Chapter 62
Chapter 62
yi kamar yanda Baban shi ya nuna mi shi ita da hannu, idon shi ne suka cika da hawaye ya sunne kai k'asa, Haseenah ce tace "Kaga dan Allah, ba na son neman magana ni, in har ba zai zauna ba saboda ya na ganin cinye shi zanyi dan Allah ka tafi da shi, dan ba zai yiwu yaro da gidan ubanshi ba a same ni daga ni sai shi a gida ya zama kamar wani maraya, dan gashi tun yanzu ya na nunawa a gaban ka, in ba ma iskanci ba ni d'in bak'uwar ka ce?" Duk da hararan shi da take amma baisa Usman jin wani abu ba ko kad'an, hakan ne ya sa ma ya nuna Bilal da yatsa yace "Kar ma kace za ka fara min wannan nunkufarcin a gida wallahi, dan ba za ka ji dad'i ba, kuma a gidan za ka zauna kai da ita naga wanda ya isa ya hana." Hannu ya sa aljihu ya matso kusan shi yace "Ka saki ranka kaji ko, idan zan dawo zan siyo maka abun mamaki." Kai kawai ya d'an d'aga mi shi alamar to, fita ya yi Haseenah na ganin haka ta kalle shi tace "To d'an masu gida, maza tashi ka d'auke kwanukan nan ka wanke su, dan na lura kai ba'a morar ka a gidan nan." Hawayen da yaron ke rik'ewa ne suka taho mi shi, mik'ewa ya yi ya d'auki farantan ya nufi madafa da su, ya kai madafar zai bud'a k'ofar ya rasa ya zaiyi, cikin dubara ya zura hannu zai bud'e sai kuwa wani faranti ya fad'o k'asa ji kake "tatssssssss." Da gudu gudu Haseenah ta taso ta fito waje ta na fad'in "Ka zubar halan? Saboda bak'in hali, dan na saka aiki shine za ka fasa min kaya." Ta na zuwa ta kalli farantin da ke k'asa ta kalli Bilal da ya kafe ta da ido cike da tsoro, cikin jin haushi da mugunta ta d'aga hannu ta d'auke da mari ta na fad'in "Dan uban ka kai musakin ina ne? Uban ka ne ya siya min da za ka fasa min kaya?" Kamar saukar aradu taji daga bayan ta ance "Sai dai uban ki wallahi ba na shi uban ba, 'yar matsiyata da ba ki gaji arzik'i ba, talaka 'yar talakawa, wato an samu wuri ko?" ππππ _Bala'i da d'umi d'umin shi, ni kam waye wannan? A cikin yan biyar wa ya fi zafin zuciya? Ku tayani tunani mana mutane na._π 13/02/2020 Γ 13:10 - πππ: ππππππππππ *KALLON KITSE* _(Ake wa rogo)_ ππππππππππ _SAMIRA HAROUNA_ *Litattafan marubuciyar* *1* _KAUSSAR_ *2* _D'AUKAR FANSA_ *3* _BA SO BANE_ *4* _AUREN HAD'I_ *5* _SANIN MASOYI_ *6* _JIHADI_ *7* _K'ANGIN RAYUWA_ *8* _ITACE K'ADDARARMU_ *9* _KAWU NA NE_ *10* _MAATA_ *11* _KALLON KITSE..._ *SADAUKARWA GA* _MATAN FARKO_ π§πΌ *(UWAYEN GIDA)* πΈπ¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S* _(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_π€π€ ```Fatan alkairi masoya``` _Bismillahir rahamanir rahim_ *24* Tunda Haseenah ta ga Hajia Turai gaban ta ya fad'i, hak'ik'a ta tsorata sosai dan Hajia Turai irin mutanen nan ne da kana ganinsu kaga zubin rashin mutumci da masifa a tare da su, riga da siket ne jikin ta na atamfa sun kamata sosai, sai siririn gyalen da ta d'ora a kafad'a d'aya ta k'araso wajen su Bilal d'in, ido waje ta kalle ta tace "Ke yanzu akan wannan banzan farantin ne har za ki tsaya ki na zagin shi, miye wannan d'in? Ke yanzu in ba halin tsiya ba me akayi akayi wannan banzan farantin