Skip to content

Chapter 64

Chapter 64

Kallon Kitse Book One Complete Hausa Novels 1,200 words 0 views Progress saved
Download Book

ta yi sakayau da ita, domin ya bata hak'uri ya sa ya k'arasa bakin titin da ke ofishin wajen masu siyar da waya, nan fa ya siya mata tsandareriyar waya ta ban hak'uri haka Bilal, dan ya jima ya na si ya siya mi shi dan ya dinga game, saida ya tsaya ya yi sallah azahar kafin ya wuce gidan, har madafa ya same ta ya bata wayar, ta yi murna sosai ta masa godiya, kallon ta ya yi yace "Ina Bilal?" "Ya na falon maman shi, ba irin lallab'ar da ban masa ba ya fito ya k'i." Fita ya yi ya na fad'in "Ina zuwa." Ganin ya sa ta bi bayan shi dan kar azo tambayar Bilal wani abu zaiyi, tare su ka shiga ya na kwance da alama ma bacci ya ke ji, zaune ya tashi yace "Abba sannu da zuwa." Shafa kan shi ya yi ya na zama kusan shi yace "Yarima hutawa ake?" "Um." Kawai ya fad'a yayin da Haseenah ta harare su ta wutsiyar ido a zuciyar ta tace "Hum! Yarima dai yarima, ku ba ku gaji sarauta ba amma ku lak'abawa yaro sunan yarima, haba dai." Ta k'arshe da yin k'wafa. Ledar hannun shi ya mik'a mi shi yace "Duba ka ga tsarabar ka." A hankali Bilal ya ciro kwalin ciki, ya na ganin waya ce ya yi sauri budewaya fito da ita sai shek'i take, dariya ya yi ya rumgume mahaifin na shi yace "Abba nagode, na ji dad'i sosai." Rumgume shi ya yi cike da so da k'auna yace "Hakan na ke son ji dama." Karb'ar wayar ya yi ya had'a mi shi da kan shi in da ya janyo mi shi mega (data) daga na shi ma'ajiyin sannan ya nuna mi shi yanda zaiyi ya dinga janyowa duk lokacin da ya ke so, nan fa suka zauna su na ta danne danne a wayar ya na nuna mi shi abubuwa da dama, Haseenah kam in ranta ya yi dubu tabbas ya b'ace, musamman da ya nunawa Bilal yanda zai iya janyo data amma ita saida ya amshi wayar ya jawo mata, haka ta gamo girkin ta kawo tare su ka ci da yaro kamar yanda suke ci a baya a faranti guda, har la'asar ya na gida tare da Bilal saida su ka yi sallah a masallaci kad'ai ya fita yace zaije gidan, dan da safe bai je ya gaishe su ba. *Hajia Turai* ta na zuwa gida ta'aniya zazzaga bala'i, k'arshe dai shiryawa ta yi a motar ta taje gidansu Khadija, Khadija na falo sun gama girkin rana suna cin abinci ta zo gidan, nan fa ta tashi duk wani mai baccin rana a gidan ta na fad'a mu su wulak'ancin da Usman ya mata, Khadija da ta iya k'awar ta ta shiru ta yi saida ta kalle ta tace "Ke kuma sai magana na ke amma kin min banza, ko har yanzu ki na son mijin na ki?" Tasan in ba ta bita sannu ba sai sunyi baran-baran, dan haka tace "Haba kema dai bari fad'in haka mana, ai ni tuni na yi wuri na aje shi tunda ya tab'a min ke k'awa ta, kwantar da hankali kinji tawa ki manta da lamarinsu kawai." "Yawwa yanzu na ji magana, ai na d'aukar har yanzu ki na son komawa gidan shi." Ta fad'a ta na saka hannu cikin kwanon abincin, murmushi Khadija ta yi tace "Haba ina, ai sai a aljanna kuma idan da rabo mun had'u." Saida ta cika baki da abinci tace "Shegiyar yunwa na damu na, amma wannan mijin na ki ya k'i bari na ci abinci ya aika min da yan sanda gida na, ke kinga bala'i da zafin shi ni da Usman a ofishin