Chapter 103
Chapter 103
sai na jika, sai anjima." Cike da zolaya yace "Au! dama muryar d'an ki kawai ki ka kira kiji? To ya yi kyau." Dariya ta yi tace "To meye a muryar ta ka da za ta dame ni? Bayan anjima kad'an za mu kasance tare da kai." Da haka sukayi sallama bai nuna mata komai ba, sai lokacin ne malam yace ya kamata su san halin da ake ciki, fita ya yi da niyyar zaije ya samu Ashir ya fad'a masa, hakan kuwa akayi dan ba jimawa ya isa in da Ashir ke harkokinshi, bayan sun gaisa ne ya fad'a masa abin da ke faruwa, ya jinjina al'amarin tare da tashin hankali, amma sai Usman yace "Idan dai har kai za ka d'aga hankalin ka to ya mahaifiyar shi kenan? Na zab'i na fad'a ma ka saboda ka san ta hanyr d za ka kwantar mata da hankali." Shiru Ashir yayi kafin daga bisani yace "Hakane Usee, insha Allahu zan fad'a mata yanda za ta fahimta, kar ka damu." Hannu ya bashi su ka yi sallama yace zai wuce gida ne, shi ma Ashir d'in gidan ya nufa daga nan dan fad'a musu, Mama ya fara fad'a ma tasan halin da ake ciki, ita kanta Mama da k'yar ta iya fad'awa Khadija, cikin tashin hankali tace Ashir ya kaita asibitin taga d'an ta, a hanya ma kuka take ta na fad'in kawai laifinta ne da ta yarda ta bashi yaron, Mama ce ta dinga tausarta da kalamai masu kwantar da hankali da k'arfafa gwiwa, suna isa asibitin aka nuna musu d'akin, da sallama su ka shiga amma Khadija na ganin Bilal kamar ba shi ba sai ta yi shiru, da k'yar ta isa ga gadon ta zauna ta na shafa fuskar shi, hawayen da suka taho mata ne ya sa malam cewa "A'a Khadija dan Allah, kar ki masa kuka mana, k'addara ce da kuma tsautsayi, ki masa addu'a Allah ya tashi kafad'un shi." Hassana ce ta yi tsaye kanta tana shafa bayan ta tana bata hak'uri ita ma, sun jima a haka kafin ta kalli Nura tace "Har yanzu bai farka ba?" Cikin sanyin jiki yace "Bai farka ba har yanzu, amma dai likitan yace an masa allura ne." Cikin zubo da wasu hawayen tace "Ko dai ya mutu ne? Dan Allah ku fad'a min idan ya mutu, wallahi zan d'auki dangana." Hajia ce tace "Haba Khadija, idan ya mutu za mu saka shi gaba ne haka, da ran shi mana gashi ma ya na numfashi." Haka suka zauna jugum sai wasu dake tafiya wasu na zuwa, sai yamma kad'ai Bilal ya farka idon shi har sun kumbura, bud'ar bakin shi da "Mummy, Mummy." Ya fara, dama ta na kusa kam ta rik'o hannun shi tace "Gani nan Bilal, bud'a idon ka." Bud'a ido ya yi ya kalle ta sosai, hawaye ne suka taho mi shi yace "Mummy ina Abba na?" Saida ta mayar da na ta hawayen tace "Ya tafi gida yanzu zai dawo." Da k'yar yace "Mummy, ciwo na, ki bani ruwa na sha." Ruwa ta d'auka ta bashi, komawa ya yi ya kwanta yanda ya ke har bacci ya sake d'aukar shi. *B'angaren* Usman kuma tun a hanya yake tunani dama Haseenah ta shirya raba shi da yaron shi, in ba haka ba me ya sa ta hana shi ya fita da shi? Kawai makirci ne ta shirya mi shi dan ta raba shi da Bilal d'in shi, tunda ai tasan baya bari Bilal ya fita da moton shi, ko a k'afa bai cika son ana aikan shi ba wajen ti-ti, da wannan tunanin ya k'araso gida dan d'aukar mataki akan