Skip to content

Chapter 49

Chapter 49

Kallon Kitse Book One Complete Hausa Novels 1,197 words 0 views Progress saved
Download Book

da sarawar kan shi, da gudu Bilal ya k'araso ya rumgume ta, rumgume shi ta yi cike da k'aunar d'an na ta tace "Yarima kai da wa?" D'agowa ya yi ya na cire jakar bayan shi ya na fad'in "Tonton Naseer ne." Gira ta d'aga sama tace "Uhum! Wato dai kun zama abokai ko?" Dariya ya yi yace "Mummy bara kiga abin da ya siyo min, kuma Hajia ma ta siyo min wani abu." Murmushi ta yi ta mayar da hankalin ta kan Usman tace "Sannu da shigowa Babban mutum." Wani irin amo ya ji muryar ta na mi shi cikin kunne marar dad'in ji da sauti, juyawa kawai ya yi ya fita ta k'ofar da ya shigo ya nufi na shi falon, ya na fita ya ji wani sak'at a zuciyar shi saboda ba ya ganin Khadija, Khadija kam abun ya bata mamaki sai dai hayaniyar Bilal da kayan da ya ke fito da su ya na nuna mata ya sa ba ta wani saka a kai ba, shi kam ya jima zaune sai ya d'auko tunani kamar akan bak'on al'amarin nan, amma kuma sai ya ji k'walwar shi ta yi wani jugum kamar babu komai a ciki, hakan ya sa ya yi tsaki sama da dubu kafin Haseenah ta shigo ta same shi. Dare ya yi dare Khadija ta kasa bacci ta na tsammanin jiran shigowar Usman amma babu shi babu labarin shi, tun Bilal na mata hira na abubuwan da suka faru a gida har bacci ya d'auke shi, haka ita ma baccin ya d'auke ta daga wurin ba ta ankara ba, haka har akayi sallaha asuba gari ya waye bai lek'o ba, shi kuma ya na can ko ya ji a ran shi ya zo sai kuma ran shi ya b'ace haka kawai, har Haseenah ta masa magana ya zo ya mu su sallama ya share kawai, dad'i ta ji a zuciyar ta amma a zahiri ta nuna bai dace ba. Washe gari da safe haka kawai Usman ya ji ba ya son fita ya yi nesa da Haseenah, ko k'ofar gida bai fita ba in ba sallah ya je yi ba, bayan sallah la'asar Aziza ta zo gidan tare da rakiyar k'awar ta, kai tsaye b'angare Khadija suka fara nufa saboda nan kad'ai k'ofar a bud'e, Khadija da a lokacin abun duniya ya isheta na rashin ganin Usman bayan kuma ta na da tabbacin ya na gidan, amsa sallamar ta yi a dak'ile tare da kallon su a raunane, har su ka zauna babu wanda ya sake magana, kallon Uwani ta yi dake gefe tace "Uwani kawo mu su abun sha ko." To." Ta fad'a ta na mik'ewa, k'ala Khadija ba ta sake cewa komai ba har Uwani ta dawo da abun sha, sai lokacin Aziza tace "Aunty Khadija wai ina Bilal? Ban gan shi ba." Kallon ta Khadija ta yi cike da rainin wayo saboda tunawa da ta yi ranar da taji Aziza da bakin ta tana kiran d'an ta shege, a kaikaice ta sake kallon ta tace "... *Allah ka bawa dukanin musulmi lafiya.* 06/02/2020 Γ  22:23 - πŸ’‹πŸ˜˜πŸ’‹: πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘ *KALLON KITSE* _(Ake wa rogo)_ πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘ _SAMIRA HAROUNA_ *Littatafan marubuciyar* *1* _KAUSSAR_ *2* _D'AUKAR FANSA_ *3* _BA SO BANE_ *4* _AUREN HAD'I_ *5* _SANIN MASOYI_ *6* _JIHADI_ *7* _K'ANGIN RAYUWA_ *8* _ITACE K'ADDARARMU_ *9* _KAWU NA NE_ *10* _MAATA_ *11* _KALLON KITSE..._ *SADAUKARWA GA* _MATAN FARKO_πŸ§•πŸΌ *(UWAYEN GIDA)* πŸ‡ΈπŸ‡¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S* _(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_πŸ€œπŸ€› ```Fatan alkairi masoya``` *πŸ‡ΈπŸ‡¦ZAMAN AMANA WRITER'S* (GIDAN ZAMAN LAFIYA DA AMANA INSHA ALLAH)πŸ€œπŸ€› *SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!!