Skip to content

Chapter 48

Chapter 48

Kallon Kitse Book One Complete Hausa Novels 1,203 words 0 views Progress saved
Download Book

wani yanayi da ita dai ba ta tab'a ganin shi a ciki ba ya sa ta d'an kalle shi da mamaki, ganin nufota kawai ya ke ba magana ya sa ta k'ara yin baya da in'i'na tace "A..Abban...Bil." Ba ta k'arasa ba yace "Khadija akan me ku ka ci zarafin mata ta a gidan biki cikin mutane?" Mamaki ne fal a idon ta, rarraba ido ta fara yi sai motsa baki ta ke ta na so ta yi magana amma ta kasa, nuna ta ya yi da yatsa yace "To daga yau kar haka ta sake faruwa, idan ba haka ba kuma ran ki zai b'ace, sannan Hajia Turai ba na son ki sake mu'amula da ita, kinji na fad'a mi ki." Bai jira me za tace ba ya fita daga d'akin ya nufi d'akin Hassenah wacce ta buga tagumi ta na jiran ta jime zai faru, ya na ganin ta da wannan tagumin sai ya ji tausayin ta a tunanin shi akan abin da ya faru ne, ita kuma ba ta ma san me ya faru ba, zaune ya yi kusan ta ya kalle ta yace "Amarya ta, dan Allah ki yi hak'uri kinji akan abin da ya faru, insha Allahu na mi ki alk'awari hakan ba za ta sake faruwa ba." Cikin rashin fahimta tace "Me kuma ya faru? Akan me ka ke magana?" Jannyo ta ya yi jikin shi ya na shafawa yace "Idan ke ba ki fad'a min ba ai Hassana ta fad'a min, amma kamar yanda na fad'a mi ki ne ba zai sake faruwa ba in Allah ya yarda." Shiru ta yi a k'irjin shi ta na tunanin me ye ya faru to? Jin ta yi shiru ya sa ya d'agata daga jikin shi da cewa "Zan shiga wanka, amma ki tabbatar kin fito mun ci abinci ba sai na zo da kai na ba." Da kai kawai ta ma sa alamar to, fitowa ya yi ya nufi d'akin shi, ya na bud'a k'ofar ya tsallaka ya sake jin gaban shi ya tsinke ya fad'i tare da sarawar kai, hannu d'aya ya saka ya dafe kai ya rintse ido sosai, da k'yar ya iya furta "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un." Gaba d'aya jikin shi ne ya yi sanyi a haka ya cire kayan shi, zai shiga wanka Khadija ta yi sallama a d'akin ta shigo, shiru ya mata kamar bai ji ta ba har ta tsaya gaban shi, wani abu ya ke ji a zuciyar shi da bai tab'a jin irin shi ba tunda ya ke da ita, amma da ya ke sabon abu ne sai ya taushi zuciyar shi, a hankali ta rik'e kunnuwan ta cikin taushin murya tace "Ka yi hak'uri *sadauki na*, na karb'i kuskuren da k'awaye na su ka yi, kuma zanyi yanda ka ce da yardar Allah." Ba fara'a a fuska yace "Ya wuce." Ban d'aki ya nufa ta yi saurin rik'o hannun shi ya juyo, marairaicewa ta yi tace "Ka tab'a wanka da kan ka idan ban taimaka ma ka ba?" Wani murmushi ya yi kamar mai ciwon baki kafin ya ja hannun ta zuwa ban d'akin, sosai Khadija ta fahimci akwai sabon al'amari a tare da shi, dan har ta gama mi shi wankan nan ba su yi wata magana ba, kamar yanda sai dai ya mata murmushin yak'e kawai, haka ta gama mi shi shiri su ka fito cin abinci, sun zauna kenan Haseenah ta fito ita ma, tunda ya kafe ta da ido bai d'auke ba har ta zauna, murmushi kawai ya ke sakar mata har Khadija ta gama zuba abinci. Haka aka ci