Skip to content

Chapter 112

Chapter 112

Kallon Kitse Book One Complete Hausa Novels 1,200 words 0 views Progress saved
Download Book

ce ki ka iyani yanda ya kamata, ke ki ka fi kowa sanin abin da na ke so da abin da na ke da buk'ata." Ba tace komai ba har suka isa gida rabe ya bud'e mu su k'ofa suka shiga, sun samu Bilal na baccin shi kamar yanda suka bar shi, nan suka kwanta suma bacci cike da gajiya, sam Khadija ba ta yi tsammanin gari zai waye ba ta haihu ba saboda abin da take ji, amma sai gashi ta tashi cikin k'arfin jiki, tunda asuba ta had'a kyakyawan abin karin kumallo sannan ta shirya, haka Bilal ma ya shirya Usman ma kafin suka karya na su kumallo abin da basu saba ba kari tunda safiya, asibiti suka tafi sun samu iyayen Haseenah da kuma Mariya, bayan sun gaisa suke mata godiya akan kayan ta da ta bayar Haseenah ta yi aiki da su, nan Usman ya zauna kuda da Haseenah ya kalle ta yace "Mai jego wai wane suna ki ka zab'awa 'yar ta ki ne?" Kunya ce ta kama Haseenah ta rufe fuska da hijabi, dariya ya yi yace "Ki fad'a mana, dan ni zan iya saka mi ki sunan tsofaffi kamar sunan su Hajia." Hajia ce tace "Sunan na mu ne na tsofi kenan? To aiko in ka yi wasa sunan Hajiar (mahaifiyar Haseenah) za'a saka mata." Dariya ya yi ya kalli Hajia a ran shi kuma yace "Asiya." Mahaifiyar Haseenahr ce tace "Ko kuma sunan ki ba, ai yafi nawa." Na kuma Haseenah ce ta kalli Hajia a ran ta ita ma tace "Allah ya sa kar ya sawa 'yata sunan mahaifiyar shi, *Hawa'u* ai sunan da ne." Jin dai su na ta cecekuce ya sa tace "Kawai tambayi mahaifiyar ta wane suna ta ke so?" Ta fad'a da nuna Khadija, kallon ta Khadija ta yi tace "Ni kuma?" "K'warai aunty Khadija, babu wanda ya dace ya saka mata suna bayan ke, a sanadiyar ki ta samu gatan da aka haifeta gidan mahaifin ta, dan haka kawai ki zab'a mata sunan da ya mi ki." Murmushi Khadija ta yi tace "To shikenan a saka mata Aisha, sai ku tayani addu'a Allah ya sa na haifi mace sai a saka mata Humaira, kunga sun zama 'yan biyu kenan, Aisha da Humaira." Kowa ya ji dad'in abin da ya faru, haka aka sawa yarinya Aisha tare da sa mata albarka, su kuma aka bisu da addu'a k'ara had'a kan su, nan Usman ya wuce da Bilal makaranta, zuwa k'arfe takwas ko da aka kama aiki aka sallame su, amma ba su bar asibitin ba har sai kusan k'arfe tara kafin Usman ya aiko Bilyamin ya d'auke su, tunda Bilal ya dawo ya ke b'angaren Haseenah ya na lagudar yarinyar, wani iko na ubangiji sai yarinyar ta yi kama da Bilal d'in kamar ciki d'aya suka fito, duk mutanen da ke zuwa wajen Bilal bai bar wajen ba, Khadija ta yi mamaki sosai yaron da ba ya son hayaniya da taron jama'a, amma sai gashi ya wuni zigidir wajen Haseenah har saida yamma lokacin islamiyya ya yi kad'ai ya bar wajen. Sosai yan uwan Khadija da abokan ta suka mata kara wajen zuwa yi wa Haseenah barka, sai dai Hajia Turai ta rantse ta maya kan ba za ta zo ba sai in Khadija ta haihu, to fa ranar za ta zo gidan ko me zai faru sai dai ya faru, a lokacin kuma Khadija ta nemi da Usman ya mata izini taje ta dawo da Uwani ko dan aikin da ke tunkaro su ta na buk'atar mai taimako, ba musu ya mata izini ta tafi tare da Bilal, ba ta