Chapter 101
Chapter 101
zaisa ya dinga kallonki da daraja da kima, saboda kina son abin da yake so, amma kishi da hauka da wauta sai ta saka mu rufe idonmu mu nuna k'iyayya da kishi kan abinda suke so, yanzu dai gashi kalaman da a baya bai iya fad'a mata yanzu gashi ya na kallonta ya fad'a mata, kenan ta jima ba ta mutu ba, Allah kasa mufi k'arfin zuciyarmu.* D'orawa ya yi da "Saboda da ita na fara had'uwa, ita Allah ya fara bani kafin ya bani Bilal, ita ce wacce Bilal d'in ya fito daga jikin ta, shi ya sa na ke mata k'aunar da ko shi Bilal ba na masa, zanji zafi matuk'a idan aka ce yau na rasa Bilal, amma kuma zanyi farin ciki idan na waiga naga Khadija a gefe na, ba dan komai ba saidan nasan za ta sake bani wani Bilal d'in." Ya na gama fad'a ya juya ya bar d'akin ya koma na shi ya kwanta ya rumgume Bilal kamar zai had'e shi, ya na shafa shi har bacci ya d'auke shi shima, Haseenah kam kuka ta fashe da shi mai tsanani, wai abin da a baya yake ma sayawa baya fad'a yau gashi ya fad'a, kai lallai abin nan bana lafiya bane, tunaninta ne ya bata duk wani shiri da tayi a kan shi ya wargaje, dan haka dole ta sake sabo, da haka ita ma ta yi bacci da tunanin kiran Mariya idan gari ya waye. *Luv u all.*π 09/03/2020 Γ 15:01 - πππ: ππππππππππ *KALLON KITSE* _(Ake wa rogo)_ ππππππππππ _SAMIRA HAROUNA_ *Litattafan marubuciyar* *1* _KAUSSAR_ *2* _D'AUKAR FANSA_ *3* _BA SO BANE_ *4* _AUREN HAD'I_ *5* _SANIN MASOYI_ *6* _JIHADI_ *7* _K'ANGIN RAYUWA_ *8* _ITACE K'ADDARARMU_ *9* _KAWU NA NE_ *10* _MAATA_ *11* _KALLON KITSE..._ *SADAUKARWA GA* _MATAN FARKO_ π§πΌ *(UWAYEN GIDA)* πΈπ¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S* _(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_π€π€ ```Fatan alkairi masoya``` _π Masoya wannan littafi wannan kyautar ku ce, nagode da soyayyar da kuke nuna min ni da kaya naπ, Allah ya barmu tare._π _Bismillahir rahamanir rahim_ *37* Ko da gari ya waye Bilal ya shirya cikin k'ananan kaya dan yau alhamis ce ba karatu, Usman ma kamar kullum cikin shadda ruwan madara ya shirya, tare suka fito falon Haseenah sun same ta zaune tana waya da Mariya, bayan ta fad'a mata akwai matsala ne Mariya tace ta sake fito da kud'i kawai a mata aiki, kafin ta yi magana ta ji fitowar su hakan ya tilasta mata aje wayar, juyowa ta yi ta na kallon su, duk da cikin hushi take amma tabbas tasan an samo Bilal ne daga Usman, dan zubin hallitarsu ma iri d'aya ce, duk da ba ta zauna da yaron sosai ba amma ta fahimci ya na da miskilanci fiye da ubansa, kai tsaye teburin cin abinci su ka nufa dan ba su ma lura da ita a zaune ba, saida ta ga sun zauna ta taso ta nufo su dan zuba mu su abinci, sai dai ta na mamaki yanda yau Usman zai ci abincin ta tunda ya jima baici ba, shi kuma zai ci ne kawai saboda Bilal na gidan yau, amma sam baya sha'awar cin abincin ta tunda ya lura kullum abinci kala d'aya ta iya sarrafawa, tun kafin ta tsaya wajen Bilal yace "Aunty ina kwana?" Cike da makirci ta shafo kan shi tace "Yarima, ashe gidan mu ka kwana jiya, lokacin da ku ka shigo har na yi bacci, ya