Chapter 7
Chapter 7
ππππππππππ _SAMIRA HAROUNA_ *Littatafan marubuciyar* *1* _KAUSSAR_ *2* _D'AUKAR FANSA_ *3* _BA SO BANE_ *4* _AUREN HAD'I_ *5* _SANIN MASOYI_ *6* _JIHADI_ *7* _K'ANGIN RAYUWA_ *8* _ITACE K'ADDARARMU_ *9* _KAWU NA NE_ *10* _MAATA_ *11* _KALLON KITSE..._ *SADAUKARWA GA* _MATAN FARKO_π§πΌ *(UWAYEN GIDA)* πΈπ¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S* _(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_π€π€ ```Fatan alkairi masoya``` _Bismillahir rahamanir rahim_ *5* Hira su ke ta kwasa shi da k'awayen ta, Haseenah kam dariya ce ta ta, a haka dai su ka isa k'ofar gidan su Haseenah da ke unguwar *ArΓ¨ne da lute*, a tare su ka fita daga motar su ka rufe a tare, sauke gilashi ya yi ya kalli k'awayen yace "To Hajia *Zeinab* saura kud'in taxi ko." Dariya k'awar ta yi ta juya ido tace "Ina fatan ka na da canji dai?" "Akwai canji mana, mai sana'a da mata ai baya rasa yan matsabbai." Dariya su ka sake yi kafin ta kalli Haseenah tace "To ki biya shi, daga baya ni sai na biya ki." Da sauri Usman yace "La la la, ke dai kawai ki ce ba ki niyyar biya na ba, dan haka na yafe kawai." Kallon shi ta yi tace "Oho, ashe kud'i na ne za ka iya amsa." Dariya ya yi yace "Shikenan dai magana ta wuce tunda na yafe, yanzu sai da safen ku." "Sai da safe." Su ka fad'a su na nufa na su gidanjen da ke unguwar, kallon Haseenah ya yi yace "Ki shiga gida, ba na so k'urar nan na tab'a min ke fa, sai munyi waya." Cike da rausaya tace "Angama ranka shi dad'e, sai munyi waya. " Gida ta shige ita ma kafin ya wuce na shi gidan shi ma, ya na zuwa ya sa mai gadi ya rufe gidan gaba d'aya dan ya shiga kenan, tun a k'ofar falo Khadija ta tarbe shi su ka yi cikin d'aki, (to ni wanka ma tare su ka yi shi ko kuwa ita ce ta mi shi oho), amma dai a tare su ka fito kuma suka shirya, kai tsaye wajen cika ciki su ka nufa, tun da ta bud'a kwanon ta d'auki k'aramin faranti ya zura kai cikin kwanon ya na fad'in "Me aka dafa mana yau *Nana*?" Ba tare da ta kalle shi ba tace "Kan kare." Yamutsa fuska ya yi yace "Kuma ki na ganin zaiyi dad'i?" Ita ma yamutsa fuska ta yi tace "Um; ba tabbas, amma ka fara d'and'ana mana tukuna." Nuna kan shi ya yi da yatsa yace "Ni? To na k'i, ki bawa d'an ki ya fara lasawa." Murmushi ta yi tace "Ka na so ne na rasa d'ana?" "Oho, ni ne kenan banda mahimmanci? To nima haihuwa ta aka yi, kuma yanzu haka da iyaye na za su ji me ki ka fad'a, to da kinga yak'in duniya na uku ganin idon ki." Tunda ya fara magana take dariya har ta gama zuba mishi ta aje farantin gaban shi, janyo kujera ta yi ta zauna daf da shi yayin da Bilal ya zauna a k'afafun Usman, dukansu hannayen su suka saka suna cin abincin, dan a d'abi'ar Usman yace Allah ya hore mu su yatsu har biyar saboda su yi anfani da su ne har wurin cin abinci ba, da hakane su ka saba da ci da hannu in ba abin da ya zama dole aci da cokali ba, su na cinyewa Khadija ta turo baki gaba tace "Duk kun fini k'atuwar loma, kuji fa kun cinye abincin kai da yaron ka." Kallon Bilal ya yi yace "Yarima ka ji me ta ke