Skip to content

Chapter 41

Chapter 41

Kallon Kitse Book One Complete Hausa Novels 1,201 words 0 views Progress saved
Download Book

ajiyar zuciya yace "Lafiyar su k'alau, kai kawo min lemu mai sanyi na sha." Ya k'arashe da kallon Bilal. D'auko masa ya yi ya kawo ya ba shi ya amsa, sai da ya fara sha ya kalli Bilal yace "Ina auntyn ka take?" "Ta na d'akin ta." Cewar Bilal ya na kallon k'ofar falon mahaifin shi, tura shi Nura ya yi yace "Je ka ce ina kiran ta, ka ce ta fito ta kwashi gaisuwa tare da albarka mai gida ya dawo." Da dariya Bilal ya nufi k'ofar falon mahaifin shi, cikin daka tsawa Khadija tace "Kai Bilal, ka na da hankali kuwa? Dallah malam dawo ka zauna min nan." Da mamaki duka su ka kalle ta, in da ta nuna masa da hannu ya zauna hakan ya bata damar kama kunnensa tace "Wallahi ka sake zuwa in da matar can take sai na b'ata ma ka rai, kaji ko?" Yanda ta d'aga murya tare da k'ara murd'e kunnen shi ya sa yace "Na ji Mummy, ki yi hak'uri ba zan k'ara ba." Nura da ke kallon ikon Allah ne yace "Khadija me ya sa za ki ma sa haka? Naga da ke da ita ai duk d'aya ne, iyayen shi ne ku." Tsaye khadija ta mik'e tace "Dakata min Nura, ni daban ita daban, wallahi duk yanda za ta kyautata mi shi ba za ta tab'a zama kamar ni uwar shi ba, dan haka kar ka sake had'a min yaro da wata banzar mata da ba ta san darajar shi ba, idan ka zo gani na ne na gode, idan wajen ta ka zo ka shiga ta na ciki." Juyawa ta yi ta shige uwar d'akin ta, mamaki ne ya kusa kashe Nura, dan shi dai a sanin shi wani ma ba su tab'a samun matsala da Khadija ba bare kuma dangin mijin ta, cikin sanyin jiki ya aje robar lemun hannun shi ya mik'e zuciyar shi na tunanin wane irin kishi ne da Khadija haka? Bilal ne ya mik'e yace "Tonton (uncle) Nura zan bika wajen Hajia." Shafa kan shi ya yi yace "To ka fara fad'awa Maman ka, idan ta amince sai ka d'auko kayan ka mu tafi." "To." Ya fad'a ya juya da k'arfi ya shiga d'akin, zaune ya same ta yace "Mummy, tonton Nura yace na d'auko kaya na mu tafi gida wajen Hajia." Cikin jin haushi tace "Babu in da za ka je, ka wuce d'akin ka ka kwanta ko kuma ka yi karatu." Hawaye ne su ka cika idon shi saboda shi dai haka ba ta tab'a faruwa tsakanin shi da maman shi ba sai yau, juyawa ya yi zai fita sai taji ya bata tausayi, amma kuma hushin ta da duk dangin Usman da suke murnar an mata kishiya, a hankali tace "Bilal." Juyowa ya yi ya dawo ya tsaya, hannun shi ta kama tace "Ka had'a kayan ka zan kira tonton Naseer ya zo yanzu ya d'auke ka, hakan ya yi?" Ba tare da sakin fuska ba ya d'aga kai alamar eh, fita ya yi Nura na tsaye yace "To ya? Za mu wuce ne?" Kamar zai fashe da kuka yace "Mummy ta hana." Ji ya yi kafin yace "Shikenan kar ka damu, ai gobe juma'a, watak'ila ku tafi gidan tare da Abban ka." Shiru bai ce komai ba har ya fita daga gidan ba tare da ma ya shiga wajen Haseenah ba, ta na kiran Naseer kam dama bai shiga gida ba, dan haka ya taho d'aukar shi, sai dai lokacin Usman ya shigo gidan, sun gaisa kamar yanda su ka saba tare da wasa da dariya, amma