Chapter 91
Chapter 91
ya shak'e shi zaiyi atshawa, to da izinin Allah duk wani bala'i dake kansa zai bar shi ko ba'a so." Daga Khadija har Hajia godiya su ke masa amma ya na cewa ba komai, haka ya tashi tafiya su ka bashi kud'in mota ma amma ya k'i karb'a yace ya yi ne saboda Allah kawai, sai lambar shi kawai sabuwa da Khadija ta karb'a ta na ci gaba da k'ara masa godiya, nan su ka shiga tattauna yanda za su saka Usman yin wanka da maganin nan, gaba d'aya kan su ne ya kulle dan haka Mama tace kawai ta bari har bayan bikin Nura in ya so sai su san abinyi, haka akayi Khadija ta kai maganin ta nasa a cikin jakar ta da ke kusa da gado, bayan sallah magrib kuma su ka yi waya da Bilal har ya na fad'a mata shi gaba d'aya surutun gidan ya dame shi, tunda yamma ake ta maganar Abban shi da matar shi har ya fara jin haushin mutanen, hak'uri ta bashi tare da cewa ya fita waje yanzu ai da malam ya shigo zai zauna k'ofar gida, haka akayi kam sai k'ofar gidan kad'ai ya samu nutsuwa. Ko da Aziza ta zo ana sallah isha'i lokacin malam da Bilal na masallaci, da kuka ta shigo gidan aka tarbe da tambayar lafiya? Nan ta fad'a ma Hajia abin da ya faru kuma ran ta ya b'ace sosai, wannan karan an tab'a mata autar ta dan haka dole rai ya b'ace, ji ta yi ba za ta hak'ura ba dan haka ta kira shi a waya, ya na d'auka ita ma ta zazzage shi da masifa har ta na fad'in ya zama lusari yarinya k'arama na juya shi, shi dai k'ala bai ce ba har ta gama ta kashe wayar, sai lokacin ne su ka san Aziza ba ta gidan, ko a jikin su kam dad'i ma su ka ji da ta tafi d'in. *Washe gari* ta kama juma'a, malam na sallah asuba ya dawo gida ya canza kaya ya fita, a k'asa ya ke tafiya cikin nutsuwa ya na zikiri har ya yi doguwar tafiya, tashar mota ya isa da ke *'yar sonita*, mota ya samu da babu komai a ciki ya fad'i garin da za shi, saboda biyan buk'ata yace shata ya ke so a kai shi a dawo da shi, dama garin ba wani nisa ne da shi ba, nan ya shiga tare da dreba su ka d'auki hanyar da zai sada su da wani k'auye da ake kira garin *Bamo*, har k'ofar gida aka aje shi ya kusa yi sa'ar samun wani tsoho da ba za su gaza wari ba a k'ofar gidan akan tabarmar kaba, daga yanda suka gaisa suke dariya zai nuna ma ka ba sanin yau bane ko kuma ma abokai ne, zaune su ka yi daga cikin wata runfa dake gefe akan wata tabarmar da ke d'auke da buzun akuya, nan ne har tsohon ya ke fad'in "Mu muna shirin tafiya garin auwa yamma kuma kai sai ka ga, lafiya kuwa?" Ajiyar zuciya malam ya sauke yace "Lafiya ba lafiya ba *Lawali*, halin da gidan nan ke ciki ne ma ya sa na kasa hak'ura har yamma ta yi ka zo ni na zo da kai na." Cikin nutsuwa yace "Toh, me ya ke faruwa ne haka malam Ali?" Nan dai bai tsaya b'ata lokaci ba ya fad'awa tsohon abin da ke faruwa a gidan na shi, malam Lawali ne yace "Amma yanzu har wannan iskancin na faruwa amma ka kasa sanar da ni, wannan shegentakar har ta bar kan wasu ta dawo kan yaran mu, gaskiya banji dad'i ba da sai yanzu ka ke fad'a min." "Da farko na d'auka abun na ta ba zaiyi k'amari haka ba, amma daga yanda ta raba shi da kowa na shi ne ya nuna min ita d'in dama ba mai son shi da arzik'i ba ce, na fara bashi taimako da kai na wanda na san zai warware komai cikin sauk'i, to matsalar da aka samu baya ma zuwa gidan akai akai bare har maganin ya karb'i jikin shi, shi ya sa na ce to bari na sada matsalar nan da kai." Cikin b'acin rai Lawali ya mik'e ya nufi cikin gidan shi ya na fad'in "Ina zuwa bani minti biyu, wannan ai maganar banza ce da wofi, mu za'a kawowa iskanci har gida, yo badan ma yaran sun zama 'yan zamani ba basa son shan saiwa na tsarin jiki yo da ko kusa da shi ta isa ta zo ma, kuma kai ma da ka fad'a min da wuri da ko kwana d'aya ya yi a cikin tarkon ta, ga dukkan alama ba ta san wata aura ba shi ya sa, mu da ake baro k'asa mai tsarki azo neman taimako wajen kuma a dace da yardar ubangiji shine har d'an mu zai shiga wannan halin kuma ya kwashe watanni a kasa fito da shi, aikin banza aikin wofi." Haka ya shiga gidan ya na ci gaba da bambami har ya shiga d'akin shi ya d'auko wasu sayun magani fari dogaye ya fito da shi, kawo mi shi ya yi yasa a leda ya zauna kan kujera ya juya bayan shi ya d'auko robar lemu sai dai ruwa ne a ciki fari tas ya bashi yace "Da wannan ruwan za'a jik'a magani, ruwan da ya yi alwalan sallah magriba da su sai ka cire maganin a zuba ruwan alwalar, idan ya yi sallah sai ya yi wanda da su amma a buta za'a zuba ruwa." "Na fahimta, nago..." Katse shi ya yi da cewa "Kar ka fara min godiya, in ba haka ba maganin ba zaiyi ba ma, ko ka manta wanene kai a wuri na?" Dariya malam Ali ya yi ya mik'e, saida ya shiga cikin gidan su ka gaisa da matan kafin ya fito ya samu dreban nan su ka wuce da cewa sai sun zo suma wajen bikin Nura, kamar bai je ko ina ba sai gashi ya dawo ko rana bata gama haska duka gari ba, jika maganin ya yi da wannan ruwan kafin ya shiga wata sabgar ba tare da ya fad'awa kowa ba. *Yamma* lik'is Khadija ta fito bayan ta biya ta karb'owa Bilal sabon d'inkin shi sannan ta zo gidan, ta na sallama kam gida dama ya samu hallarar dangi har an fara d'ora tukunyar abincin d'aurin aure, nan fa kowa Hajia Khadija Hajia Khadija, sosai ta gaisa da mutane kafin ta wuce d'akin Hajia, abun mamaki sam Hajia kasa had'a ido ta yi da ita sai haka suka gaisa cikin kunya, su Hassana ma da Rabi'a haka, sai ma wani sabon al'amari daga gare su na kowa ya na son ya mata magana, wurin zama suka samar mata tare da kawo mata ruwan sha da lemu, sai dai suma ba kowa ke kallon ta ba, ita kam ko a jikin ta sai dai ba ta sakar mu su fuska ba, kuma ta zo gidan nan dan ta ga malam ta bashi wannan maganin, dan ita bata san yanda za ta sa shi ya yi wanka da shi ba, ganin sun baibaiye ta ya sa ta fito tace su yi aiki, sai lokacin Bilal ya shigo Khadija ta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117