fad'a, ka duba ka gani wa yafi k'aton ciki a duk cikin taron nan." Tsaye Khadija ta mik'e tace "Kai ka fi mu cin mai yawa, dan haka zan k'ara kuma banda kai za mu ci." "Tab'dijam, na kawo abincin, na sarrafa shi, na dafa shi, kuma ace ba zan ci na k'oshi ba, lallai ma yau za mu tara yan kallo a gidan nan." Ya k'arashe maganar da juya baki, hannu Khadija tasa ta d'auki kwanon miya ta na fad'in "Ai dai abinci ba zai ciyu gaya ba, ni kuma zan iya cinye naman ciki na kuma tsoma bredi a miyar." Shi ma jan kwanon shinkafar ya yi yace "Ni ma kuma zan iya zuba man gyad'a a shinkafa ta, haka zan iya saka sardine (kinfi gwangwani)." Bilal ne ya katse su da "Kai, Kai, wannan rigimar ta ku wata rana za ta ja min ciwon yunwa, kaga Abba kawo nan." Karb'ar kwanon ya yi ya aje ya nufi Khadija ya karb'i kwanon miyar ya aje sannan yace "Yanzu kowa ya d'aga min rigar shi na ga tunbin shi sai na ga wanda ya fi k'oshi." Dukan su a tare suka turo baki gaba da rumgume hannaye a k'irji, Usman kam har da k'arawa da mak'ale kafad'a yace "Um, um." Murmushi Bilal ya yi ya rumgume kwanukan ya na fad'in "Dan haka ni kad'ai zan ci abincin nan, kuma na ga mai ja a maganar yarima." "To shikenan, yanzu ga nawa." Cewar Khadija ta na d'aga rigar ta sama, hannu ya sa ya shafi cikin ta ya marairaice yace "Ayya! Sarauniyar uwa ta ba ta k'oshi ba har yanzu." Kai ta girgiza ma sa kamar za ta fashe da kuka, Usman ma haka ya d'aga ya shafa cikin, shima a marairaice yace "Sarki ma bai gama k'oshi ba, to ku zo mu ci tare." Matsowa su ka yi Usman ya kalle ta yace "Kinyi sa'a fa yarima ya ceceki, da gay kin sha miya." "Kai ma da ka ci gayan tuwo." Ta fad'a har da masa gwalo, cewa ya yi "Amma dai na san ba ki jin ana cewa azo asha miya, sai dai ace azo aci tuwo." Yatsa Bilal ya d'ora a labb'an shi yace "Ya isa haka to, aci abinci ba magana ba." Shirun kam su ka yi su ka saka hannu a abincin da ya zuba su ka ci gaba da ci, daga nan kuma kallo su ka tab'a kafin su ka kwanta da fatan wayewar gari lafiya. Tunda asuba Usman da Bilal su ka wuce masallacin da ke manne a jikin gidan, bayan sun dawo kuma kowa d'akin shi ya nufa, duk da Khadija ta ji dawowar su amma ba ta je in da Usman ya ke ba, saboda ta san abin da zaiyi yanzu ba ya son hayaniya da takura, sai da ta ga k'arfe *07:00* ta buga daidai ta tashi daga sallaya ta nufi d'akin, da sallama ta shiga ta same shi zaune a kan sallaya, d'ago kai ya yi tare da amsa sallamar ya na rufe Qur'anin hannu shi ya aje gefe, zaune ta yi k'asa kusan k'afar shi cikin ladabi tace "Antashi lafiya *babban mutum*?" Cikin kafeta da ido yace "Lafiya lau na tashi, fatan kema haka?" Da murmushi tace "Lafiya k'alau na ke tun da dai kun tashi lafiya." "Masha Allah, Allah abin godiya." Kallon shi ta yi cike da kunya tace "Zan shiga madafa ne dama, shi ya sa na ke so na ji abin da miji na ya ke sha'awar ci dan na sarrafa mi shi." Cike da kallon bege yace "Zab'in ku shine zab'i na, za ki iya dafa abin da ran ki ya ke buk'ata."
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117