Chapter 86
Chapter 86
tarbiyar Bilal, bai iya amsa sallamar sai cewa ya yi "Yariman hushi ka ke da Abban ka?" Jiki na rawa Bilal yace "A'a Abba ba hushi na ke da kai ba, dan Allah ka yi hak'uri ka yafe min, ba zan k'ara ba insha Allah." Murmushi ya yi yace "Ba komai yarima ya wuce, ya ka ke? Ya karatu?" "Lafiya lau Abba." Ya yi maganar ya na kallon Khadija da ta kafe shi da ido, ta na ji su na wayar su kafin daga bisani Usman yace "Yarima yaushe za ka zo mana gida? Kasan fa mu na kewar ka." Cikin turo baki yace "Gaskiya Abba ba zan je gida ba ba tare da Mummy ba, kawai kai ka zo nan." Ba tare da damuwa ba yace "Shikenan to, amma idan naje makaranta zan gan ka?" Cike da k'aguwa yaron yace "Abba! Me ya sa ba za ka zo gida ba?" "To to shikenan, na ji zan shigo gidan zuwa gobe." "Wane lokaci?" Saida ya d'anyi tunani kafin yace "Umm, ina ga zuwa dare zan shigo." "To Abba." A hankali Usman yace "Saida safe ko, ka yi bacci lafiya." "To Abba, ga Mumm..." Bai k'arasa fad'a ba ya ji ya datse kiran, kallon maman shi ya yi yace "Mummy ki yi hak'uri to, Abba ya hak'ura." Janyo shi ta yi ta rumgume hawaye na fita a idon ta tana fad'in "Bilal ba na so ne abin da ke tsakani na da mahaifin ka ya shafe ka, idan ba ka manta ba a baya haka bata faru ba tsakanin mu, yanzu ne haka ta fara faruwa saboda dama ita rayuwa ta gaji haka, ba lallai mutum ya tabbata cikin farin ciki ba, zan iya cewa a rayuwa ta ban tab'a fuskantar matsalar da ta sani bak'in ciki ba kamar wannan, dan haka zanyi hak'uri da jarabawar da Allah ya d'ora min har na cinye ta, ko da kuwa hakan na nufin k'arshen zama na kenan a gidan mahaifin ka." Da sauri ya d'ago yace "A'a Mummy, gaskiya ba za ku rabu ba, ni dai wallahi idan ku ka rabu to ba za ki sake wani aure ba." Zaro ido Khadija ta yi ta na kallon shi da mamaki tace "Kai kuma a ina ka samu wannan tunanin?" Cikin shagwab'a yace "To ba *Beby* (d'iyar Ashir ta farko mai sunan maman su) ce tace mana Maman su za ta yi aure ba." Girgiza kai ta yi tace "Kenan idan ban koma gidan sa ba saina tabbata a cikin d'akin nan? Kai ba ka kishi na ne? Ko ba kaga shi mahaifin naka ya k'ara aure ba, me ya sa ba ka hana shi?" "To Mummy ai shi namiji, ni kuma ba na so ki sake min wani Abba, na fi so ku zauna ku biyu abunku yafi dad'i." Shiru ta yi tunda shekarun shi basu kai tace dole saita fahimtar da shi ba, sannan ita kan ta tana wa Usman kishin kan ta ta yanda take fatan ya zama mijinta har abada, da haka suka ci gaba da karatun su har dare ya yi su ka kwanta. *Washe gari* da safe gidan ya yi shiru sosai aka amshi bak'uncin Murtala, dan gaskiya abun bai masa dad'i ba sosai, a falon Hajia suka zauna tare da Khadija da Hajia ya na basu hak'uri da nuna mu su rashin jin dad'in sa, sannan ya d'ora mu su da sam bai sani ba sai jiya, cikin fara'a suka nuna mi shi babu komai haka Allah ya hukunta, kuma ai da sauk'i tunda ba saki bane Allah zai iya daidaita lamarin, haka dai ya tafi abun ba dad'i sai hak'uri kawai. Yau Usman ya samu malam a gida bai fita ba saboda jiki da jini, saida ya