Skip to content

Chapter 111

Chapter 111

Kallon Kitse Book One Complete Hausa Novels 1,200 words 0 views Progress saved
Download Book

baya na ke fargaba da shakkun fad'a mi ki, ki yi hak'uri ko da hakan zai b'ata mi ki rai, kinga Khadija da ki ke gani?" Ya fad'a ya na nuna Khadija dake gefen shi, Haseenah dai ta baza kunne ta na saurare, d'orawa da "Ba iya matata ba ce kad'ai, rayuwa ta ce, kuma kin dawo gidan nan ne a dalilin ta, ita ta dage har saida ta ga kin dawo gidan nan, ke na tak'aice mi ki ma har saida ta kai munyi fad'a da ita ko magana ba ma yi saboda ke kawai, Haseenah dan Allah ki tsarkake zuciyarki ku zauna lafiya, Allah kuma ya bani ikon yin adalci a tsakanin ku." Khadija ce tace "Ameen mijin mu, Abban Bilal da kuma k'annan shi ma su zuwa, mun yarda ka ci gaba da jagorancin mu har zuwa gidan aljanna, mu na da yak'inin ba za mu tab'a yin nadama saboda kai *adalin miji* ne da mu ka yi sa'ar samun shi a wannan zamanin." Fuskar nan ta Usman kamar gonar audiga haka yake mata murmushi, saida ta kai aya yace "Allah yasa matata, Allah kuma ya sa ba zigani ki ke yi ba dan naga ki na neman fasa min kai." Dariya ta yi sosai ta mi shi fari da ido tace "A haba dai alaji, ai kasan ba ma haka da kai, duk abin da zai fito daga baki na akan ka gaskiya ne, saima saya wani abun da na ke saboda tsaro." Kashe mata ido ya yi ita ma kuma haka, Haseenah ta saki baki ta na kallon su, wani zafi taji ya na taso mata a zuciya tare da jin mugun kishi, amma a take ta lumshe ido ta furta a ranta "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un, Allah kasa na fi k'arfin zuciya ta." Ta na bud'a ido ta kalle su sai taji sanyi tare da jin sauk'in abin da ke ran ta, murmushi ta yi ta na ci gaba da kallon su ta ayyana a ranta in har ta na son zama da Usman dole ta girmama matar shi, sannan ya zama dole ta iya zama da su ta durmiya cikin rayuwar da suke, da k'yar ta mik'e tsaye saboda nauyin da ta yi tace "To sarakan soyayya, ni zan shiga na kwanta, kunsa fa na yi kewar gado na." Ba Khadija ba har Usman saida ya dara kafin yace "Kenan rayuwar gida babu dad'i ko?" Turo baki ta d'anyi tace "Babu kam." Jingina ya yi a kujera yace "Dan haka sai kowace ta kama kanta ta, in ba haka ba zan dinga yanka mu ku kati ne ku na tafiya gida ku na hutu." Kallon shi Khadija ta yi ta kalli Haseenah tace "Idan mutum ya shirya siyan abinci da kwanan kad'aici to ai ko yanzu a shirye muke, dan idan zamu shekara gida ma kaga lafiya lau mu ke kum hankali kwance." Haseenah ce ta juy tace "Saida safen ku aunty." Da murmushi tace "Allah tashe mu lafiya." Mik'ewa Usman ya yi yace "Bara na raka ki mai ciki, kar ki je ki zame." Hannun ta ya kama har suk isa falon ta, suna shiga ya saki hannunta har ta shiga uwar d'aka ta kwanta, juyawa ya yi zai fita yace "Ina zuwa." D'akin Khadija ya je ya mata saida safe kafin ya koma d'akin Haseenah, sam bai wani sakar mata fuska ba har bacci ya d'auke su, dan har ga Allah har yanzu ya na jin haushin ta idan ya tuna baya, kawai babu yanda zaiyi ne Khadija ta tilasta mata ya dawo da ita, kuma tunda ya dawo da ita dole ya sauke