Skip to content

Chapter 38

Chapter 38

Kallon Kitse Book One Complete Hausa Novels 1,202 words 0 views Progress saved
Download Book

yi kafin su ka tashi kamar ba su ci ba. Kamar yanda ya yi alk'awarin komawa gida haka ya wuce, ya kuma samu su Kabir Mannir da Nura, hakan ya sa suka bud'a babin hira su ka dinga yi, Haseenah da ke jiran shigowar shi taga shiru sai da ta kai ga kira, amma sai ya d'aga yace ya na gida zai zo ba da jimawa ba, amma fa bai zo d'in ba saboda suna tattaunawa da ahalin shi, sai wajen *22:20* ya baro gidan ya nufi gida, Khadija har sun kwanta ita da Bilal ya shigo, ko da ya ga babu wuta a falon sai ya wuce falon shi kai tsaye, Haseenah na ganin shi ta d'ago kai ta kalle shi, ba fara'a ko sakin fuska tace "Sannu da zuwa." Sai da ya kamo hannun ta tayi tsaye ya rumgume ta yace "Sannu da gida." Kamar ba ta son magana ta amsa da "Yawwa." Kallon fuskarta ya yi yace "Ki yi hak'uri na barki ke kad'ai ko? Ina can gida tare da yaran nan su na ta min shirme." Cikin shagwab'a tace "Na ji to, yanzu dai mu je ka yi wanka sai ka zo ka ci abinci." Rimgume ta ya yi yace "Wallahi kamar kinsan kam na d'ebo yunwa, muje ki kintsani yanda ya kamata." D'akin shi su ka nufa, bayan ta taya shi wanka ya canza kaya su ka fito, ya na jan kujera ya kalle ta yace "Da alama su Bilal har sun kwanta ko?" Kallon shi ta yi tace "Eh to ban sani ba dai, amma tun da na ji shiru babu hayaniyar tv na ke tunanin haka." Ba tare da ya kalle ta ba yace "Haseenah me zai hana idan ba na nan ki dinga zuwa wajen su ki na zama ku na hira? Ina ga hakan ai zaifi ko? Tunda daga ke sai sune a gidan, kuma sune abokan rayuwar ki a yanzun." Ta na aza marar tuwo a farantin ya kalle ta, bai kai ga jin amsarta ba yace "Haseenah tuwo ki ka dafa?" Kallon shi ta yi tace "Eh, da matsala ne?" Ya na ci gaba da kallonta yace "Khadija ta ga ki na aikin nan?" Sam Haseenah ta ma manta da abin da Khadija ta fad'a mata, sai kawai tace "Eh, me ya faru?" Da wani irin kallo yace "Kuma ba ta fad'a mi ki komai a game da hakan?" "A'a, wai me ya faru ne?" Ta fad'a cike da k'aguwa, a hankali yace "Shikenan kawai, zo zauna nan." Janyota ya yi ya zaunar da ita akan cinyar shi ya na kallon fuskarta yace "Haseenah, ki yi hak'uri kinji, ina ganin laifi na ne da har mu ka yi soyayya da kai ba tare da kinsan abubuwa da dama a kai na ba, kuma hakan ya samo asaline saboda ba mu jima tare ba, sannan ni mutum ne da bai cika fad'an abin da ya shafe shi ba, amma a gaskiya ni ba na cin tuwo da dare, ba kuma shi kad'ai ba, akwai abin da ma kwata-kwata ba na cinsu kamar wake da nasan sa, sannan kinga shinkafa ma ban cika son ta ba haka, sannan kifi ma ba na cin shi da dare, wannan shine." Bushewa ta yi da dariya ta sauka daga cinyar shi taja kujera mai fuskantar shi, da k'yar ta tsayar da dariyar tace "Miji na, ka na d'an africa, a africar ma a niger, kuma ka ce ba ka son shinkafa, lallai ka na jin dad'in ka." Ganin ta mayar da abun kamar wasa ya sa ya d'an gimtse fuska yace "Ni dai ban son ta, na fad'a mi ki ne dan ki kiyaye." Ita ma had'e fuska ta yi tace "To yanzu tuwon nan fa ya zanyi da shi?" Shima dariya ya yi yace "Ku ba kun ci ba? Kawai ki samar min wani abu na ci." Cike da kasala tace "Kamar me fa?" "Ko taliyarku ta yara ki d'ora min." Yanda ya yi maganar da zolaya ya sa ta taso ta na dariya ta rumgume shi ta baya ta na fad'in "Yanzu ni yarinya ce a wurin ka?" "Sosai ma." Ya fad'a ya na dariya, cikin kunne ta rad'a ma sa "Ni kam banyi tsammanin za ka iya kira na da yarinya ba." D'ago kai ya yi ya kalle ta yace "Shekarar ki nawa ne wai dan Allah?" Saida ta waina idon ta tace "Sha takwas." Da sauri ya mik'e tsaye ya na k'are mata kallo, har zagayata ya ke ya na kallonta, tab'e baki ya yi yace "Lallai ina da sa'a, gani tsoho amma sai Allah ya dinga had'a ni da yara yan sha takwas shakaf." Juyawa ta yi ta nufi madafar, d'ora tukunya ta yi duk da ba wani sanin kan indomie ta yi ba, amma dai wani lokaci ta d'an dafawa yayan ta *Mubarak*, yanzun ma yanda take yi a gida haka ta dafa, sai dai da ta zuba a faranti sai ta ga abun bai birge ta ba, dan indomien duk ta dahu sosai kamar za ta narke, to amma ya ta iya haka ta d'auko ta kawo mi shi, dakewa kawai ya yi tamaza ya d'ura indomien nan, amma bai ci sosai ba, ya na gamawa ya mik'e yace "Zan lek'a na ga su Bilal." Kallon shi ta hi ta kalli farantin indomien, k'ala ba tace masa ba ta tashi ita ma ta wuce d'akin ta dan shirin bacci, shi ma ficewa ya yi bai kula ta ba, d'akin Bilal ya fara shiga, sai da ya k'arewa yaron kallo ya shafi kansa kafin ya fito, da sallama ya shiga d'akin amma shiru, kujerar gaban madubi ya janyo ya zauna bayan ta ya daddab'a ta, bud'a ido ta yi ta tashi zaune ta janyo gilashin ta ta sanya, kallon shi ta yi shi kuma yace "Hajia Khadija ki na lokaci, yanzu har an daina sona ta yanda ba'a jira aga na shigo lafiya ko akasin haka." Murmushi ta yi tace "Abban Bilal ma ya na lokaci, tun da har zai shigo gidan nan amma ya kasa neman mu." Da mamaki ya bita da kallo ita kuma tace "K'warai, na ji shigowarka ai." "Hum." Ya fad'a ya yi shiru, ita kuma tace "Ka daina mantawa, yanzu mu biyu ne da hakk'in kula da kai, in da lokacin kwana na ne zan iya jiran ka har gari ya waye." "Amma in ba kwananki bane kuma ko oho ko?" "Kai ma kasan dole zan damu da kai, sai dai ba na son shiga hurumin da ba nawa bane." Mik'ewa ya yi ya nufi frije d'in ta ya bud'a, wani k'aton cake ya d'auko mai suffar zuciya tare da yagourt mai kauri da sanyi, komawa ya yi ya zauna ya fara ci ya na shan madarar, Khadija dai kallon shi take har ya sai da ya cinye duka kafin ya mik'e, ban d'akin ta ya shiga ya wanko bakin shi ya dawo, kallon ta ya yi yace "Umman Bilal ya yarinyar can ta fad'a min kinga lokacin da take tuwo ko?" Gyara zama ta yi akan gadon tace "Eh, na gani." "To amma me ya sa ba ki fad'a mata ba na cin tuwo ba? Tunda ke kin sani." Da mamaki ta

Table of Contents

Chapters

117 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117