Chapter 54
Chapter 54
gaskiya matsayi na bai taka wannan matakin ba, ka yi hak'uri idan na b'ata maka rai." Ta na fad'a ta rufe kwanukan ta juya ta bar wajen, komai bai ce ba sai bayan Haseenah da ya bi da abincin ya lallab'a ta har ta ci, saida su ka gama kad'ai ya samu ya fita, saida ya shiga wajen Khadija ya same ta falo zaune, tsaye ya yi a kan ta ya ciro kud'i aljihun shi ya mik'o mata yace "Ba na da tabbacin za ki yi abin da na saka ki, amma dan Allah ki taimaka ki mana abinci mai yawa saboda ba zan dawo ci ba, zan aiko a d'auka saboda akwai bak'in da su ka zo mana." Karb'a ta yi da hannu biyu tace "Zanyi farin ciki a lokacin da nake aikin nan, saboda hidimar ka ce." Juyawa ya yi zai fita ta bishi da "Adawo lafiya." "Allah ya sa." Ya fad'a a tsaurare. Tun k'arfe d'aya Khadija ta kammala komai kamar ba ta yi ba, sai bayan sallah azahar Usman ya aiko aka d'auki manyan kwanukan tare da lemun da aka had'a na zallar abarba, ba jimawa ta kira shi tace su na so su koma ganin jikin Baba, cike da k'aguwa yace "Kuje, amma ki tabbatar tare ku ka tafi da Haseenah, dan ba na son raba kan nan da ku ke, sannan kar ki manta su na gida an sallame su." Kafin ta yi magana ya datse kiran, dama a shirye take ita kam, Uwani ta kalla tace "Uwani ki je ki fad'awa Haseenah ta shirya yanzu za mu tafi ganin jikin Baba." "To." Cewar Uwani ta nufi hanyar fita, jim kad'an ta dawo tace "Na fad'a mata tace ta na zuwa." Kallo suke su na hira har sama da awa d'aya Haseenah ba ta fito ba, Khadija ta k'agu sosai dan haka ta kalli Uwani tace "Uwani dan Allah koma ki sake fad'a mata ta gaggauta, har uku ta na shirin yi mana a gida ba mu fita ba, ni kuma a wannan lokacin madafa ya kamata ace zan shiga." Fita Uwani ta sake yi, amma ko da ta dawo sai cewa ta yi "Umman Bilal wallahi da na shiga na same ta kwance akan kujera da d'aurin k'irji, da na fad'a mata sai tace wai da zata shiga wanka, amma kula ba ta jin dad'in jikin ta kawai ki tafi za ta je daga baya." Saida Khadija ta lumshe ido saboda haushi, mik'ewa ta yi ta kalli Bilal tace "Ka koma d'aki ka sako kayan makarantar ka daga nan saina aje ka, dan banga anfanin dawowar ba tunda mun riga da mun makara." "To Mummy." Ya fad'a ya na nufa d'akin shi, bayan yan mintuna ya dawo da kayan makarantar shi da jakar shi a hannu, Khadija kuma bawa Uwani makullai tace "Ki rufe ko ina sai ki same ni a mota." Karb'a ta yi ta kulle ko ina ta fita waje ta same su a k'ofar gida su na jiran ta, shiga ta yi su ka wuce suna tafe su na hira har suka isa, Uwani ce ta fito da kwanukan ita kuma ta na rik'e da jakar ta, haka suka shiga bayan sun gaisa suka zauna aka d'an tab'a hira, ana fara kiran sallah Khadija ta tashi su ka yi alwala su ka yi sallah, suna gamawa kuma suka musu sallama suka tafi saboda kar Bilal ya makara, haka suka aje shi sannan suka wuce gida kai tsaye, da shigar su ta hangi motar Usman, ba ta yi mamaki ba dan tasan wasu lokuta ya kan dawo ya yi wanka, su na