ba." "Ke ni ki ke fad'awa haka?" Ya fad'a a hassale, ni ma a hassalen na fad'a "Eh anyi d'in, me za ka yi?" Tasowa ya yi ya nufo kaina amma ban gusa daga in da na ke ba, saida ya tsaya gaba na ya nuna ni da yatsa zaiyi magana na ga an rik'e hannunshi daga baya ance "Haba kai kuwa Adam, aunty Meera ce fa, ba ka gae ta bane?" Sai lokacin na ga mai magana ashe *Marwan* (jarumin littafin *Kawu na ne*) ne, huci ya yi ya sauke hannun shi ya koma mazaunin shi, har ya zauna a kalli Falmata na ce "Fati wai ina d'an uwan ku mahaukaci?" Cike da jimami tace "Ki bari kawai aunty Meera, har yanzu ya na can babu sauk'i, wallahi duk ya sauya ya zama mahaukacin gaske." Tab'e baki na yi karo na farko da na ce "Allah ya yaye mi shi, *Fadjimata* kuma Allah ya mata rahama." "Ameen." Ta fad'a ta na mayar da kallonta gaban ta, sai lokacin na kalli Marwan na ce "Marwan ina aunty na take?" Da yatsa kawai ya min ishara zuwa bayana, ina juyawa na ga *Wafa'atu* bayana da tulelen cikinta masha Allah, da farin ciki na mik'e na rumgume ta na ce "Aunty Wafa'atu ashe Allah ya nufa." Ita ma da farin ciki tace " allah ya nufa Meera, addu'ar ki data fan's d'in ki ta same mu har inda muke, gashi yanzu Allah ya sa nima ina d'auke da cikin wata bakwai." "Kai to Allah ya raba lafiya aunty wafa'atu." Da "Ameen." Suka amsa su dukan su, sai lokacin Wafa'atu tace min "Amma me ki ke yi anan? Ke ma Khadija ce ta gayyace ki." Raina ne ya b'ace da tambayar sai kawai na yi gaba na bar su tsaye, ina cikin tafiya naji anyi magana cikin shagwab'a ance "Aunty Meera shine ko ganin mu ma ba kya yi." Juyowa na yi sai kuwa naga *Raheenat* (jarumar littafin *K'angin rayuwa*) ce, saida na gama kallon mutanen da ke tare da ita, ita da *Sameera* suna manne da juna haka ma *Abdul hakeem* da *Sadiq* suna jone sai tattaunawa suke, matsawa na yi dan mu gaisa amma Abdul hakeem sai cewa ya yi "Ke me ya kawo ki nan?" Baki bud'e na ce "Abdul hakeem yaushe ka zama haka kuma? A sani na dai ka na da taushin zuciya." "Sanin baya ki ka min, ai yanzu abin ba sauk'i, dan haka b'ace min da gani kafin ran ki ya b'ace." Yanda ya ke maganar ya sa na tsora ta na juya zan tafi Sameera tace "Haba takwarata, yaushe ki ka zama mai tsoro ne haka har da wannan zai tsorata ki." Abdul hakeem ne ya kalli Sadiq yace " aboki na ka sa matar nan taka ta yi shiru kafin na fitar mata da jini a baki." Kallon Sadiq Sameera ta yi tace "To sa na yi shiru d'in, ina jira." Wuk'i-wuk'i Sadiq ya yi da ido kafin ya kalli Abdul yace "Aboki na ka yi hak'uri, ba zan iya ma ka komai ba gaskiya, wannan matar da ka ke gani ina tsoron bala'in ta." Wata dariya Sameera da Raheenah su ka yi harda tapa hannu, ni kam dariya na yi na yi kafin na ce "Wai ina yara na ne?" "Suna gida." Cewar Raheenat, juyawa na yi na ce "Sai anjiman ku." Kallon Sadiq na yi na ce "Ka gaishe min da bazawarar nan taka." Waro ido ya yi ya kalle ni ya kalli Sameera, tasowa yayi