sha wahalar shawo kan su ba saboda dama ba laifin ta bane, nan suka dawo tare da su aka d'ora daga in da aka tsaya. Sosai Khadija ke kama girmanta wajen ganin ta sauke nauyin da Usman ya d'ora mata, kowace safiya kafin Haseenah ta fito daga wanka za ta samu abin karyawarta yana jiran ta, da rana kuma idan su Mariya su ka zo tare suke aikin rana cikin raha da annashuwa, haka za su dinga cewa ta zauna ta huta za su yi amma sai tace a'a, haka suke girkin rana da na dare tare, kuma sosai suke k'aruwa wajen koyan girkin, dan kwana uku da akayi da haihuwar kullum akwai abin da ake girkawa, a haka aka shiga kwana na hud'u, a lokacin sosai Khadija take jin jikin ta fa ba dad'i amma ta na daurewa ne, yau dai ko da suka gama girkin rana ta shiga d'akin ta ba ta fito ba, saida Uwani taga abin ya fara tsananta ta fito ta nemi taimakon mutane dan su tafi asibiti, Hassana da su Rabi'a na gidan a lokacin su ka taho dan ganin lafiya, d'aki suka same ta kwance sai nishi take ta na ware k'afafun ta saboda tasan haihuwarta kusa take, nan suka duk'ufa aka taimaka mata, leda aka shinfid'a akan gadon suka fara karb'ar haihuwa, ai kuwa ba jimawa sai kan yarinya ya lek'o duniya, suna k'arasa jawo ta sai ta fashe da kukan da ya sa Usman da ya taho hankali tashe lokacin da Bilal ya kira shi ya tsaya cak, rufe fuska ya yi kafin ya bud'e ya na dariya mai kama da kuka, d'aukar Bilal ya yi ya na juyawa da shi cikin farin ciki. Nan su Hassana su ka fito da yarinyar suka bashi ya karb'a, ya na kallon ta ya ji wata muguwar k'aunar yarinyar saboda sak Khadija ya ke ganin fuskarta, yan uwa fad'an irin bidirin da ake ma b'ata lokaci ne, Khadija dai ga farin jinin mutane gashi haihuwar ta zama biyu, hakan ya sa kullum gidan kamar ranar ake biki, kuma an mayar da bikin rana d'aya ma'ana ranar da Khadija ta haihu, a k'alla mutanen da ke zuwa gidan basa irguwa kuma mafi aksari mutanen Khadija ne, shirye shirye ake sosai in da k'awayen Khadija su ka yi anko har kala biyar saboda farin ciki, kuma babu wanda Usman baiwa Khadija da Haseenah ba, dan ma Khadija ta yi wa kan ta dayawa da bai sani ba, a lokacin kuma Khadija ta tuna da ranar bikin ya yi daidai da zagayowar ranar haihuwar Usman, wanda shekarun su ka kama *arba'in da biyar*, dan haka ta fad'awa k'awayen ta su kaltume cewa ta na so ta mi shi bazata, nan aka fara wani sabon shirin dan bashi mamaki, in da ba kowa ya sani ba daga yan uwan Usman maza da mata, sai yan uwan Khadija da na Haseenah, sai kuma abokan Usman d'in wanda aka gayyata. *Rana bata k'arya* sai dai uwar d'iya ta ji kunya, yau akayi suna kuma yara sun ci sunan da uwarsu ta zab'a musu wato *Aisha* da *Humaira*, duk girman gidan Usman sai gashi ya kasa d'aukar mutanen da ke wajen har saida aka had'a da wasu runfa har biyu a k'ofar gida, duk wanda ya zo sai yace masha Allah saboda taron jama'ar, kuma kashi uku a cikin hud'u duk na Khadija ne, ita ma kuma hakan ya faru ne sakamakon jimawa da tayi ba ta haihu ba, Usman yayi iya k'ok'arin shi wajen samarwa mutanen abinci da abin sha, inda aka yanka manyan shanu har

Table of Contents

Chapters

117 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117