Chapter 29
Chapter 29
k'asa da murmushin jin dad'i a ran ta kuma ta furta "Ashe ma makauniya ce, gilashi shine idon ta, hum." D'agowa ta yi tace "Allah sarki, Allah bata lafiya." "Ameen." Ya fad'a ya na cire hannun shi ya wanke cikin wata k'aramar roba mai d'auke da ruwa, mik'ewa ya yi ya kalle ta yace "Zan d'an shiga d'akina na kwanta, misalin *11:00* sai ki tashe ni." Mik'ewa ta yi cikin kwarkwasa tace "Ni kad'ai kenan zan zauna? Gaskiya a'a sai dai na bika mu je tare." Kallon ta ya yi ya na sauke ajiyar zuciya yace "Haseenah kenan, kedai kawai ki na so ki hana ni bacci ne, amma idan ba haka ba me zai hana ki je wajen yayar ki." Cikin sanyin jiki tace "A'a gaskiya, gwara na zauna d'aki na ni kad'ai." Da mamaki sosai ya kalle ta yace "Me ki ke nufi? Haseenah akwai wani abu da ake mi ki a gidan nan da ba kya jin dad'i ne?" Wani murmushi ta yi da bai kai zuci ba tace "Ba komai fa, kawai ka je ka kwanta abin ka." Rumgumo ta ya yi jikin shi su ka nufi d'akin na shi ya na fad'in "Ai sai kin taimaka min kafin na yi baccin ko?" Su na shiga d'akin ya cire doguwar rigar shi ya kwanta, hijabin ta ta cire k'ananan kayan ta su ka bayyana, bayan shi ta kwanta ita ma ta na shafa kan shi har zuwa kunne, ba tare da magana sai kuwa bacci ya d'auke shi, a hankali ita ma sai bacci ya yi awon gaba da ita, daga nan fa su ka shiga baccin su hankali kwance. Khadija kuma na falo ita da Uwani su na ta hira su na kallo, har ita ma Khadija ta kwanta a kan kujera bacci ya soma d'aukar ta, *12:15* Uwani ta daddab'a k'afar Khadija ta farka, agogo ta kalla tace "Aunty, na ga sha biyu har ta wuce amma Bilal bai dawo ba." Da sauri ta zabura ta mik'e zaune ta na fad'in "Abban shi ya fita ne?" "Gaskiya ban ga fitar shi ba, dan har yanzu motar shi na waje." Wayar ta ta d'auka ta kira shi amma ta na silent, dan haka ba ta sake na biyu ba kawai ta kira lambar Naseer, ya na d'auka ya fara da "Autar Hajia ya ake ciki ne?" Cikin shagwab'a tace "Yaya na, Bilal ya na makaranta har yanzu ba'a d'auko shi ba, kuma na kira wayar Abban shi ba ya d'agawa, shine na ce ko za ka saka cikin yaran shagonka su d'auko min shi?" Daga in da ya ke ya mik'e yace "Abu mai sauk'i, dama zaune na ke ina kallon titi, bara na isa da kai na na d'auko shi." "Yawwa yah Naseer nagode." "Uhum! Kar ki damu." Aje wayar ta yi ta na mamakin abin da ya sa Usman mantawa da gudan jinin shi a makaranta, sharewa kawai ta yi ta kalli Uwani tace "Uwani, ki duba madafa ki ga idan babu kowa sai ki d'orawa Bilal indomie kafin ya dawo, dan kinsan abinci ya ke fara nema da ya sauko." "To aunty." Ta fad'a ta na tashi ta nufi madafar, ba kowa a ciki dan haka ta fara abin da ya kai ta, sallama ta ji tun daga tsakar gidan, lek'owa ta yi dan madafar a bakin k'ofar shiga duka b'angarorin take, su Rabi'a ne da kuma matar Kabir *Jauza'u*, amsawa ta yi ta na fad'in "Aunty Rabi'a sannun ku da zuwa." "Yawwa Uwani sannu, aiki ake?" Cewar Rabi'a, k'ofar Haseenah su ka nufa Rabi'a ta sa hannu