amarsu. _Ita dama rayuwa haka take tafiya, ka shuka alkairi saika girbi alkairi, a baya mutane suna ganin laifin Khadija saboda makircin Haseenah, wanda ita Khadija a kan gaskiyarta take, yau kuma gashi Haseenah ita ma bata da niyyar cutar da Bilal, amma sakkayar Allah dama haka take, gashi ita ma yanzu za'a hukunta ta akan laifin da bata san hawa ba bata san sauka ba, Allah ka mana agaji da kan ka._ Haseenah da ke madafa a lokacin da waya a kunne ta kira Mariya ta na tambayar ko za ta zo? Cewar Mariya "Haseenah ba zan samu damar zuwa ba wallahi, saboda kwana biyun nan munyi hidimar biki, ko na tambayi Abban Fadila ma ba zai bar ni ba, amma ke ki zo ki kawo kud'in, idan na samu dama sai naje wajen malam d'in." Cikin damuwa tace "Haba aunty Mariya, na fad'a mi ki fa halin da nake ciki, wallahi Usman ko magana ba ya son yi min, ina ga fa Khadija wani asiri ta masa ya juya min baya, kuma yace za ta dawo gidan, jiya ma kar ko so kiji maganar da ya fad'a min akan Bilal, to ina ga ta dawo gidan? Ai sai dai ya sake ni." Mariya ce tace "To ya za ayi? Ni dai yanzu na fad'a mi ki uziri na ai, kinga kuwa dan na gyara aurenki ai bana b'algace nawa ba." Ajiyar zuciya ta sauke tace "To shikenan, bara ya shigo saina tambaye shi naji idan zai bar ni, ko zuwa gobe sai naje na kai mi ki kud'in, amma fa aunty Mariya wannan karan so na ke gaba d'aya a zautar da shi ya zama ba komai a gabansa sai ni, sannan ba shi kad'ai ba har iyayen shi da yan uwan shi ina so a rufe bakin su, su zama babu ruwansu da harkar shi bare har wani ya yi tunanin taimaka masa da ko da addu'a ce." Da matuk'ar mamaki Mariya tace "Ke Haseenah, a ina ki ka koyi mugunta haka? Yaushe zuciyar ki ta zama marar imani haka? To kinga gaskiya no ba zan iya wannan aikin ba, dan in na biye mi ki mu ka yi haka to kashin mu zai bushe wallahi." Cikin rashin nuna damuwa tace "Me ki ke nufi? Kamar ya banda imani?" Muryar Usman ce ta bata amsa da "To ki na da shine imanin?" Bata san lokacin da ta saki wayar ba ta juyo da k'arfi, hannu tasa ta rufe bakinta matuk'ar tsoro a fuskarta, tabb', lallai yanda ta ga alamunshi ta san yau babu tsumi ba dabara, amma duk da haka bara ta jaraba lallab'a shi ko Allah zaisa a dace, a cewar ta fa, durk'ushewa ta yi ta had'e hannayenta ta kalle shi tana hawaye tace "Dan Allah dan girman Allah Abban Bilal ka yi hak'uri, wallahi tallahi sharrin shaid'an ne da zugar aunty Mariya, ka yi hak'uri ka yafe min dan Allah ko dan cikin nan dake jiki na, wallahi na ma ka alk'awarin haka ba za ta sake faruwa ba." Takowa ya yi har kusanta ya sa hannu ya kashe wutar gas d'in, tsayawa ya yi ya na k'are mata kallo, wai yarinyar da ya aura saboda nutsuwarta da hankalinta, ita ce ta yi sanadiyar faruwar abubuwa marasa dad'i irin haka a rayuwar shi, ita kam kallon da yake mata ne ya sa ta sake cewa "Dan Allah babban mutum ka yi hak'uri, wallahi ba laifi na bane, wall..." Marin da ya zuba mata ne ya sa ta kwamtsa wata k'ara ta fad'i kwance, duk'awa ya yi ya d'ago ta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117