Chapter 56
Chapter 56
ka yi farin ciki hakan ya ishe ni." Mik'ewa ya yi yace "Nagode matata, ni zan koma can na canza kaya, amma ki tashi ki yi wanka yanzu sai ki fito mu ci abinci." Cike da makirci tace "Toh." Ya na fita ta sauka da gaggawa ta shiga ta yi wanka ta fito ta yi sallah, riga ta saka iya gwiwa yar kanti ta fito da ita kai babu d'an kwali, lokacin Bilal har ya shirya Bilyamin ya d'auke shi sun tafi, Usman na zaune akan kujera Khadija na zuba masa abinci, yanda ya d'aure fuska babu annuri ne ya sa ta share shi ita ma, mayar da kallon shi ya yi ga Haseenah da ta fito ta na karkad'e gashin ta cikin takon jan hankali, kallon ta Khadija ta yi har ta zauna akan kujera, da wani shegen murmushi Usman yace mata "Sannu da fitowa." Turo baki ta yi cikin shagwab'a tace "Ba zan sake ma ka magana ba sai nan da wata d'aya." "Me?" Ya fad'a da zaro ido, d'orawa ya yi da "Haba amarya rufa min asiri mana, ina zan saka kai na to idan ki ka daina min magana, kinsan fa ke ce haske kuma fitilar zuciya ta dama gidan nan ba ki d'aya." Sake turo baki ta yi ta kawar da kai tace "Ni ka k'yale ni kawai." "To wai me na yi ma da za'a min wannan hukuncin?" Kallon Khadija ya yi saboda aje farantin abinci da ta yi gaban shi, ita ma zubawa ta yi ta zauna ta fara tsakura ta na satar kallon su, amma zuciyar ta ta kai k'arshe wajen k'una, cike da shagwab'a tace "Ka ma manta kenan? Haka kawai ina bacci na za ka zo ka tara min gajiya, yanzu gashi duk jiki na ciwo ya ke, kuma saida na fad'a ma ka kar ka yi amma ka k'i saurara ta." Hannu ya sa ya na shafa wuyan shi cikin alamun rashin gaskiya, satar kallon Khadija ya yi wacce ta k'i d'ago kai saboda hawayen da ke son taho mata, dan ya kawar da zancen ya sa ya kalle ta yace "Ba ki zuba mata abincin ba ita." Wani jan kallo ta mi shi tace "Au! Wai ni ce ma zan zuba mata? To ai na ga duka yau kwanan mu ne ni da ita, me zai hana ta zuba da kan ta ko kuma ka zuba mata." Had'e rai ya yi yace "Ke me ki ke nufi ne? Ba na son maganar banza fa kinji ko, daga k'aramar magana za ki wani tasowa mutane, zuciyar ki ta raya mi ki k'arya da gaskiya kawai sai ki zauna akai." Zunbur ta mik'e tace "Au! Wai zuciya ta ma ce ta raya min kenan? To kamar yanda ba ka son maganar banza haka nima, wallahi Abban Bilal ka ji tsoron Allah kasan cewa za ka mutu." Maida kallon ga tayi ga Haseenah tace "Ke kuma ki sani duk rayuwar da aka ginata babu Allah a ciki wallahi k'arshen ta munin ta ya na bayar da mamaki, Allah ma shaida ne ban rik'e ki a zuciya ta ba ko kad'an, na so na zauna lafiya da ke mu taru mu farantawa mijin mu, amma na fahimci kin biyo abun ta bayan gida saboda cimma burin ki a kai na, ki sani Haseenah wallahi tallahi da ace zan yi dan na raba ki da Usman, to ina da bokan da idan har ya shiga tsakanin ki da shi wallahi tallahi ba ke ba duk wanda ya zauna tare da ke ma sai ya tsane shi, amma tuna akwai Allah kuma zan mutu ya sa na d'aga mi ki k'afa, amma muje zuwa." Ta na fad'a ta juya ta koma falon ta, janyo Haseenah ya yi ya d'ora a cinyar shi ya fara bata abincin ya na fad'in "Ki shirya kayan ki, ina tunanin tafiya da ke Dubai a satin nan, dan ba zan yarda na barki tare da matar nan ba a gidan nan." Duk da a zuciyar ta akwai abin da taji shed'an na raya mata, amma sai ta nuna ta yi murna ta hanyar cewa "Dubai? Ni? Wayyo Allah yaushe? Da gaske ka ke?" "Um, ki shirya kawai, ina tunanin tafiya nan da kwana biyu zuwa uku." Haka suka gama cin abincin ya fita ita kuma ta koma d'aki, ta jima ta na waya da Mariya ta na fad'a mata canjin da aka samu, amma ba ta fad'a mata abin da ta ke shirin aikatawa ba har suka yi sallama, su na gamawa Haseenah ta shirya tsaf ta fito, kai tsayz k'ofar fita ta nufa mai gadi ya bud'e mata k'ofa, a lokacin Khadija na madafa ta tsinkaye ta ta fice, aikin gaban ta ta ci gaba da yi ba tare da tunanin komai ba, har ta gama aiki da duk abin da ta ke yi, ta na zaune falo tare da Bilal Usman ya shigo, ta yi mamakin ganin shi a lokacin sosai, shi ma kuma ya na ta kiran Haseenah ne ta k'i d'aga wayar shi duk abin duniya ya dame shi, hakan ya sa ya zo gidan kuma ya na nufa b'angaren ta ya ga k'ofar rufe alamar ba ta nan, shi ya sa ya shigo wajen Khadija, tsaye ya yi a kan ta yace "Na ga yarinyar nan ba ta nan ko kinsan in da ta tafi?" Wani murmushin ta yi tace "Ni kuma ina zan san in da ta tafi? Ko gaishe ni ka ga ta na yi bare na samu kimar da za ta fad'a min za ta fita." Wani dogon tsaki ya yi ya sake kara wayar shi a kunne, ta na kururuwa wayar amma ta k'i d'auka, sake maida kiran ya yi hakan ya sa mahaifin Haseenahr d'auka, dama ko da ta je gida da kuka ta isa, ta na zuwa ta k'ara fashewa da kuka wai ita wallahi ta gama auren gidan Usman, anyi tabbaya amma ta k'i fad'a saida aka kira Baban ta ya zo sannan tace "Ni kawai ba zan koma gidan shi ba, wallahi ba na bacci a cikin dare sai a dinga bani tsoro, yanzu kuma kawai..." Kuma sai ta yi shiru, mahaifin ta ne yace "Kawai me?" Kallon shi ta yi da ido tsakar kai tace "Ba komai, ni kawai ba zan koma ba." Ta na ganin kiran Usman a waya sai ta ture wayar wai ko sunan ma ba ta son gani, hakan ya sa iyayen jikin su yin sanyi su ka fara tunanin shiga baga ne na kishiya kawai, shine yanzu da ya kira baban ta ya d'auka, saida su ka gaisa cikin mutumci kafin yace ya zo ya same shi gida ya na son ganin shi, ba musu yace ya na nan tafe yanzun, dan shima idan bai ganta ba ba zai iya salun nutsuwa ba, Khadija na kallo ya fita daga gidan da sauri. Ya na zuwa kam suka tattauna sosai in da Haseenah ke cewa kawai ya sake ta ba za ta koma ba, shi kam yace ba zai iya rayuwa ba yanzun babu ita, dan haka dai aka sasanta mahaifin ta yace ta je gida zai samar mata magani, haka ya d'auko ta suka dawo gida bayan ya bawa Baban
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117