zai min magana sai kawai takwara ta jawo rigarshi ya koma ya zauna tace "Dan Allah ya toni asirinka shine za ka bud'e mata ido." Abdul ne ya kalle ni yace "Kedai anyi guba wallahi, to yanzu dad'in me ki ka ji?" Kallonshi na yi na ce "Ka mantabi guba ce lokacik da ka ke sawa ina rubuta labarin soyayyarka da sabuwar budurwarka." Kallon shi Raheenat ta yi ,dariya na yi na wuce gaba ina ganin bala'i ya b'arke tsakanin Sadiq da Sameera, Raheenah da Abdul dan fa ita ta yarda bazawara yake nema tunda a ganinta ina bibiyar rayuwar mutane, ta teburin da Adam ke zaune na wuce nan ma cewa na yi ya gaishe da budurwar shi, a tak'aice saida na bi duka ma'auratan d'aya bayan d'aya ina hura mu su wuta, kuma babu wacce ba ta yarda ba saboda ganin ba zan fad'a mu su abinda ba haka bane, kafin ka ce me wajen taron ya fara d'aukar gumi saboda muryoyin dake tashi sama, musamman Kaussar da Khairat da Sameera ta Abbbas, sosai suka rufe ido wai ana cin amanarsu, da dai abin ya k'i sauk'i sai gashi ina niyyar sulalewa na bar wurin na ji ance "Aunty Meera barka." Ina juyowa da sauri naga teburin cike da jaruman littafin *Aure*, da farin ciki na k'arasa muka gaisa kafin na kalli matan na ce "Ina yaran?" *Fatima* ce tace "Suna gida aunty Meera." Sai *Rauda* da tace "Ai sun fara wayo yanzu." Kallon Laure nayi da kanta ke k'asa duk take jin ta a takure, murmushi nayi na ce "Lauratu sarauniyar kunya, to Allah ya mayar da ku gida lafiya, ni na yi gaba wajen nan ba zai zaunu gare ni ba." "Me ya sa?" Cewar *Iro*, kallon shi na yi kafin na ce wani abu *Siryanu* yace "Akwai bala'in data had'a tunda kaji haka." *Imam* ne yace "Ko kuma tsokana ba, kasan Meeran mu da tsokana fa, watak'ila akwai wanda ta harzuk'a." Ban tsaya saurarensu ba na fece ba su ma san da tafiya ta ba sai gani sukayi bana wajen. 😂😂😂😂😂 Ina shirin hawa adaidaita sahu na ji an shak'o hijabina na dawo baya, wazan gani in ba Umar faruk ba da hijabi na a hannu, Saif da Marwan sune masu sanyin ciki sune suka ce ya sake min hijabi tunda ni ma fa ba kara zube ni ke ba ina da aure, saki na ya yi amma Abbas yace "Wallahi ko kije ki fad'a mu su k'arya ki ke ko kuma mu kwana anan mu da ke." Ahmad ne yace "Ai ba maganar mu kwana anan bane, magana ce ta muje gidanta a matsayin samarinta ma su son ta." 😂 *Ahmad ko bala'i* Jin haka ya sa na ce su yi hak'uri mu tafi na fad'a mu su gaskiya dan ina son *beby na* ni ma, haka suka tasoni a gaba na zo na fad'a mu su kawai dan raha ne, saida magana ta fara lafawa sai kawai muryar Usman naji yace "Abokai ku taimaka ku tafar min da matar nan dan Allah, dan nima ta d'an fara damu na, sam bata bari mutum ya yi sirri da matarsa." Murgud'a masa baki na yi na ce " To babu in da zanje sai na k'arashe labarin har k'arshe sannan." Cikin fad'a Usman yace "To zan gani idan gidanki ne ko nawa." "Gidanka ne amma babu in da zata je har sai
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117