Skip to content

Chapter 69

Chapter 69

Kallon Kitse Book One Complete Hausa Novels 1,199 words 0 views Progress saved
Download Book

dai gani Aziza da idon ki, duk wanda ya zo gidan nan wajen ta sai ya zo ya ci mutumci na, ba na shiga sabgarta amma ita sai ta san yanda ta yi ta tsokane ni, yanzu wannan da me ya yi kama?" "Ki yi hak'uri dan Allah ki rabu da ita, can aniyarta ta koma mata." Cewar Aziza, Haseenah ce tace "Mu sauka k'asa kawai dan magriba ta gabato." "Gaskiya kam." Aziza ta fad'a ta na d'aukar kwanon abinci ta na fad'in "Ta mayar da mu mabarata k'arfi da yaji, in dai ta yi abinci ran alhamis da juma'a to ranar za mu samu abinci, saboda ta na yin abincin da take rabawa mutanen ta, shi ma fa ba kullum ba sai taga dama." Kallon ta Haseenah ta yi ta wutsiyar ido a zuciyar ta tace "To ai saboda ki na gidan a wannan ranakun shi ya sa ba na iya zubar da shi, sai kin fita kad'ai na ke samun wannan damar." Tunda Aishatu ta koma take mita akan amaryar Usman, har akayi sallah magrib da isha'i su ka ci abinci, anan take tambayar Khadija za ta je bikin *Saratu* (kamar jikanya take ga mahaifiyar Khadija), zaro ido ta yi tace "Wai yaushe ne bikin Saratu?" "Jibi mana." Cewar Aishatu tana shirgar wainar ta, cike da mamaki Khadija tace "Wallahi na manta, kuma Mama ba ta sake tuna min ba, amma dai bara na kira Abban Bilal na fad'a mi shi yanzun nan, dan zan iya mantawa, kuma tafiya ce da ba nan cikin gari ba akwai buk'atar ya sani da wuri." Saida ta d'auki wayar ta ga kiran shi har uku ba ta d'aga ba, maida kiran ta yi kamar kuma jira ya ke sai kuwa ya d'auka dan ya zazzage kwandon bala'i, cikin sa'a sai Aishatu ta d'aga murya tace "Gaida min shi, ki ce na ga amaryar shi ina taya shi murna." Dariya Khadija ta yi tace " bara na baki sai ki fad'a mi shi." Bata wayar ta yi, kasancewar akwai fahimtar juna tsakaninsu ya sa su ka dinga hira ta na tsokanar shi shima haka kafin Khadija ta karb'i wayar, ta na d'orawa a kunne tace "An wuni lafiya saraki." "Lafiya lau, anga damar d'aukar wayar?" Murmushi ta yi tace "Ka yi hak'uri, ina aiki ne a lokacin ban lura ba, yanzu ma na d'auko wayar ne zan nemi izinin ka sai na ga kiran." "Izinin me kuma?" "In ba ka manta ba wata biyu da ya wuce na baka goron Saratu? To bikin ne ya taso yanzu ni har na manta ma saida Aishatu ta tuna min." "Yaushe ne?" Ta na wasa da yatsunta tace "Jibi, ranar da su Bilal za su koma makaranta." "Amma ai ba cikin gari bane?" "Eh hakane." "Shikenan, Allah ya tsare, zan kira Mama na tambaye ta shirye shiryen tafiyar." Ya na fad'in haka ya datse kiran, ita kam bata wani damu ba tunda dai ya barta, sai wajen tara na dare Khadija ta ma Aishatu kyautar fitar hankali kafin ta bar gidan. B'angaren Haseenah kam tunda ta ci wainar nan dayawa sai ta tayar mata da zuciya ta dinga kelaya amai, sosai ta galabaita har Aziza ta tashi hankalin ta, dare na sake yi kuma sai zazzab'i da ciwon kai, Hajia su ka kira aka fad'a mata tace su shirya su fad'awa Khadija tunda ita ta iya mota saita kai ta asibiti, ira kuma za ta same su asibitin yanzu, har Aziza za ta tafi wajen Khadija kawai Haseenah ta rik'e