sha ruwan shi kafin ya mik'e zai bar gidan Hajia ta tambaye shi ko yaje ganin Khadija? A cewar shi dai "A'a ban je ba, amma na ce yau zanje anjima." "To aiko gwara ka tafi dan kasan halin da take ciki." Da mamaki ya kalli Hajia yace "Hajia wani abun ne ke faruwa da ita?" Cikin murmushi tace "Ai Khadija Allah ya..." Da sauri malam ya d'aga mata hannu alamar ta yi shiru, girgiza mata kai ya yi kawai bai ce komai ba, jin ba tace komai ba ya sake mu su sallama ya fita, Hajia kuma malam ta kalla tace "Me ya sa ba ka so ya sani? Ya na da hakk'in sani fa." "Ki barshi kawai, idan ya je saita fad'a ma sa idan ta so ya sani, idan kuma ba ta so ba saiya gano da kan sa." Har ya mik'e zai fita Hajia tace "To amma ni banga anfanin b'oyewar ba." Juyowa ya yi ya kalle ta yace "Ni kuma na gani, in dai ina fad'a aji to ban yarda ki fad'a ma sa da bakin ki ba, dan halin da Fodio yake ciki yanzu ba ya iya rik'e sirrin kan shi ma bare na wani, a gaskiya ni ban yarda da amaryar nan tasa ba." Da *yamma* Khadija su na farfajiyar gida yara duk sun cika gidan da hayaniya suka ji sallama, amsawa akayi tare da masa izinin shigowa, Bilal na ganin shi da gudu yaje ya rumgumr shi, Khadija ma na juyowa ta mik'e ta na dariya saboda farin cikin ganin shi ta na fad'in "... *Addu'ar ku tamkar takobi ce a gare ni mafi kaifi a duniya, ina k'aunar ku masoya.* 25/02/2020 Γ 21:16 - πππ: ππππππππππ *KALLON KITSE* _(Ake wa rogo)_ ππππππππππ _SAMIRA HAROUNA_ *Litattafan marubuciyar* *1* _KAUSSAR_ *2* _D'AUKAR FANSA_ *3* _BA SO BANE_ *4* _AUREN HAD'I_ *5* _SANIN MASOYI_ *6* _JIHADI_ *7* _K'ANGIN RAYUWA_ *8* _ITACE K'ADDARARMU_ *9* _KAWU NA NE_ *10* _MAATA_ *11* _KALLON KITSE..._ *SADAUKARWA GA* _MATAN FARKO_ π§πΌ *(UWAYEN GIDA)* πΈπ¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S* _(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_π€π€ ```Fatan alkairi masoya``` _Bismillahir rahamanir rahim_ *32* "Ango kai ne a gidan namu, lallai babban bak'o, amma dai da alama hanya ce ta d'auka ka ya sa ka biyo nan, ba dan haka ba ni dai na san ka da tsoron bayar da kud'in cefanai." Dariya ake in da ta nufi falon Mama ta na fad'in "Bismillah Nura shigo." Bayan ta ya bi ya na rik'e da hannu Bilal, saida ya gaisa da mutanen da ke nan kafin ya k'arasa shiga ciki, zaune ya yi akan kujera ita ma ta zauna bayan ta aje ma sa ruwa da lemu, kallon ta ya yi yace "Ke haka ake sai ki tarfani a gaban manyan mutane, sai kisa su d'auka gaske ne abin da ki ka fad'a." "Au! Ba gaske bane kenan? To ka na bayarwa ne? Yanzu fad'a min yaushe rabon da ka zo gidan nan?" Sosa kai ya yi yace "Gaskiya na kwana biyu, yanzu kuma da na samu labarin ki na nan wallahi kunya ce ta hanani zuwa." Murmushi ta yi tace "Ba na son ku na fad'in haka wallahi, kenan idan k'addara tace za mu rabu da Usman ba da shi kad'ai zan rabu ba har da ku?" "Ah haba dai, ai ba za mu tab'a bari ki fita a cikin dangin mu ba wallahi, ke fa alkairi ce a cikin mu, shima yasan da haka, wannan mai k'afafun angulun ce ta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117