abinci babu wani nishad'i bare jin dad'i, su na gamawa ya nufi wajen Haseenah dan yi mata saida safe, ita ma Khadija shiga ta yi dan ta yi shirin bacci, amma har ta gama ta dawo bai dawo d'akin shi ba, abun mamaki shine har ta d'auki minti ashirin kwance kafin ya shigo, ya na can Haseenah na zuba shagwab'a wai zai tafi ya bar ta, ya na shigowa kashe wuta ya yi ya kwanta, zunbur Khadija ta mik'e da tafarfasar zuciya ta na kallon k'eyar shi tace "Me zan gani haka Abban Bilal?" Juyowa ya yi a kasalance yace "Me fa?" "Baya fa ka juya min, me na ma ka haka da zafi? Akan abin da ya faru ne? Dan Allah ka yi hak'uri in dai abin da ya faru ne zai sa ka juya min baya." Yanda ta yi maganar cikin muryar kuka ya sa k'wak'walwar shi hasko mi shi wacece ita, tashi ya yi zaune ya rumgumo ta jikin shi yace "Shikenan to ya wuce, ki yi hak'uri kar ki min kuka, ba na yi bane da gangan, kawai ba na jin dad'i ne." Da kuzari ta kwantar da shi akan gadon tace "Kwanta to na ma ka tausa." Cire mi shi rigar shi ta yi a hankali ta fara shafar bayan shi, yanda ta gama kashe mi shi jiki ya sa ya juyo ya sauke idon shi akan ta, da k'arfi ya fizgo ta ta fad'a jikin shi ya had'e labb'an su...saida safe. Kwana biyun da ya yi a wajen Khadija ya zo da al'ajabi, dan sosai ta ke gani bak'in al'amura daga gare shi, shi kan shi ya na jin wannan canji a tare da shi, amma tasirin wani abu ne ya ke mi shi togaciya ga abin da ya ke ji, asabar da yamma Haseenah ta karb'i girki, a daren ranar da ta yi anfani da maganin nan a marar ta ko da Usman ya kusanceta ya ji duk fad'in duniya babu maccen da ya ke son kasancewa da ita sama da ita, ba ma wannan bane yafi d'aga hankali kamar yanda ya ke jin kamar ita ce ma macen da ta fara gamsar da shi a shinfid'a, gaba d'aya ya nemi tasirin wata mace ya rasa, tun a daren ya fara ririta Haseenah kamar yau ya fara ganin ta ko sanin ta. Washe gari ma bayan ya fita ta sa aka samo mata fura ta dama, sosai ta had'a furar kafin ta zuba maganin na k'arshe a ciki, da kan shi ya zo cin abinci bayan ya kammala ta kawo mi shi furar cikin kofin tangaran mai kyau, kallon ta ya yi yace "Fita na ke so na yi fa, idan kuma na sha furar nan jiki na zai mutu na yu bacci." Cike da shagwab'a tace "Uhum uhum, wallahi ni dai ban yarda ba sai kasha, saboda kai fa na had'a." Take ya ji sak'on ya kai zuciyar ya ji ai tafi k'arfin ma ya yi gardama da ita, amsa ya yi tare da kurb'ar furar har ya shanye, mik'ewa ya yi ya shiga wanka ya na fitowa ko riga bai saka ba ya kwanta sai bacci. Da da magriba ta tashe shi ya yi alwala ya tafi masallaci, bai shigo gidan ba har ya yi sallah isha'i, ya na idawa ya d'auko hanyar dawowa a lokacin kuma Naseer ya dawo da Bilal gida, sun jima a k'ofar gidan su na kafin Naseer ya tafi shi ya shigo ciki, kai tsaye tare da Bilal suka shigo b'angaren Khadija, tunda ya hangi Khadija akan kujera ya ji wani bala'i ya taso mi shi tare

Table of Contents

Chapters

117 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117