Chapter 109
Chapter 109
a d'akin ya na yi ya na kallon kayan da Khadija ta bado. *Daga ranar* komai ya k'ara canzawa Haseenah, kaf gidan yanzu babu mai kallon ta da mutumci, girki da wanke-wanke ko ga yara a gidan ita ce ke yi, wani lokacin ma mahaifin su har kayan shi ya ke bata ta wanke mi shi, duk a ganinsu horon da za su iya yi mata kenan da zaisa ta shiga hankalinta, wani abu dake damun Haseenah sosai shine rainin da duka k'annan ta suka aza mata, ko kallon su ta yi sai ka ga wata ta kwad'a mata harara, haka kullum take cikin fad'a ita da k'annan ta, ga ciki na ta girma sosai ga kuma rashin kud'i, idan ta tafi awo kad'ai take jin dad'i duk da rashin kud'i ya sa ta canza asibiti, yanzu haka ta na awo ne a asibitin da ke kusa da su asibitin *Ali Chaibu*, a haka ta yi laushi sosai take k'ara nadamar abin da ta yi, gashi Usman ko kiran ta bai tab'a yi ba bai kuma tab'a zuwa ba da sunan ya ganta, ya je sau biyu amma wajen mahaifin ta ya tambayi komai lafiya suka gaisa ya tafi, sai dai duk sati biyu yakan aiko Bilyamin ya kawo mu su kayan abinci da kud'i saboda bebyn shi, har yanzu babu abin da ya rage daga jikin ta na k'iba da ta yi, sai dai fatar ta ta canza sosai ba kamar da ta na gidan ta ba, dan kuwa duk kayan da zai aiko iyayen ta sukan zama na anfanin duka gidan ne, kud'i kuma sai in za ta tafi asibiti ake bata wanda basu taka kara sun karya ba. Duk lokacin nan da aka d'auka a wajen Khadija ita ma ta matsa lamba sosai kullum maganar Haseenah take wa Usman, ta yi rarrashin duniya ta yi kissar ta yi nisihar amma ya mayar da ita kamar mahaukaciya, akan maganar nan har fad'a su ka yi suka daina magana tsawon kwana uku, saida Bilal ya shirya su kad'ai suka koma magana, amma fa ba ta daina mi shi maganar ba, har tsawa ya mata ya zare mata ido yace idan ta na da zuciya ta daina mi shi maganar Haseenah amma tace ba ta da zuciya in dai akan maganar nan ne, haka kawai take jin zuciyar ta na yin sanyi kullum take son ganin ta dawo gidan ta, ta fad'a mi shi ya sake bata dama ta biyu mana tunda 'yar adam ce ita, amma abun baiyi tasiri ba, har Bilal ta sa ya rok'e shi take yace ya fita a harkar manya ba ruwan shi, izuwa yanzu kanta ya yi zafi akan maganar, hakan ya sa ta samu malam ta kalallame shi sosai, kuma ta yi sa'a ya gamsu da abin da ta fad'a sosai, alk'awari ya mata zan mi shi magana, kuma kamar yanda ya fad'a ya wa Usman magana, amma sai yace shi fa in aka sake matsa mi shi to zai bar mu su garin ita ma Khadijar ta koma gidan su, wannan magana ita tasa malam cewa "A'a Fodio, me ya yi zafi haka, Allah ya huci zuciyar ka, shikenan tunda ba ka so ai." Cikin b'acin rai yace "Baba Khadija hankali ne bai ishe ta ba, in ba haka ba yarinyar da ta cutar da ita da ni da ku ma amma wai ta dage kai da fata sai an dawo da ita, to tsiyar me za ta mana idan ta dawo?" Malam dai cewa ya yi "Yi hak'uri to shikenan, zam fad'a mata ta yi hak'uri kawai a bar maganar, Allah ya sa haka shi yafi zama alkairi." Malam da kan shi yaje har gidan ya fad'awa Khadija dan Allah ta manta da maganar Haseenah ta kula da mijin ta kawai, ba dan haka ta so ba ta nuna shikenan ya wuce, saida malam ya fad'a mata yace idan an sake takura shi fa zai bar gari ne, kai kawai ta gyad'a alamar taji, da dare ko da Usman ya shigo ya na zaune a falon ta tare da Bilal suna kallo Khadija ta fito da kinkimemiyar akwati da cikin ta masha Allah ya fito sosai, saida ta zo gaban shi ta tsaya tace "Malam ni zan tafi gidan mu tunda ka kasa min alfarma d'aya, idan na haihu nima ka zo ka d'auki abin da aka haifa." D'auke kan shi ya yi daga kallon ta ya na kallon telebijin kamar bai san ta na yi ba, juyawa ta yi da jakar Bilal ya zabura zai tashi Usman ya rik'e shi ya fad'a jikin shi, cikin kunne ya rad'a mi shi "Bari kaga yanda zanyi da ita, ko k'ofar gida ba za ta je ba." Har ta kai bakin k'ofa amma ba ta ji ana tsayar da ita ba, juyowa ta yi ta kalle shi ta tsaya cak, cikin d'aure fuska ya sa hannu aljihu yace "Kai na manta, zo karb'i kud'in adaidaita mana." Lalaba aljihu ya ke kafin yace "Hajia banda canji, karb'i makullin mota ta ki tafi da ita gobe zan je na d'auko." Ya k'arashe maganar da jefa mata makullin gabanta, haushi ne ya kamata sosai ta d'auki makullin ta juya ta fita, a hankali take tafiya da tunanin ko zai zo ya hanata amma shiru, k'wafa ta yi ta juyo da sauri cikin jin haushi ta dawo falon, zaune ta same shi yanda suke hankali kwance suke kallo, da sauri ta k'araso wajen shi ta d'auki akwatin dama ba komai ciki ta jefa mi shi a jiki tana fad'in "Hamago kawai, kenan dama so ka ke na tafi na bar ma ka gidan saboda ka gaji da ni ko? To babu in da zanje wallahi mutu ka raba ni da kai, sai na yi takabarka da yardar Allah." Tunda ta fara magana Usman ke dariya har da d'aga k'afafu ya na rik'e ciki, d'auke akwarin Bilal ya yi ya shiga d'akin ta da shi, Usman na ganin haka ya fizgota ta fad'a jikin shi ya rumgume ta yace "Ke a haukanki kin d'auka zan zauna hakane har ki bar gidan nan? Ai kafin ki isa gida zansa a sato min ke a dawo da ke." Cikin kukan shagwab'a ta kalke shi tace "Abban Bilal dan Allah kayi hak'uri ka dawo da ita, wallahi tausayi take bani sosai inna tuna rayuwar da take, wannan ita kad'ai ce alfarmar da na ke nema a gurin ka, ka taimaka ka dawo da ita gidan nan mana ta haihu gidan mijin ta, kullum ina aunata da kaina sai naga idan ni ce ya zanyi ace zan haihu gidan mu, babu dad'i ko kad'an wallahi, dan Allah babban mutum ka taimaka mata kaji, na maka alk'awarin za mu zauna lafiya da yardar Allah." Tun tana magana ya mayar da kallon shi ga telbijin, saida ta gama ya kalle ta yace "Khadija me ya sa ki ke son takura min akan magana d'aya? Me zaisa ba za ki bar maganar ba tunda har na ce ba na so? Me ta mi ki a rayuwa na alkairi da har ki ke son dawo da ita cikin rayuwar mu?" Cikin muryar tausayi tace "Wallahi babu komai, na dai fad'a ma ka dalili na kawai, Abban
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117