Skip to content

Chapter 10

Chapter 10

Kallon Kitse Book One Complete Hausa Novels 1,199 words 0 views Progress saved
Download Book

nufi masallaci, Khadija na gama sallah da azkar d'in ta kwace ta koma ta yi dan bacci ta ke ji wanda ba ta yi ba, sai da gari ya waye Bilal su ka dawo tare da baban shi, d'akin amarya ya fara wucewa tun da ba ta san tsarin gidan na su ba, kwance ya same ta a kan sallaya ta na bacci, a hankali ya juya ya fita ya koma d'akin *Dije*, ita ma kwancen ya same ta ta na bacci, k'arfin hali ya yi ya tashe ta, ta na bud'a ido ta ya sakar mata murmushi yace "Ammien Bilal, ashe bacci ki ke? Na d'auka ki na madafa ai." Sai da ta d'auki gilashin ta kafin tace "Yin me a madafa?" Cikin murmushi yace "Yin girki mana, ko ba za ki mana abin karin kummalo ba? Kinsan fa bak'uwa ce da mu a gidan, watak'ila ita ta na karyawa da wuri ba kamar mu ba." Gyara zama ta yi tace "Sai kuma aka ce wannan ya zama matsala ta? Me ka ke so na yi? Na je na dafa mata abinci kenan ta ci? To ka yi hak'uri, ban da ra'ayin shiga madafa yau." Ta na fad'a ta tashi ta shiga ban d'aki, wanka ta yi dan baccin ma ya fita idon ta, Usman kam na fita ya wuce d'akin Haseenah ya d'auko makullin mota dan ya siyo abinci, a farfajiyar gida ya samu mai gadi ya bud'ewa k'anin shi k'ofa ya shigo, musabaha su ka yi kafin k'anin yace "Ango abinci fa Hajia ta ce na kawo mu ku." "Da gaske *Nura*? Kai amma Hajia ta kyauta wallahi, dan dama duka mutanen gidan a gajiye su ke." Dariya Nura ya yi yace "Lallai kam, to ko dai za ka d'auke ni ina dafa mu ku abinci har lokacin da za ku huta?" Hannu ya sa ya karb'i kwanukan ya na fad'in "Dallah ni bani nan ba na son shiririta." Mik'a mi shi ya yi yace "Dama ba na son shiga ciki saboda ban sanyo manyan kaya ba, kasan halin Dijen nan da son girma." Kai ya girgiza yace "Allah ya shirya da wannan son girman na ka, wai matar da ta zo gidan nan ka nada shekara biyar a duniya, tun fa ka na yawo ba wando ta ke tare da kai, amma yanzu har ka ke son bud'e mata ido." "Ni fa matsala ta da kai kenan, yanzu dai sai anjima, sai na zo cin tuwon amarya." Wucewa kawai ya yi ya shige ciki, ya na shiga a teburin cin abinci ya aje ya d'auko farantai ya jera sannan ya shiga ya taso Haseenah, tare su ka fito ta na sake k'arewa falon na shi kallo, ganin za su wuce teburin abincin ya sa ta tsaya ta na kallon shi, juyowa ya yi shi ma yace "Muje mana." Binshi ta yi su ka wuce, k'ofar falon Khadija ya bud'a ta shiga, saboda yawan turaren da akewa d'akin ya sa har ya kama d'akin sosai, a hankali Haseenah ta lumshe ido ta bud'e kai tsaye, rarraba ido ta fara ta na kallon ikon Allah, wai, masha Allah, tabbas ba k'arya falon ya had'u kuma ya tsaru sannan ya ga kaya, ba had'i kam nata falon da wannan falon, ta na ganin kyawun falon Usman, amma sai ta ga ashe na shi ma somin tab'i ne, takawa ta fara yi ta ji k'afafun ta ta lumewa cikin shinfid'add'en tappi da ke kai, ta na kallo ya k'wank'wasa k'ofar d'akin tun da ba shi kad'ai bane, amma a wajen Haseenah kawai mulkin da Khadija ke yi a gidan ne ya sa ba ya iya shiga d'akin sai ya nemi izinin ta, jin shiru ya sa ya bud'a a hankali ya lek'a, ganin