Skip to content

Chapter 37

Chapter 37

Kallon Kitse Book One Complete Hausa Novels 1,199 words 0 views Progress saved
Download Book

Khadija kar ki ce min ba ki hango matsalar da ni na hango ba, hakan bai dace ba, kuma gaskiya ba na so, idan har zai yiwu, to cikin d'aya dole ku yi d'aya, ko dai ku had'a kanku ku dinga girki tare, ko kuma dai duk ranar girkin d'aya to d'aya ba za ta tab'a d'ora min tukunya ba da sunan girki ba, wannan hukuncin yankakke ne, kuma umarni." Mik'ewa ya yi ya juya ya kalli d'akin Bilal ya kalli agogon hannun shi, mik'ewa ta yi ta kalle shi tace "Ban k'i ta taka ba, amma kafin ka yanke wannan hukucin ya kamata ka fara fad'awa amaryarka cewa ba'a raba abinci a gidan nan, in dai har za ta ci gaba da ware mana abinci ni da yarona, to wallahi ba zan ci ba haka ma d'ana, kuma ko kaga ai bama zauna da yunwa ba alhalin Allah ya hore abinci ta ko ina, wannan shine." Ta gaban shi ta rab'a za ta wuce ya rik'o hannunta, kallon ta ya yi yace "Na fad'a mi ki ba na so, raba abinci kuma na yan kwanaki ne da ba su taka kara sun karya ba, idan ki ka duba tsawon lokacin da mu ka d'auka tare hakan bai tab'a faruwa ba, me ya sa yanzu za ki gagara fahimta Khadija? D'an lokaci fa kawai tace a bata ita ma ta san ta na da miji, me ya sa za ki zama mai son kan ki dayawa, me zai rage ki idan ki ka hak'ura ki ka ci abincin, nan da lokacin da kwananta zai k'are fa shikenan komai ya wuce." Rik'e k'ugu ta yi da hannu d'aya tace "Uhum! Anzo gurin, yau kuma sai gashi ka na fad'in wai ni ce mai son kai na, ni ce mai son kai na yau? To na ji kuma nagode, amma ka sani in dai wannan ne son kai to tabbas ni mai son kai na ce, wallahi ba zai tab'a yiwuwa ba ta barbarad'a min iskanci a abinci sannan ta bani na ci, wallahi ka ji na rantse ko ba zai yiwu ba, rai a baran mai shine, lafiya kuma uwar jiki, daidai da ciwon hannu wannan idan ya same ni akwai abin da za ka iya yi min ne? Ni fa zan ji zafin kuma na yi jinyata, hasalima duk soyayyar da ka ke sauki burutsun cewa kana min wallahi babu abin da za ka iya tsinana min, haka kawai kuma sai na jefa kai na a motar da na tabbatar ba ta da birki, rai fa guda d'aya ne." Yanda take masifa sai abun ya ba shi dariya da mamaki, a zaman shi da ita bai tab'a ganin ta na fad'a haka ba sai yau, b'ata rai ya yi yace "Wallahi ba da wasa nake ba, kar ki sake d'ora min tukunya indai har ana girki a gidan nan, kinji na fad'a mi ki." Za ta yi magana Bilal ya fito daga d'akin, sai kawai ta yi murmushi ta sa hannu ta shafo d'an gemunshi ta kashe masa ido tace "Ban ji da kyau, d'an sake maimaita min." Dariya ce ta so sub'uce mi shi sai ya dake ya matsa kusan ta ya rad'a mata a kunne "Wallahi karki sake na sake ganin kin aza girkin ki, in ba haka ba rai zai b'ace fa." Bilal ne ya shiga tsakansu ya na fad'in "Idan na bi taku sai na makara islamiyya, muje Abba." Hannun shi ya kama ya na juyowa ya na kallon Khadija, ita kam wani shegen murgud'a baki ta yi irin ai ba ka ma isa d'in nan ba, daga yanda ya motsa bakin