hakk'ok'in ta ko kuma ya had'u da fushin ubangiji, Haseenah kuma sam ba ta yi bacci ba saboda sabon ciwon bayan da ya taso mata, tun tana shiru ta na addu'a har ta daddab'a Usman ya farka, nan fa ya rikice saboda ba'a tab'a nak'uda a gaban shi ba, haihuwar Bilal ma baya garin, Khadija ya taso daga bacci ta taimaka mi shi, kayan haihuwar Haseenah na gida ba'a d'auko ba sai Khadija ce ta d'auko nata su ka tafi asibiti da su, saida aka karb'e ta an shiga d'akin haihuwa kad'ai Usman ya kira Hajia ya fad'a mu su, kafin Hajia ta iso Khadija ma ta fara jin bayan ta na d'aurewa tare da rik'ewar mara, a hankali taja baya ta zauna kan bancin da ke wajen, da sauri Usman ya sunkuya ya na kallon ta yace "Ya dai Nana, ko dai kema jikin ne?" Wani iska ta furzar ta girgiza kai tace "Um um." Sake kafeta ya yi da ido yace "Kin tab'a ba komai?" "Babu." Ta fad'a ta na huci, kallon tuhuma ya mata yace "Khadija ko dai kema a shigar da ke ciki ne?" "Ka bar shi kawai, ba buk'ata." Ta fad'a a wahalce, "Kin tabbata?" Da k'yar tace "Na tabbata." Mik'ewa ya yi yace "Shikenan, amma dan Allah da kinji wani abu ki yi magana tun da wuri." Komai ba tace ma sa ba har Hajia ta same su tare da malam da ya kawota, kamar dama jiran zuwan Hajia ake sai ko ga wata likita ta fito ta kalli Usman tace "Alhamdulillah ta haihu lafiya, an samu d'iya mace." "Alhamdulillah." Suka fad'a kusan a tare, nan akayi duk abin da ya kamata wanda suke buk'ata, lokacin dare ya yi sosai Hajia tace Usman ya koma gida da Khadija ita za ta zauna wajen su, ba b'ata lokaci suka kama hanyar gida Khadija sai gyangyad'i take, kallon ta ya yi ya na murmushi yace "Hajia wane suna ki ka zab'a da za'a sawa 'yar ta ki?" Cikin doguwar hamma tace "Ka tambayi maman ta mana, watak'ila ta na da sunan da take sha'awa ita ma." Wani kallo ya mata yace "Ta na da wata uwa ce da ta wuce ki a duniyar nan?" Cike da kasala tace "To idan da hali a saka mata *Nana Aisha* kaga idan na haihu nan kusa nima munyi 'yan biyu kenan sai a saka mata *Humaira*." Cikin murmushi yace "Idan kuma namiji ki ka sake sunkuto min fa." Cikin zolaya tace "Sai ka saka masa *Humair*." "To amma..." Da sauri ta katse shi tace "Dan Allah ka rabu da ni bacci na ke ji." Dariya ya yi yace "To idan ki ka yi bacci a motar fa?" Kai tsaye tace "Saika d'auke ni ka kwantar da ni akan gadon ka." Wani kallo ya mata yace "Me ya sa sai a kan gado na?" "Saboda ina so haihuwa ta same ni akan gadon." Marairaicewa ya yi yace "Yanzu ku saboda Allah haka za ku had'e min kai ku haihu lokaci d'aya, kenan dole nima sai na yi jego kamar ku." Dariya Khadija ta dinga shek'awa har da rik'e ciki kafin tace "Ai daidai kenan, kaga kai ma sai ka nemi k'unzugu ka aje saboda tarban jinin bik'i." Kamar zaiyi kuka yace "Allah ni dai ban yarda ba, babu wani jego da zanyi haka kawai da raina da lafiya ta, dole kisan dubarar da za ki dinga min saboda na gujewa abkawa jego." Hararan shi ta yi tace "Saboda ni kad'ai ce ke da kai?" Saida ya kashe mata ido yace "Amma ai ke dabance, ke kad'ai

Table of Contents

Chapters

117 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117