har Khadija ta had'awa Bilal kayan shi su ka tafi babu fara'a a tare da ita bare ta yi magana, a tak'aice dai haka duka gidan su ka gudanar da daren su babu armashi a ciki, dan Usman ya nunawa Haseenah kuskuren ta ma ko abincin ta bai ci ba, haka ma a d'aki da suka kwanta juya mata baya ya yi, dan in har za ta iya cin zarafin d'an shi har haka to fa akwai yiwuwar ya nuna mata ba'a mi shi wasa da gudan jini. Washe gari da safe ma haka abin ya ke, kasancewar Khadija ta san a wannan lokacin ya na d'akin shi ya na karatu ya sa ta shiga har can ta gaishe shi, bai wani yi karin kummalo ba ya yi shirin masallaci, *11:00* cif ya fita ya bar gidan zuwa masallaci kamar yanda ya saba, bai dawo cin abinci da rana ba sai aikowa da ya yi aka d'aukar ma sa, da yamma kuma ya kira Khadija yace su shirya dukan su za su je su yi barka gidan Issoufou, tunda magriba Khadija ta gama shirin ta tana jiran shi, Haseenah ma ba ta b'ata lokaci ba wajen shirin duk da fitar ta ta farko kenan, watak'ila ta na zumud'i ne saboda yace zai aje ta har gidan su ma su gaisa da mutane, ana idar da sallah isha'i ya shigo gidan, shi ma sai da ya sake shiri kafin su ka fita gaba d'aya, Haseenah ce baya tare da kwanukan abincin da zata kai gidan su. Babu mai magana a motar dan kowa da abin da ke ran shi, sai Khadija da ke latsa wayar ta hankali kwance, gidan su Haseenah su ka fara tsayawa dan ya fi kusa da gidan Issoufou, Usman da Haseenah ne su ka fita, amma ganin Khadija ba ta da niyyar fitowa ya sa ya kalle ta yace "Uwar gida sarautar ta motsa ne? Ko sai na fito da ke?" Ko kallon shi ba ta yi ba tace "Ku shiga kawai zan jira ku." Wani murmushi ya yi yace "Ke ma kinsan ba zan lamunci haka ba ai, fito mu wuce dallah." Cike da damuwa tace "Ba na cikin yanayin dad'i, ba na so kowa ya fahimci hakan har a dasa min hak'ora, dan ina fitowa za ace ba na da mutumci na fiya kishi da yawa." Bud'e murfin motar ya yi ya kamo hannun ta ta fito, bai saki hannun ta ba har sai da su ka shiga cikin gidan, sakin ta ya yi ya saci kallon ta yace "In dai ina da mahimmanci a wajen ki, to ki kankaro min mutunci na a gurin mutanen nan, kar ki bari laifin 'yar su ya shafe su." Kallon shi ta yi da farko turo baki ta yi, amma da ya marairaice sai ta saki fuskar ta na murmushi, Haseenah da tuni ta shiga gidan su ba ta ma san tsiyar da ke faruwa ba, sallamar su ce ta sa ta mik'e ta d'auko mu su kujeru su ka zauna, mahaifin ta na daga gefe zaune akan kujera, sai mahaifiyar ta na cikin sange zaune akan katifa da alama sunyi shirin bacci kenan, sosai su ka gaisa cike da mutunci da girmamawa, jim kad'an su ka mik'e Khadija na fad'in "Mama mu za mu wuce, saida safen ku." "To Allah ya bamu alkairi, Allah fisheku dare." Cewar maman. Da "Ameen." Su ka amsa, Haseenah kamar kar ta tafi take ji haka dai ta taso su ka fito, su na d'aukar hanya Usman ya kalli Haseenah ta madubi yace "Ke Hajia haka ake harkar duniya, daga kawo ki ku gaisa

Table of Contents

Chapters

117 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117