Chapter 28
Chapter 28
cikin da ku ma da ke yan uwana ba ku ba ni shi ba kafin zuwan ta rayuwa ta, dan haka in dai har ku na son zama da ni to dole harshenku ya san me zai dinga fad'a akan mata ta." Ya na fita Hajia ma ta mu su fad'a sosai tare da tuna mu su baya, daga ranar kuma ba su sake yarda sun b'ata Khadija ba a gaban iyayen su bare kuma Usman, amma abin takaicin shine k'iyayyar da su ke ma Khadija sai ta shafi har Bilal, dan yanda su ke ganin Bilal na wahalar da mahaifin shi, yaro ya zama saurayi amma kamar k'aramin yaro, ba ma in sun had'u da shi gidansu Hajia, ya kan zo da kayan ciye ciye ma su tsada da kyau da dad'i, duk abincin da za'a mi shi tayi ba zai ci ba, haka mahaifin su malam Ali zai dinga biyewa yaron ya na siyo mi shi duk abin da ya ke son ci, to fa ana hakane har Allah ya had'a Usman da Haseenah, lokacin ya na yawan zuwa wajen wani shago da ke can wajen filin kokawa saboda wasu kaya da ya ke kawowa mai shagon, a nan ya had'u da Haseenah wacce a lokacin ta samu exam (brève) d'in ta ta na zaune gida, baban ta ne ya tilasta mata komawa makarntar islamiyya dan ta k'ara samun ilimin addini, a lokacin har nik'abi take sakawa da dogon hijab, wannan nutsuwa da hankalin na tane su ka sa Usman jin kamar ya samu wata Khadija, fatan shi shine ta zama kamar yanda ya ke tunani, bayan ya yi tambaya a kan ta an fad'a mi shi yarinyar kirki ce daga gidan mutanen k'warai, sai kawai ya gabatar da kan shi a matsayin yana son auren ta, duk da bai cika magana akan matar shi ba, amma ya fad'a mata ya na da mata d'aya da yaro d'aya, kuma ya na matuk'ar son su, a lokacin da su ka fara soyayya Usman na bata lokaci wajen waya da Haseenah har dare, sannan duk abin da ta yi ya kan yaba hakan kamar d'abi'ar shi ce, amma a tunanin Haseenah matar shi ba ta da kulawa ne shi ya sa har za ta yarda ya na waya da ita tsawon dare ko ya na gari, abin da kuma ba ta sani ba shine duk lokacin da ya ke wayar da ita to ba ya gida, Khadija kuma ba ta damuwa saboda ta san in baya gida yana tare da su Murtala, ta na ba shi lokaci sosai da ya ke jin dad'in rayuwar shi shima kamar yanda ya ke wuni tare da ita da safe har zuwa yamma, ko kwalliya ta yi taji yana kod'ata sai tace wai uwar gidan shi ba ta yi shi ya sa idan ya ganta da kwalliya kamar ya ga matar aljanna, hakan ya sa ta sawa ranta ta na zuwa gidan za ta cinye yak'in ba tare da tasha wahala ba, amma kuma gashi Mariya ta kawo mata wani labari da ya sa har ta fara had'awa da malamai. _Toh, ko tunanin Usman ya fad'a mi shi daidai? Shin Haseenah za ta zama kamar yanda ya d'auka? Ko kuma dai *kallon kitse ne ya ma rogo*?_ *Mu koma labari* Ko da ya dawo daga kan Bilal kai tsaye falon shi ya wuce, sak'o ya turowa Khadija ta same shi falo haka ma Haseenah da ke d'akin ta, hakimcewa ya yi ya na jiran zuwan su, (da alama Usmanu yan mulkin sun motsa, yau kam duk wacce ta yi wasa za ta gane shayi ruwa ne 😉), kusan a tare su ka shigo falon sai Khadija da ta k'ara da sallama, zaune su ka yi su na fuskantar shi su na kallon shi, d'ago kan shi ya yi ya kalli Haseenah ya kalli Khadija kafin yace "Kun gaisa ne da safen nan?" Khadija da tasan waye mijinta ne ta yi saurin cewa "Sosai ma, har falo ta same ni ai, mun gaisa da ita." "Da kyau." Ya fad'a ba annuri kafin ya d'ora da "Ku zuba mana abinci mu ci." Satar kallon shi Khadija ta yi dan tasan ya same ta tana karin kummalon ta, amma jin haka daga bakin shi da kuma ganin yanayin shi ya sa tasan yau ba ya yanayin wasa, dan haka ta mik'e tare da Haseenah da ke ta wani yauk'i kamar za ta karye, murmushi ta mata tace "Kinga amarya zauna, ki zauna zan zuba." Ci gaba ta yi da zuba ma kowa har ta gama ta aje farantin a gaban shi kafin ta matso kujerar ta kusa da shi, sai da ya fara saka hannu tare da bismillah sannan su ma suka saka, Haseenah dama haushi ne kamar ya kashe ta, Khadija kuma a k'oshe take neman agaji take, a tare su ka cire hannun su suna kallon shi, shi ma kallon su ya yi yace "Me ku ke nufi?" Cikin wata shegiyar shagwab'a Khadija tace "Mun k'oshi." Duk daba kuzari a tare da shi sai da ya murmusa yace "Ku na nufin ni kad'ai za ku bari? Ai ba ku isa ba, dan haka ku mayar da hannuwan ku." Kamar za ta fashe da kuka ta shafa cikin ta tace "Ciki na fa zai fashe, ka ci kawai sai ka had'a da nawa ka ci." Sama da k'asa ya harare ta yace "Sannu mai wayo, kenan ni na cika cikin nawa? To na k'i wayon." Mik'ewa ta yi tace "To bari na je na amaye wanda na ci sai na dawo mu ci gaba ko?" Da gayya Khadija ta dinga tafiya ta na wani juya k'ugunta, mazaunan ta na kad'awa yanda su ke so, sai da ta kai k'ofar fita ta juyo ta kalle shi dan dama a sanin da tawa mijinta ba ta ba da baya bai bita da kallo ba, su na had'a ta ga ya wani saki baki ya na kallon ta, cije leb'e ta yi ta kashe ma sa ido d'aya ta fice da murmushi, Haseenah Usman ta bi da kallo ganin ya wani wagale baki har da rumgume hannaye ya na kallon ta, sai da yaga ficewar Khadija ya sauke wata sayayyar ajiyar zuciya da murmushi a fuskar shi wanda shi kad'ai ya san ma'anar shi, a hankali ya zuro hannun shi cikin farantin da nufin ci gaba da cin abincin shi sai ya lura da Haseenah da ta kafe shi da ido, saita nutsuwar sa ya yi yace "Ya dai?" Ita ma had'e abin da ke ran ta tayi tace "Ranka shi dad'e, wai me ya sa aunty Khadija ke jin dad'in anfani da gilashi a kowane lokaci? Ba ta tsoron ta samu matsala a idon ta." Kallon ta ya yi ya na tunani, bayan gamsuwa da zuciyar shi sai kawai yace "Haseenah kema yanzu iyalin gidan nan ce, ba wani abu da za'a b'oye mi ki, Umman Bilal na fama da larurar ido ne, kuma anyi neman maganin amma har yanzu shiru ba labari, sai dai har yanzu ba mu cire rai da rahamar ubangiji ba, mu na sa rai wata rana za ta samu lafiya da yardar Allah." D'auke idon ta ta yi daga kan shi ta kalli
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117