Chapter 104
Chapter 104
cikin zafin rai ido jawur yace "Haseenah me nai mi ki a rayuwa? Me ya sa ki ka cutar dani? Me ya sa Haseenah?" Cikin duburburcewa tace "Wallahi ba ni bace, ka yi hak'uri dan Allah, ba zan.." Shak'e mata wuyan da ya yi ne yasa komai nata tsayawa idon ta fitowa waje, cikin fitar hayyaci Usman ke fad'in "Haseenah ke annoba ce, jaraba ce kuma masifa ce ke da bala'i, barin irin ki a doron duniya wallahi japa'i ne, wallahi da zan kashe ki amma ba zan iya ba saboda cikin da ke jikin ki, Haseenah banga anfanin zama da ke ba a rayuwa ta, kin raba ni da hankali na da ubangiji na, kin raba ni da iyaye na da 'yan uwa na, kin raba ni da matar da nafi so a rayuwa ta, sannan kin raba ni da d'ana da ya fito daga ciki na, Haseenah ni kam ya zanyi dake? Wane irin hukuncin ma zan mi ki ne da zai sa na huce abin da ki ka min." Haseenah dake ta fafutukar neman rayuwa ya na sakin ta ta samu ta sauke wasu numfarfashi, mik'ewa ya yi tsaye ya juya baya ya cire hular kan shi yana shafa sumar shi kamar zai cire kan, sake juyowa ya yi ya nuna ta da hannu yace "A dalilin ki yanzu haka Bilal na kwance asibiti, bansan ko zai rayu ba saboda yanda jikin shi yake, dan haka Haseenah ba zan iya ci gaba da zama dake ba, kije gidanku kawai na sake ki saki biyu." Wata k'ara Haseenah ta yi ta d'ora hannu akai tace "Ahhhhhhh, na shiga uku na lalace, dan Allah Usman ka rufa min asiri ka yi hak'uri ka yafe min, wallahi ba zan sake ba na rantse ma ka, ka taimaka min mana ka dubi cikin nan dake jikina, kar ka mayar dani bazawara tun yanzu Usman ko haihuwar fari banyi ba." Girgiza kai yayi ya tab'e baki yace "Hum, ai ko meya faru ke kika jawa kan ki, dan haka ki tattara naki ya naki ki bar min gida na, idan ki ka bari na dawo gidan nan na same ki wallahi saina lahira ya fiki jin dad'i." Yana fad'a ya fice daga madafar ya shiga b'angaren shi, rage kayan jikinshi ya yi ya shiga ya watsa ruwa saboda yaji sanyi, yana fitowa maganin ciwon kai yasha kafin ya canza kaya ya bar gidan ko kallon b'angaren Haseenah baiyi ba, a tunanin shi ma tana barin gidan zai ruguza wannan b'angaren dan ya zauna lafiya, dan ba zaisake bari zuciyarshi ta raya mi shi sake k'ara wani aure nan gaba, lokacin har an fara kiran sallah la'asar sai kawai ya tsaya ya yi sallah kafin ya isa asibiti. *Ana tare*π€ 11/03/2020 Γ 19:36 - πππ: ππππππππππ *KALLON KITSE* _(Ake wa rogo)_ ππππππππππ _SAMIRA HAROUNA_ *Litattafan marubuciyar* *1* _KAUSSAR_ *2* _D'AUKAR FANSA_ *3* _BA SO BANE_ *4* _AUREN HAD'I_ *5* _SANIN MASOYI_ *6* _JIHADI_ *7* _K'ANGIN RAYUWA_ *8* _ITACE K'ADDARARMU_ *9* _KAWU NA NE_ *10* _MAATA_ *11* _KALLON KITSE..._ *SADAUKARWA GA* _MATAN FARKO_ π§πΌ *(UWAYEN GIDA)* πΈπ¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S* _(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_π€π€ ```Fatan alkairi masoya``` _Bismillahir rahamanir rahim_ *38* Bai samu ganin Khadija ba saboda a lokacin suna sallah, kuma an rufe d'akin da Bilal ke kwance saboda hayaniyar da tayi yawa aka barshi shi kad'ai kafin wani lokaci, fita Usman d'in ya yi yace zai dawo anjima. A wajen Haseenah ba yanda ta iya dole ta d'an d'auki abin