Chapter 32
Chapter 32
a wurin ta ko da a'a ne, idan na ce a'a haka ita ma za tace a'a, a iya zama na da ita ban tab'a ji ko a labarin ta ba cewa ta na da abokin fad'a ba, d'azu ma na tambayi me ya faru ne saboda shine adalcin da zan iya yi, amma a gaskiya ni nasan Khadija ba ta da tashin hankali ko kad'an, dan haka Haseenah ki kiyaye dan Allah, Khadija dai ita ce gaba da ke a shekaru da ma zuwa gidan nan, kuma nasan kinsan karin maganan da ake cewa *duk wanda ya rigaka bacci dole zai rigaka tashi*, ba na so ki sawa zuciyarki irin tunanin matan yanzu cewa, wai ko shekara d'ari ka samu mata a gidan mijin ta, to wata na shigowa gidan kuma tasan mijin sun zama d'aya, eh tabbas dukan ku matana ne kuma d'aya ku ke, amma ki sani Khadija ta riga kwana a gidan nan har da ma tashi, duk da Allah bai bamu 'ya'ya dayawa ba, amma dai ita ce uwar d'an da ni a yanzu na ke kallo kuma ina jin dad'i, sannan Haseenah duk da ki na ganin kamar kinsan komai a kai na har yanzu da saura, sani na a namiji ba shine sanin da ya kamata kuyi alfahari da shi ba, me na ke so?Me ye ba na so? Me ke sani farin ciki? Me ya ke b'ata min rai? Me yafi saka ni nishad'i da akasin haka? Wannan shine ya kamata ki zage damtse wajen sani, sai maganar makauniya da ki ka kira ta da shi, a gaskiya ba zan b'oye mi ki ba Haseenah rai na ya b'ace fiye da yanda ki ke tunani, me ya sa ba ki yi tunanin larura ce da Allah ya d'ora mata ba, wacce ke ma ba ki wuce ya jarabce ki da ita ba? To wannan ya zama na k'arshe da ko a mafarki za ki sake kiran da makauniya, kin fahimta?" Haseenah da zuciyar ta ke tafasa ta ke jin kamar ta fashe da ihu, saboda ganin duk ya tattara laifin ya d'ora mata, hakanne ya sa hawaye su ka zubo mata ta d'ago kai ta kalle shi tace "Ka yi hak'uri, insha Allah za'a kiyaye." Mik'ewa ya yi yace "Shikenan, sai ki bata hak'uri, da fatan hakan ba zai sake faruwa tsakanin ku ba." A hankali ta kalli Khadija tace "Ki yi hak'uri aunty Khadija, insha Allah ba zan k'ara ba." Hannun ta Khadija ta rik'o tace "Ba komai yer uwa, ki gafarce ni nima kinji, sharrin zuciya ne da b'acin rai, amma insha Allah hakan ba zai sake faruwa ba." Cire doguwar rigar shi ya yi ya fad'a ban d'aki dan yin wanka, mik'ewa Khadija ta yi tare da hannun Haseenah tace "Ki je ki taya shi wanka, zai iya wuni bai saki maganar nan ba, amma da kin mi shi abin da ya dace sai komai ya wuce." Tura ta tayi ban d'akin ita kuma ta fita, ta na rufo k'ofar ta jingina a jikin k'ofar ta lumshe ido, a hankali ta ji zuciyar ta na hasko mata mijin ta da Haseenah a ban d'akin, yanda ta san mijin ta da sauk'in kai da raha da barkwanci ta san yanzu har sun fara juyewa, da sauri ta bud'e ido har sun cika da hawaye, "A'uzu billahi mina shaid'anir-rajim." Ta furta ta bar wajen, ta na zuwa ta samu Bilal har ya shirya cikin gajeran wando da riga, *cornflakess* ta d'auko da kofi da madara ta yamutsa mi shi, ba dan ran shi na so ba ya karb'a ya na turo baki, shafa kan shi ta yi tace "Yi hak'uri mana