da ake siyarwa dala tamanin, shine da ba ki da mutumci har za ki tsaya ki na wani zagin shi, ke kinsan waye wannan yaron kuwa? To Bilal da ki ke gani kamar d'an ciki na haka na d'auke shi, domin kuwa uwar shi ta min abin da ba zan tab'a mantawa ba har abada, kar ki ce za ki saka k'afar wando d'aya da Khadija, dan wallahi ki na sakawa fatar jikin ki ce zata yaye ta bar ki da kunya, Bilal kuma ya zama dole ki zauna da shi dan gidan uban shine nan d'in, yarima ne a fadar mahaifin shi dan haka ya zama dole mai son ya zauna da sarki ya so yarima." Gyara tsayuwa ta yi har da wani jijjiga ta nuna ta da yatsa tace "Wallahi tun ranar da na ganki nasan sai an samu munafurci a k'ugun ki, bansan irin zaman da ku ke ba dan har yanzu ba mu zauna da Khadija ba, amma dai tabbas nasan akwai matsala a gidan nan, to ki shirya da kyau yarinya dan zuwa na na gaba gidan nan ba lallai ya mi ki kyau ba, wallahi tallahi kinci sa'a akwai in da zanje yanzu cikin gaggawa, ba dan haka ba da sai na kwab'e rigata na yi zigidir kafin in ci ubanki, dan na lura ke 'yar marasa mutumci ce." Kallon Bilal ta yi ta fito da chocolat daga jakar ta ta hannu da murmushi ta mik'a mi shi tace "Saboda kai kawai na zo gidan nan, ga wannan nasan ka na son ta sosai." Karb'a ya yi da hannu biyu yace "Nagode aunty." Shafa kan shi ta yi tace "Ba komai d'an auntyn shi." D'orawa ta yi da "Maman ka na ciki ne?" Saida ya kalli Haseenah da ta juya ta shiga madafa yace "Bata nan, tun jiya ta tafi gida, ni ma ina so naje wajen ta." Shiru ta yi ta na nazartar wani abu kafin ta sake shafa kan shi tace "Ka yi hak'uri kaji yarima, yanzu ni ina sauri zanje wani wuri ne duba wasu kaya, kuma kaga banda ikon da zai fitar da kai daga gidan nan dan bansan me ya faru ba, amma ka yi hak'uri kji ko." Kai kawai ya d'aga mata, murmushi ta sake mi shi tace "Yawwa, to yanzu ka shiga ciki ka zauna kaji ko, ni na tafi sai anjima." "To aunty." Ya fad'a ya na shiga ta falon mahaifin shi dan sada shi da falon maman shi dan k'ofar waje rufe take, Turai na ganin haka ta lek'a madafar ta ga Haseenah ta yi tsaye jugum ta na jiran Turai ta tafi ko ta samu ta koma falon ta, wani murmushi ta mata tace "Amarya ni zan wuce." Hannu ta sa aljihu ta fito da 'yer jaka goma ko karyawa babu ta cilla mata tace "Wannan zai isheki ki siyi sabbin farantai har dozin dozin, amma ki sani yarima da iyayen shi ba matsiyata bane irin ki." Har ta juya zata fita ta kuma sake tsayawa ta juyo tace "Idan Usee d'in ya zo ki fad'a ma sa Hajia Turai DubaΓ― ta zo, sannan ki ce ya fad'a mi ki wacece ni, za ki ji baya ni daga bakin shi." Juyawa ta yi ta fice ta bar Haseenah duk ta yi gumi saboda tsoro, dan har ga Allah har zuciyar ta tsoron matar ya d'arsu a zuciyarta, dan kana ganin kasan ta take Khadija ta shanye wajen masifa da ma k'arfi, amma da ta samu nutsuwa ta dawo jikinta saita shirya sake wani makircin da tugu, d'aukar kud'in ta yi ta saka a cikin rigar nonon ta, kiran Usman ta yi a waya ya na d'auka ta fashe da kuka tace "Abban
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117