* *INA JIGA JIGAN MASOYAN πŸ‡ΈπŸ‡¦ZAMAN AMANA WRITER'S WAD'ANDA BASU DA TAMKA A WAJENMU????? DUK WANDA YAKE TARE DAMU A CIKIN GROUPS D'INMU TO MUN TABBATAR K'AUNARMU CE TASA KUKA KASANCE TARE DAMU, MUNA YABAWA KUMA HAR ABADA BAMU DA KAMARKU WALLAHI,πŸ‘ DUK DA HAKA DAI GA LOKACI YAZO, KUMA DAMA TA SAMU NA TABBATAR MANA DA KUMA NUNA MANA HAK'IK'ANIN K'AUNAR DA KUKE MANA,πŸ‘‡* Kunsan cewa k'ungiyarmu *πŸ‡ΈπŸ‡¦ZAMAN AMANA WRITER'S* suna cikin gagarumin gasa na samun award Wanda *women24 TV WhatsApp group* suka shirya kuma zasu gudanar? A wannan gasar ne za'a samu k'ungiyar da tafi kowacce k'ungiya yawan fans da Kuma bin k'a'idar rubutu Dan ki samu damar zabar k'ungiyarmu *πŸ‡ΈπŸ‡¦ZAMAN AMANA WRITER'S ASSOCIATION* zaki iya tuntub'ar wannan lambar 09030159301 Dan su saki a *WOMEN24 TV WHATSAPP GROUP* anan ne za'ayi zab'en k'ungiyar da tafi kowacce k'ungiya yawan masoya *Women24 Tv* Ba zabe kad'ai zakiyi ba Zaki k'aru da abubuwa da yawa kamar haka *Yanda ake girke girke* *yanda zaki gyara jikinki* *yanda zakiyi makeup* *yanda zaki daura Dan kwali* Kuma suna shirye shiryen nan na *arewa24 tv* kamar su *TARKON KAUNA* *DADIN KOWA* *KWANA CHASA'IN* *JAMAI RAJA* *SAPNE SUHANE* *GIDAN BADAMASI* *RUDIN ZUCIYA* *BAGHYA LAKSHMI* *AKUSHI DA RUFI* *AUDIO NOVEL* *HAUSA NOVELS* Kada ki manta da ranar zabe inkin shiga group d'in ki zaba *πŸ‡ΈπŸ‡¦ZAMAN AMANA WRITER'S* tanan ne zaki iya nuna mana irin sonda kuke ma k'ungiyarmu da littattafammu, kuma a ko'ina ko a kowace k'asa masoyanmu suke sunada damar zab'enmu ba sai 'yan nigeria kad'ai ba. Allah yabar zumunci🀝😍πŸ₯°πŸ’‹ _Bismillahir rahamanir rahim_ *20* "Bilal ya na nan, kinyi kewar shi ne har haka?" Wata 'yar dariya ta yi tace "Ban gan shi bane ba ai." "Uhum." Cewar Khadija can k'asan mak'oshi, jim kad'an Khadija ta kalle su tace "Ku wuce ciki mana ai suna nan, dan nasan wajen su ku ka zo." Cike da kunya Aziza ta d'anyi jim kamar ba za ta tashi ba, a hankali su ka tashi tace "Bara mu gaishe ta sai mu wuce." Da ido kawai ta bisu ba tace k'ala ba, saida su ka fita ta gyara zaman ta, su kuma sun jima bakin k'ofa su na bubbugawa tare da sallama amma shiru, da k'yar Haseenah ta fito cikin riga da wando ta bud'e, saida ta saki wani d'an k'aramin tsaki saboda ganin su, washe baki ta yi ta na fad'in "A'a'a'a, su Aziza ne a gidan mu? Sannun ku da zuwa, ku shigo mana, ashe ku ne ke ta bubbugawa, ina wanka wallahi." Duk ta yi maganar ne lokacin da suke shiga ciki, zaune su ka yi ita ta wuce ciki, da kallo su ka bita kafin su mayar da kallon su kan telebijin, Usman ta samu kwance akan gadon ta kamar mai son yin bacci, da k'yar ta samu ta rabu da shi ta sanyo hijabi ta fito, nan fa su ka shiga hira dan dama Usman yace kar ta gajiyar masa da kan ta za su fita cin abinci tare, dan haka ba ta damu ba har Aziza ta d'an kalle ta dan ita dama madafar ta ke son shiga, cikin taushin murya tace "Auntyn mu yunwa fa na ke d'an ji." Hararan gefen wutsiyar ido ta wa Aziza amma a zahiri ta yi dariya tace "Ki ke d'an ji ko ki ke ji?" Dariya su ka yi tace "To na ke ji, akwai indomie?" "Kinsan ai ba za'a rasa ba, bara na d'ora mu ku" Ta fad'a cike da k'arfin hali, Aziza ce tace "Ah haba dai amaryar mu, ina mu ina saka ki aiki, yayan mu fa na d'aki, dan haka ki bar mana komai ni zan shiga da kai na, ko kin

Table of Contents

Chapters

117 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117