da ta d'auka ta fito ta na kuka ta bar gidan, amma da taje gida kasa fad'an komai ta yi sai tace kawai ta na girki ya same ta yace ta taho gida ya sake ta saki biyu, su kam iyayen take su ka d'ora laifin kan Khadija cewa ita ta shiga ta fita aka sake ta, Haseenah dai komai ba tace ba sai sauraren su, mahaifin ta ne yace zai je ya samu mahaifin Usman d'in dan ba zai d'auki wannan wulak'ancin ba a sako masa 'ya da tsohon ciki, ba ta yi yunk'urin hanawa ba tunda ita kan ta za ta so ta koma d'in, haka ko akayi bayan sallah magriba anyi katari malam ya na gidan mahaifin Haseenah ya sallama ya fito, da ganin shi malam ya tarbe shi yanda ya kamata ya shinfid'a mu su tabarma a waje su ka zauna, nan fa malam *Mussa* ya fad'awa malam abin da ke faruwa, sosai malam ya jinjina ya kuma fad'a mi shi baisan me ke faruwa ba sai yanzu, amma ya yi alk'awarin tuntub'ar Fodio yaji dalilin yin hakan, nan dai ya kwantar masa da hankali suka rabu lafiya, malam kam baiyi k'asa a gwiwa ba wajen kiran Usman yace ya same shi gida, ana idar da sallah isha'i ya k'araso ya samu malam, a cikin gida suka samu waje tare da Hajia suka tattauna sosai sosai, anan ya fad'a mu su cewa "A gaskiya Baba ba zan iya zama da yarinyar nan ba, domin kuwa duk ita ce silar abubuwan da suka dinga faruwa da ni, kawai ku rabu da ita can ta haihu, idan ta haihu zanje na d'auko abinda ta haifa bayan ta shayar da shi dan ba zan iya barin abin da ta haifa a hannunta ba saboda mugun halin ta." Malam ne yace "Amma duk abin da tayi Fodio bai kamata ka sake ta a wannan halin ba." Shirun da ya yi yasa Hajia cewa "Koma dai menene ita taja, a gaskiya Hassenah ta bamu mamaki, yarinya sumi-sumi ashe lunbu-lunbu ce macijin k'yaik'ayi, muna ta wa Khadija kallon mai laifi ashe ita ce muguwar." Murmushin gefen labb'a malam ya yi yace "Ai ni na sani dama *kallon kitse ne ku ke wa rogo*, kawai na zura mu ku ido ne har ita yarinyar ta mu ku ido, in banda hauka irin na ku ma ko gaske ne Khadija ta mallake Usman ai ni a gani na daidai ta yi, domin kuwa in har za mu iya yin magana irin ta jahilai to za mu iya cewa k'ashin arzik'in shi a jikin ta yake, shi ba kyau ba, shi ba hasken fata ba, shi ba kud'i ba a lokacin da ta aure shi, kuga kuwa tana da damar da za ta iya d'aukar kowane mataki dan ya zama na ta." Cikin sanyin jiki Hajia tace "Gaskiya ne, wallahi sai yanzu na ke jin kunyar ta akan abubuwan da suka faru, daurewa kawai nake ina kallon ta." Murmushi Usman yayi yace "Hajia ku kwantar da hankalinku in dai Khadija ce na tabbata ba ta kallon ku da wannan abun." Nan dai suka gama tattaunawarsu kafin ya mu su sallama yace zai tafi asibiti, su kuma dama acan su ka yi sallah magriba, ba su jima da dawowa ba Abban Haseenah ya zo, daga nan asibiti ya nufa ya samu kam kamar ana wata sabga d'akin taf da mutane, Khadija dake zaune kusan Bilal muryar shi ce ta fallasa mi shi yanayin da yake ciki, duk sai taji ba dad'i tausayin shi ya kamata, gaisawa ya yi da mutanen dake d'akin kafin ya isa a gadon Bilal, kafe Khadija ya yi da ido yace "Nana ya mai jikin?" Saida ta had'e abin da ya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117