yan sanda." Yanda Khadija ta santa tasan yanzu ma saita sake dawo da labarin baya, hakan ya sa Khadija cewa "Haba k'awa ta rabu da su kinji, ci abinci dai yanzu muje d'aki akwai hira." Wata dariya ta yi "Hahahaha, haka na ke son ji k'awa ta, ki barsu kawai wallahi lokaci na zuwa da saiya dawo da k'afafun shi ya neme ki, wallahi saiya durk'usa har k'asa ya na neman afuwarki, ita kuma wannan tsinannar ko, haba, yo an fad'a mi shi mu na wasa ne, ai iskancin ma ba haka kawai mu ke yin shi ba, wallahi ko uban..." Tabbas Khadija tasan cewa za ta yi uban shi dan ita ba damuwa bane gare ta, dan haka ta rufe mata baki tace "A'a k'awata, surukina ne fa, dattijon arzik'i ne babu ruwan shi." "Hakane kuma, ai da ina so na mi ki misali da gyatumin shine." Duk abin da suke fad'a mamar Khadija na gefe na saurarn su, dariya kawai take ba tare da sanin su ba, haka suka gama sun shiga d'aki nan ma kuma Salamatu ta zo wacce Khadija ta fad'a mata a waya tana gida, aifa d'akin Khadija kamar zai tsage saboda hargowar da suke yi, har k'arfe biyar na yamma suna gidan nan kafin suka tafi. A wajen Usman kuma ko da ya je gida bayan sun gaisa da Hajia ta tambaye shi ya iyali, nan fa ya kora mata bayanin abin da ya faru daren jiya, Malam da shigowar shi kenan ya rabka salati ya na fad'in "Fodio, me na ke ji kana fad'a haka? Ka ce ta tafi gidan su sai ka neme ta? Me ka ke nufi da haka? Fodio ba ka ji kunyar fad'in maganar nan ba dan Allah?" K'asa ya yi da kan shi baice k'ala ba, malam ne ya d'ora da "To tashi ka fita, kuma da anyi sallah isha'i ka zo ka d'auke ni k'afar ka k'afa ta muje mu dawo da ita, ni ba za ayi wannan haukan da ni ba kaji na fad'a ma ka." A hankali ya mik'e ya saka takalmin shi zai wuce ta gaban malam ya kalle shi da kyau har ya fita, kallon Hajia ya yi yace "Anya kuwa yaron nan lafiyar shi k'alau?" "Ni ma dai abin da na ke tunani kenan, ya na wasu abubuwa kamar ba'a hayyacin shi ba." Cewar Hajia da ke k'ok'arin d'auke tabarmar da ya tashi akai. "Ai kuwa sai a d'auki mataki tun kafin abu ya yi nisa, amma in ba haka ba taya ma zai ce Khadija ta tafi gida saiya neme ta." "Gaskiya kam." K'arasa shiga d'aki malam ya yi ya na fad'in "Allah ya sawak'e." Kamar yanda ya fad'a ana sallah isha'i ya dawo gidan ya d'auki malam, basu zame ko ina ba sai gidan su Dijeh wajen biko, karo na farko a rayuwar su da haka ta faru, sallama su ka yi tun farfajiyar gidan aka amsa, Ashir da kan shine ya mu su iso falon Mama, dan dama suna nan zaune dukan su, matansu ne suka fito tare da yara aka bar mazan tare da Mama sai Khadija da ke d'aki ta kan iya jiyo maganganun da suke. *'Yata kawai ki koma*😉 14/02/2020 à 16:55 - 💋😘💋: 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑 *KALLON KITSE* _(Ake wa rogo)_ 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑 _SAMIRA HAROUNA_ *Litattafan marubuciyar* *1* _KAUSSAR_ *2* _D'AUKAR FANSA_ *3* _BA SO BANE_ *4* _AUREN HAD'I_ *5* _SANIN MASOYI_ *6* _JIHADI_ *7* _K'ANGIN RAYUWA_ *8* _ITACE K'ADDARARMU_ *9* _KAWU NA NE_ *10* _MAATA_ *11* _KALLON KITSE..._

Table of Contents

Chapters

117 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117