ka ke?" Shi kam yaron fuskar shi ba fara'a yace "Lafiya lau." Kallon Usman ta yi wanda ke kallon cikin ta shi ma tace "Ina kwana babban mutum?" Ba walwala a tare da shi yace "Lafiya lau, ya jikin na ki?" Da murmushi ta amsa da "Da sauk'i sosai." Shayi ta fara had'awa Bilal ta aje ma sa kafin Usman d'in, tare su ka karya dukan su bayan sun gama Usman ya mik'e zai fita, hannun Bilal ya kamo yace "Muje ko yarima, yau da kai za mu fita." Da zumud'i ya mik'e tsaye dan bin mahaifin shi amma sai Haseenah tace "Haba dai babban mutum, wannan ma ai son kai ne wallahi, yaushe rabon da na ga Bilal, yau ya zo kuma shine za ka fice da shi, gaskiya ni dai ban yarda ba." Kallon ta ya yi yace "To ya ki ke so ayi?" Kallon Bilal ta yi tace "Ka bar min shi mana, anjima idan ka dawo sai ku fita tare." Duk da ya samu labarin dalilin da yanzun mahaifiyar shi ke gida, amma kuma ba ya jin akwai wani abu da za ta iya yi wa Bilal tunda ya na gari, ajiyar zuciya ya sauke ya kalli Bilal yace "Yarima, ka zauna tare da auntyn ka kaji, zan fita amma ba zan jima ba zan dawo, idan kuma ka gaji da zaman gidan ka na iya fita k'ofar gida wajen Rabe sai kuyi hira." Saida Bilal ya kalli Haseenah kafin ya kalli Usman yace "To Abba, amma fa kar ka jima sosai." Dafa kan shi ya yi yace "Ba zan jima ba insha Allahu." Saida ya sumbace shi kafin ya kalli Haseenah yace "Ba wani abin da ki ke buk'ata?" Sosa kai ta yi irin na kunyar nan ta kasa magana, hannu kawai ya sa aljihu ya fito da kud'i ya bata, karb'a ta yi ta mi shi godiya kafin tabi bayan shi har ya shiga mota, Rabe da ke zaune da littafin karatu (dan tunda aka ce za'a maidashi makaranta abun ya sake shiga ran shi) ya taso suka gaisa kafin ya bud'e mi shi k'ofa ya fice ya na binshi da addu'a, rufewa ya yi har ya zauna Haseenah ta k'wala mi shi kira ya zo, tsaye ya ke kamar yanda take su na kallon juna tace "Wannan pliwoyin ka basu ruwa mana, ya ka ke abu kamar ba ka san aikin ba ne." Wani kallon raini ya mata dan babu abin da bai wani ba game da ita kafin yace "Tofa, to na ji zan ba su ruwan, shikenan?" Ya na fad'a ya juya ya bar mata wajen, ciki ta koma ba ta damu da shi ba dan a cewar ta k'aramin arne ne shi ba ta shi take ba, yau dai ba wata matsala tsakanin ta da Bilal, ya na zaune gefe ta na zaune ita ma sai dai su kalli juna, dan dama ba tace ya bar shi bane saboda ta na da wani nufi akan hakan, kawai ta fahimci ta b'ata mi shi rai ne jiya saboda abin da ta fad'a, ana hakane ta shiga madafa d'ora girkin rana, ba jimawa da fara aikin Bilal ya shigo da sallama, amsawa ta yi tace "Ya dai?" Cikin ladabi yace "Aunty dama zanje gidan aboki na *Abdallah* yanzu zan dawo." "To shikenan sai ka dawo, amma kar ka jima kuma uban ka ya dawo ya min tijara." Ta fad'a ta na ci gaba da aikin ta, da sauri ya fita ko amsa ta biyi ba, ashe Bilal moton shi ya d'auka ya fita da shi Haseenah ba ta ma sani ba, Rabe kuma tunda bai san ba'a barin shi fita da shi ba shima bai hana shi ba sai ma bin moton da kallo da ya yi har
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117