ta ya yi zaune bakin madubi ta na shafa hoda (powder), "Mu shigo?" Shine abin da ya fad'a, ta na jin haka ta san ba shi kad'ai bane, dan haka ma ta saki murmushi tace "Ku shigo mana." K'arasa shiga su ka yi Haseenah na d'ard'ar da satar kallon d'akin, ko dan na ta d'akin sabbin kaya ne a ciki sai warin sabintaka su ke, hakan ya sa taji kamar ta yi kwance a d'akin Khadija, zaune ta yi kujerar da ke gefen kwabar saka kaya (wadrob) kanta k'asa, shi kuma tsaye ya yi gaban Khadija yace "Wannan kwalliya haka matar, wa ake ma ne?" Tsaye ta mik'e ta na gyara d'an kwalin ta ta juyo ta kalli Haseenah da fara'a tace "Amarya ke da kan ki?" Ita ma murmushin ta yi tace "Ina kwana?" "Lafiya lau amarya, kin tashi lafiya?" "Lafiya lau." Ta fad'a a tak'aice, da murmushi Khadija ta d'ora da "Ya kwanan bak'unta kuma? In ce dai kinyi bacci?" A birkice Haseenah ta kalli maganar Khadija, hakanne ya sa ta d'an d'ago ta kalle ta ido tsaye tace "Ai Abban Bilal bai barni na yi bacci ba, kin san shi da rigima." Kallon ta Khadija ta yi ta na wani murmushi irin na babba da yaro tace "Ke ma kenan da ki ka zo jiya, yanzu na san za ki fahimci k'ok'ari na akan mijin ki." Haseenah kam a zuciyar ta tsaki ta yi, Usman ne yace "To na ji, yanzu dai ai nine rigimammen ko? To nagode, yanzu ku wuce muje mu ci abinci." Cikin zolaya Khadija tace "Wai har ka gama girkin? Amma gaskiya ka yi sauri." Hararan wasa ya aika mata yace "Kin d'auka ke kad'ai ce gwana a fannin girki? To ni har lambar yabo aka ban, nuna miki ne ban yi ba saboda tsaro." Dariya ta yi tace "Ko dai saboda tsoron girki ba." Takawa ta fara yi tace "Muje to." Da sauri ya rik'o hannun ta ya mayar da ita gaban madubi ya bud'a ya d'auko wani k'aramin akwatin gilashi yace "Ki saka wannan ya na miki kyau." Da kan shi ya saka mata kafin suka wuce, Haseenah kuma kamar zuciyar ta za ta harba saboda bak'in kishi na banza da wofi, haka su ka zauna tare da Bilal a faranti d'aya su ka saka hannu dukan su, sai dai Khadija da Haseenah ba sosai su ke cin abincin ba, dan kowa da abin da ke ran shi, haka dai su ka gama ango ya shirya ya fita, amarya ta koma b'angaren ta. *Yau* ma dai sosai aka gwangwaje walimar damu, mutane sun sha anko gwanin ban sha'awa, haka aka yi abin da ya tara mutane sai dai sisin kwabo ko k'wayar gero Usman bai karb'a ba a hannun iyayen Haseenah, daga k'arshe dai tsofaffi da iyaye sun sake had'a kan Khadija da Haseenah sun mu su nasiha da jan kunne tare da gargad'i, a k'arshe kuma su ka bisu da addu'ar fatan zaman lafiya da kuma zuri'a mai albarka, haka yau ma taro ya watse in da kowa ya koma gefe dan a kalli kalar na su zaman, da dare ma Usman ya shigo tare da manyan aminan shi Alhaji *Murtala* da Alhaji *Adamu* mijin Salamatu, suma dai nasihar su ka sake mu su tare da fatan alkairi daga bisani su ka tafi. *Allah ya bada hak'urin zama da juna.* 05/01/2020 à 22:11 - 💋😘💋: 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑 *KALLON KITSE* _(Ake wa rogo)_ 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑 _SAMIRA HAROUNA_ *Littatafan marubuciyar* *1*

Table of Contents

Chapters

117 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117