hannunta tace kar taje, "Me ya sa to?" Ita ce tambayar da ta mata. Cikin galabaita tace "Kawai ba na so tasan halin da na ke ciki, ko ta taimaka min ba dan Allah bane, dan ta samu mafakar da za ta yak'eni ne." Da mamaki tace "Amma Haseenah dan ta kai mu asibiti miye a ciki?" Kallonta ta yi tace "Aziza in za ki samo mai adaidaita ki samo, in ba za ki sami ba ki bar shi, yanzu haka da yan uwa na za su san ina cin abincin ta wallahi da sun tofa min yawu, mutum fa ba abun yarda bane, kuma ke kinfi kowa sanin ta ai." "Gaskiya ne kuma." Cewar Aziza jiki a sanyaye, haka suka shirya suka fita a hanya suka yi sa'ar samun adaidaita su ka hau, asibitin kud'i aka kai da ke nan kusa da su ta *Clinique Alheri*, tun kafin su ka likitan Hajia ta k'araso ta na waya da Usman da ta sa aka kira shi take fad'a mi shi, aifa kamar ya taso ya zo ya ke ji ance amarsu ba lafiya, ko da su ka ga likita ya mu su albishir da ta na da ciki amma k'arami, nan dai aka mata allura tare da bata magunguna, bayan sun biya kud'i tsagaga su ka dawo gida da rankiyar Hajia, kwance Haseenah ta yi Hajia ta kalli Aziza tace "Da na ce ku fad'awa Khadija ta kai ku me ya sa ba ku mata magana ba ku ka hau adaidaita?" Aziza ce "Hajia zan..." Da sauri Haseenah ta mata alama da hannu kan ta yi shiru, duk da Hajia ta gani amma da tace "Me ye ta yi shiru?" Cike da tausayi tace "Hajia kawai ku bar maganar, tunda dai gashi mun tafi kuma mun dawo lafiya." Shiru Hajia ta yi da mamaki, kallon ta tayi tace "Kun ci abinci?" Kallon juna su ka yi sai Haseenah ce tace "Wallahi wata waina ce aunty Khadija ta aiko mana, ko gama ci banyi ba zuciyata ta tashi sai amai." "Yanzu ta na aiko mu ku da abincin kenan?" Cewar Hajia ta na kafesu da ido, Aziza ce tace "Hajia bata aikowa fa, sai kamar irin wannan ranakun alhamis ko juma'a, shi ma sai in ya na girkin ta ne." Kallon Haseenah ta yi tace "Ki fad'awa Aziza idan za ki ci wani abu mai sauk'i saita d'ora mi ki kafin ki sha magani, ni yanzu gida zan tafi dare ya yi." "To." Ta fad'a ta na yamutsa fuska, Hajia na fita tasa Aziza ta d'ora mata zallar shayi tasha kafin tasha magana, kiran ta Usman ya yi suka dinga hira har saida tace za ta yi bacci, Hajia kuma na fita ko kallon b'angaren Khadija ba ta yi ba saboda ran ta ya sake b'acewa a game da ita, adaidaita ta hau ta koma gida, ba ta yi nauyin baki ba wajen fad'awa malam abin da ake ciki, sai dai shi baiji komai ba a zuciyar shi, sai dai yafi mayar da hankalin shi kan Usman da ya ke d'an ganin canji a tare da shi yanzun, da haka suka kwanta da fatan ganin wayewar gari lafiya. Tunda safe Hajia ta had'a abin kari ta bawa Nura ya tafi ya kai ma su Haseenah, a lokacin Khadija na madafa da doguwar rigar bacci a jikinta Nura ya shigo, da kallo ta bishi har ya wuce b'angaren Haseenah kai tsaye kamar yanda Hajia ta fad'a mi shi, amma bai jima ba ya dawo dan gaisawa kad'ai ya yi da Haseenah ko jiki bai tambaye ta, falon Khadija ya lek'a sai Bilal kwance akan kujera, baisan da shigowar shi ba yace "Yarima barka da safiya." Juyowa ya

Table of Contents

Chapters

117 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117