shi ya tabbatar mata da k'wafa ce ya yi, gwalo ta masa tare da d'ora k'afa d'aya kan d'aya ta d'auki wayar ta, su na fita ta ci gaba da latsa wayar ta hankali kwance, kamar daga sama ta ke jin k'amshin daddawar kalwa na bad'e ko ina na gidan, tashi ta yi ta fito farfajiyar gidan sai ta fahimci daga madafar su ne ya ke fitowa, kai tsaye ta shiga ta samu Haseenah ta zage ta na tuk'a tuwon shinkafa, da murmushi Khadija tace "Amarya sannu da aiki, yau kuma tuwo ake mana?" Wani takaici ne ya taso ma Haseenah wacce ke wahalar tuk'a tuwon, k'ala ba tace mata ba sai Khadija ce ta sake cewa "Sai dai kuma mijinki baya cin tuwo da dare, ko bai tab'a fad'a mi ki ba? Musamman ma na ga wake ne ki ke miyar da shi, kuma ba ya cin wake ko kad'an, amma za ki iya had'a ma sa wani sassauk'an abun, mu sai mu ci tuwon dan munyi kewar shi." Ran Haseenah ne ya yi mugun b'aci tace "Kutumar uba, baiwar Allah na fad'a mi ki ina neman taimakon ki ne? Kinga Khadija, gaskiya ba na son haka, mijin ki ba ya cin tuwo a lokacin da ke kad'ai ce cikin gidan, yanzu kuma Haseenah ta shigo, dan haka ki barni na yi rayuwa ta mana, ki barni ni ma na kafa salon nawa tarihin a gidan nan kuma a zuciyar miji na, amma ba ki dinga min shishigi ba, ba lallai dan kin saba mi shi da saka kalar fari ba ki ce nima wannan kalar ki ke so na saka mi shi, ki barni na yi abin da ya dace, nan gidan miji na ne." Wani warrr Khadija ta yi da manyan idon ta kafin ta sa hannun ta tana fifita da shi tana fad'in "Wash Allah, zafi." Kallon Haseenah ta yi da murmushi tace "Sannu mai miji, Allah ya bar k'auna." "Ameen." Ta fad'a har da zaburowa, fita Khadija ta yi, tsaf Haseenah ta gama tuwonta ta mulmule, da kan ta ta kawowa Khadija na su tuwon, ko k'ala ita ma ba tace da ita ba har ta fita, Uwani ce ta tashi tafiya tace "Uwani d'auko wani kwano a d'akin can ki tafi da abincin nan." D'aya d'akin ta shiga da ke da tarkacai abubuwan buk'ata ta fito, juye tuwon ta yi ta tafi da shi bayan sun yi sallama, Bilal ne ya shigo gida shi kad'ai da takarda a hannun shi, rumgume maman shi ya yi ita kuma tace "Wa ya dawo da kai ne?" " *Bilyaminu* ne Abba ya tura ya d'auko ni, Mummy karb'i wannan." Ya fad'a bata takardar, ta na dubawa tace "Har wata ya k'are kenan?" Kai kaxai ya d'aga mata, ba shi ta yi tace "To ka aje wurinka idan Abbanka ya dawo sai ka ba shi, amma ni zan iya mantawa." A tare su ka tashi ita ta shiga d'akin ta saboda magriba ta gabato sosai, kaya kawai Bilal ya canza ya wuce masallaci, Khadija ma na idar da sallah ta shiga wanka, shiryawa ta yi sosai kafin ta lalabi gilashin ta na jiya da Usman ya cilla kan gadon, dan tun jiya bata waiwaye shi, shi ta saka dan ya fi mata kyau sannan ta fito, zaune suke ita da Bilal su na kallo su na hirar su, bayan sallah isha'i ko da su ka yi sallah abincin ranar da Uwani ta kwashe mata a kula ta d'auko ta zuba, tare su ka ci hankali kwance su ka k'oshi, hamdala su ka

Table of Contents

Chapters

117 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117