shiga falon su suka ja birki ita da Uwani saboda ganin Usman zaune kai da gani kasan babu arziki ko mutunci cikin zaman, gabanta na fad'uwa ta k'arasa kusa da shi tace "Abban Bilal ashe ka dawo? Sannu da zuwa." Uwani ya ma jan kallo yace "Kira min Haseenah." Wucewa ta yi ba tace komai ba dan dama tun farko ya na mata kwarjini, Haseenah ta kira suka fito kusan a tare, tsaye duka su ka yi sai Uwani da ta fita farfajiyar gidan, tsaye ya mik'e yace "Nace ku tafi tare, amma me ya sa ki ka tafi ki ka barta?" K'aramar ajiyar zuciya ta sauke ta kalli Haseenah tace "Na fad'a mata ai, da farko mun jira ta sai tace ba ta jin dad'i mu tafi kawai." Kallon Haseenah ya yi yace "Ke ya ki ka fad'a min?" Ko kallon Khadija ba ta yi ba ta kalle shi tace "Bansan za su tafi ba, fitar su kawai na gani daga gida, idan da ta fad'a min ai zan bisu tunda lafiya ta k'alau." Kallon Khadija ya yi yace "Na d'auka zan iya fad'a mi ki kiji ashe ba haka bane, yanzu ina so naji raina ni ne ki ka yi ko me?" Da mamaki ta kalli Haseenah ta kalle shi tace "Amma fa wann..." "Amma me, ki na so ki nuna ba na da mahimmanci ne ko me? Zan fad'i yanda na ke so ayi a cikin gida amma ke kiyi gaban kan ki, wannan ai iskanci ne da d'aukar mutane yan iska, to ban makullin motar." Da mamaki kawai ta ke kallon shi kafin tace "Makullin mota kuma?" Zaro ido ya yi yace "Eh, ko taki ce? Ai ba yan uwan ki bane suka siya mi ki bare ki ji dad'in magana, ni ne na siya da kud'i saboda tunanin kin cancanta." Hannu tasa a jaka ta fito da makullin ta mik'a mi shi, hannu ya zuro zai karb'a ta rik'e tace "Zan baka, amma ina so ka k'ara bincike akan lamarin nan, sanin kan ka ne wannan yarinyar ba ta kai na tsaya na mata k'arya ba, Uwani ita ce na aika ta mata magana, kuma Bilal ya na wajen." Haseenah ce ta katse da cewa "Uwani? Ita ce tace mi ki ba zanje ba? K'arya take wallahi, wannan yarinyar fa munafuka ce wallahi." A fysace Khadija ta kalle ta tace "Kar ki sake kiran Uwani munafuka dan ba ita ba ce, Uwani ba yau mu ke tare da ita ba, nafi sanin ta fiye da ke kamar yanda shi kan shi ya fi sanin ta fiya da ke." Cike da rashin kunya tace "Idan an kira ta munafukar me za ki yi? Me ya sa ki ke son had'a yar aikin gidan nan da mu ne? Da alama wata rana ma cewa za ki yi matar shi ce ita ma." "Kai." Ya daka musu tsawa, cikin b'acin rai yace "Akan wata banzar yar aiki ne za ku tsaya kuna musayar yawu? Ba na so, kowace ta wuce d'akin ta." "Banza? Uwani ce banza?" Cewar Khadija ta na kallon shi, "Eh na fad'a, ko nima rashin kunyar za ki min?" Rumgume hannaye Haseenah ta yi tace "To ai ba ka wuce ta maka ba tunda ka tab'a yar gold d'in ta, wallahi yarinyar can munafuka ce ta gidan gaba, ranar ma ai duk ita ta haddasa masifar da matar ka ta kusan k'ona ni da raina." "Oho, hakane kenan?" K'ofar fita ya nufa ya na fad'in "To bara ki gani, yau zata bar gidan nan kuma na ga wanda ya isa ya hana tunda gida
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117