yarima, yau ne fa kawai, kuma yanzu za'a kammala abinci." Cikin turo baki yace "Mummy ni da wannan abun gwara ki bani ayaba na ci." "Shikenan to." Ta fad'a ta na mik'ewa, friji (fridge) ta nufa yar k'arama da ke d'akin na ta wacce ita ta siyi abar ta, ta d'auko ayaba biyu da gwanda da ke yanke a faranti ta dire gaban shi tace "To maza ka ci." Da sauri Bilal ya fara ci dan yunwa ya ke ji sosai, kuma a k'a'ida ya na zuwa gida zai samu maman shi har ta kammala abincin, fita Khadija ta yi ta bar shi ta nufi madafa, sai da ta gyara ko ina kamar babu abin da akayi b'ari a ciki sannan ta d'ora ruwan zafi, cikin sauri ta ke komai in da ta b'areye doya ta zuba sannan ta fara had'a sauce d'in. _Tukunya ta d'ora ta zuba mai, bayan ya yi zafi ta zuba silalallan naman ragon da ke fridge wanda ya ji albasa attarugu da maggi, soya shi ta yi sosai ya soyu kafin ta kwashe, albasar da ta yanka mai yawan gaske ta zuba a cikin man, haka ma tumatiri d'anye da ta yanka da fad'i ta zuba a ciki, rufewa ta yi ta fara b'are tafarnuwa, zuwa lokacin albasa da tumatir sun rusuna sosai, kayan k'amshi da gishiri ta zuba kafin ta jajjaga ataru da tafarnuwa da poivron kafin ta jujuya sosai, maggi ta saka da yan ruwa kad'an sannan ta sake rufewa, a lokacin kuma doyar ta ta silala ta juye ta a mataci kafin ta zuba ta in da ya dace, komawa ta yi kan miyar nan ma komai ya yi daidai, k'wai ta d'auko guda uku d'anye ta fasa shi cikin wata k'aramar roba ta kad'a shi sosai, cikin miyar ta zuba ta na motsawa saboda kar ya yi gudaji-gudaji, ta na zubawa kuma ta kawo soyayyen namanta ta zuba sai ta rage wuta dan ta k'arasa dahuwa, doyar ta d'auka ta kai kan teburin d'akin Usman ta dawo ta juye miyar bayan ta fitarwa da mai gadi na shi, tsaf ta jera su akan teburin._ Ta juyo za ta fita dan yin wanka ta ji fitowar su daga d'akin, juyawa ta yi ta kalle su da murmushi tace "Barka da fitowa." Sai da ya kalli teburin yace "Barka baiwar Allah." Haseenah ta kalla tace "Amarya ki yi hak'uri na yi karambani, na kammala mi ki girki amma fa mai sauk'i ne, ban san ko zai birge ki ba." Ta wutsiyar ido ta harare ta amma sai ta yi murmushi tace "Haba aunty Khadija ya ki ka wahalar da kan ki? Gashi kuma da fitar da zaiyi yanzun abinci ne zai siyo mana." Da mamaki Khadija ta kalle ta tace "Siyowa kuma, haba dai amarya, gidan nan cike da abinci Allah ya hore, ga kuma mata ma su rai da lafiya, amma ya fita siyo abinci, a'a gaskiya sai dai in da wata larura." Usman da ke kallon ta da murmushi ne ya taka ya isa ga kujera ya ja ya zauna, tangale hab'a ya yi ya kalli dukan su yace "Ku taimaka ni ku zuba min abincin to na ci." Haseenah da ranta ya gama b'acewa saboda abin da Khadijar ta fad'a d'akin ta ta nufa tace "Aunty kawai ta zuba, tun da dama ita ta yi girkin, ni wanka zanyi." Da sauri Khadija tace "Ni ma fa wankan zan yi." Amma ina Haseenah har ta fita ta shiga k'ofar da za ta sadata da na ta falon, abu d'aya da Khadija
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117