ta bud'e sai ta jita a rufe gam, kallon Uwani ta yi tace "Amaryar ba ta nan ne?" "Ta na nan, amma ina jin kamar ta na d'akin Abban Bilal." Ta fad'a da nuna mu su falon na shi, Jauza'u ce tace "Shikenan bara mu shiga wajen aunty Khadija to." Da sallama su ka shigo a bakin su, Khadija da ke zaune ta na danna waya ne ta d'ago ta kalle su, sharrin shaid'an da zafin kishi ya sa Khadija tuna irin k'iyayyar da yanzun su ke mata, a ganin ta suna matuk'ar farin ciki da k'ara auren Usman, su na jin dad'i saboda an mata kishiya, sai kawai ta ji ba ta buk'atar sakar mu su fuska kamar baya, fuska ba fara'a ta amsa da "Wa'alaikum salam." Suma k'asa su ka zauna Jauza'u na fad'in "Aunty Khadija ke kad'ai zaune?" Kallon ta ta yi tace "Umm." "Ina kwana aunty Khadija?" Cewar Jauza'u, ta na ci gaba da danna wayar ta tace "Lafiya k'alau, ya ki ke?" Duk da Jauza'u ba haka ta saba gani ba ammata dake tace "Lafiya lau, ina Bilal?" Ba tare da ta d'ago ba tace "Bilal ya na zuwa yanzu daga makaranta." Sai lokacin Rabi'a tace "Ina kwana?" D'agowa ta yi ta jefe ta da wani banzan kallo kafin ta yi k'asa da kan ta tace "Lafiya, ya gida?" Sai da ta harare ta ta wutsiyar ido kafin tace "Lafiya lau." Shiru ne ya d'an ratsa wajen kowa da abin da ke sak'awa a ran shi, Jauza'u kam duk ta ji ba dad'i dan har ga Allah ta na k'aunar Khadija, saboda ta mata abin da ko mijin ta bai iya yi mata ba a lokacin da baya da k'arfi, su na haka babu mai magana shiru kamar ba gidan wannan Khadija ka zo ba wacce ke washe baki idan ta yi bak'o har ya tafi ta na rawar jiki, amma yau gashi sai wani shan k'amshi take. Usman ne ya zabura ya tashi ya na rarraba ido, da sauri ya kalli agogon da ke fuskantar shi, " *12:45*." Shine abin da ya fad'a da k'arfi har ya sa Haseenah tashi zaune ita ma, da hanzari ya sauka daga kan gadon ya na d'aukar doguwar rigar shi ya zura, makulin mota ya wawura a gefen gadon ya juya zai fita Haseenah tace "Wai saurin me ka ke ne haka?" Ba tare da ya juyo ba yace "Yarima zan d'auko, lokacin tashin su ya wuce sosai." Da sauri ta duro daga kan gadon ta tari gaban shi tace "Amma haka za ka fita ko wanka ba ka yi ba?" Ture ta ya yi daga gaban shi yace "Wani wanka dallah, yaro na can tsaye ya na jira na, ban san a wane hali ya ke ba." Fita ya yi daga d'akin ta bishi da kallo, k'wafa ta yi ta fita daga d'akin ita ma kai tsaye madafa ta nufa da tunanin d'ora silalar nama sai ta yi wanka, ta na bud'a k'ofar ya yi daidai da Uwani ma za ta fito, hakan ya sa Uwani bige ta ba ta sani ba, rik'e hannun ta tayi da ta bugu ta na ma Uwani kallon tsana, cikin jin zafi da b'acin rai ta kife Uwani da marin da ya sa farantin indomien zubewa k'asa saboda yanda ya zo a bazata , dafe kunci ta yi ita kuma ta na fad'in "Dan uban ki ni za ki bige? Wacece ke a gidan nan? Me ma ya kawo ki madafar nan? Ko kin manta yanzu ni ke aiki a ciki ko wacce ta aje ki sai na yarda za ta shigo? To ki saurare
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117