Chapter 72
Chapter 72
na fita ya samu mai gadi shi ma ya gaji da jira ya siyo wake da shinkafa, a hallitar Bilal bai tab'a cin wake da shinkafa ba, amma yau da ya ke jin yunwa sosai kuma mai gadi yace su ci, sai kawai ya sa hannu su ka ci abincin tare, saida su ka gama su ka sha ruwa, sun d'an fara tab'a hira Bilal ya ji cikin shi ya fara k'ullewa, a hankali ya fara dafe ciki ya na d'an matsa shi, amma sai abun ya fara k'amari sosai, mik'ewa ya yi kawai ya koma cikin gida kai tsaye madafa ya nufa, jar kanwa ya samu ya samu kofi ya sa ruwa ya jik'a yasha kamar yanda wani lokacin idan cikin shi na ciwo maman shi ke bashi, har zai fito sai ya ji ciwon ya fi na baya ma, dafe ciki ya yi sosai ya na murd'awa har ya sulale k'asa, jin azabar ciwon na k'aruwa ya sa shi tafiya wajen Haseenah, falo ya same su wannan karan su na kallo ana hira, a dafe da ciki ya tsaya gaban ta yace "Aunty ciki na ke ciwo, dan Allah ki bani magani idan ki na da?" A wulak'ance ta kalle shi tace "Cikin ka kuma? To miye a ciki ya wuce kayan zak'in da kullum uwayen ka ke siyo ma ka ne ka na had'iya, sune kawai za su tambaye ka, ni ba na da magani." Ganin idon shi cike da hawaye ne ya sa ta d'auki kud'i ta mik'a mi shi tace "Je ka siyo maganin bakin titi sai ka sha." Karb'a ya yi ya fita ya na duk'e-duk'e, mai gadi na ganin haka yace "K'aramin Alhaji lafiya ka ke, ya na ga ka na dafe ciki? Ko ciwo ya ke ma ka." Cike da k'aguwa yace "Ba komai." Ya wuce abinshi, da k'yar ya kai kan shi shago ya siyo maganin ya juyo ya dawo, madafa ya zarce ya samu ya sha maganin sannan ya wuce d'akin Haseenah, kwance ya yi bawan Allah akan kujera sai Haseenah tace ai ya sauko daga kan kujera ko ubanshi bai tab'a kwance anan ba, k'asa ya kwanta babu ko tapi (carpet) shinfid'e in da ya ke. Ko dare Haseenah ba ta yi girki ba ta na hutawar ta, Bilal na gefen ta kwance ya galabaita dan babu abin da ya yi sauk'i daga ciwon cikin, sai ma kumbura da cikin shi ya yi kamar zai fashe, hakan ya sa zazzab'i sauko mi shi mai zafin gaske, yamma lis ta kalli Bilal da ke ta rawar d'ari tace "Kai zo amshi nan ka karb'o mana salade wajen mutumin can na tsallaken titi." Da k'yar ma ya iya bud'a idon shi ya kalle ta sunyi jawur, rarrafawa ya yi ya zura mata hannu ya karb'i kud'in da take mik'o mi shi, da wuya ya iya mik'ewa tsaye ya fita sai rangaji ya ke, k'wafa ta yi tace "Munafiki, ciwon k'arya ne ka ke k'irk'irowa saboda kawai ka jaza min masifa." An fara kiran sallah magriba kenan sai ga Khadija ta sallamo gidan, daga jakar ta sai ledar da tayowa d'an gudaliyar ta tsaraba, kai tsaye b'angaren ta ta fara bud'awa ta shiga, uwar d'aki ta shige ta cire kayan jikin ta ta saka doguwar riga ta atamfa, lokacin kuma Aziza ita ma ta sallamo gidan dan Hajia tace ta zo ko aiki ta kama ma Haseenah, zaune ma ta same ta tace ba ta d'ora komai ba, amma ta bada a siyo mu su salade su ci, Khadija kuma jin shiru ba motsin d'an gudaliya ya sa ta sallamo falon Haseenah, "Sannun ku da hutawa." Haseenah da gabanta ya shiga fad'uwa dan ta d'auka ma can za ta kwana, Aziza ce kad'ai tace "Sannu aunty Khadija, har kin dawo?" "Na dawo yanzun nan, ya gida?" Ta tambaya ta na kai kallon ta kowace kusurwa na falon, kallon Aziza ta yi tace "Wai ina Bilal? Ko ba'a dawo da shi ba." Cikin rashin sani Aziza tace "Eh...to, ban dai..." Jin kakarin amai a k'ofar d'akin ne ya sa Aziza yin shiru yayin da Khadija ta fita da sauri dan ta gane ko muryar waye, da sauri ta rumgumo shi jikin ta duk da aman da ya ke bulalowa, take idon ta suka kawo ruwa ta kalle shi tace "Bilal, me ya same ka? Me ka ci ka ke amai haka? Lafiya?" Da k'yar ya iya kallon ta da ido dishi-dishi cikin muryar galabaita yace "Mummy, ke ce? Ki kai ni likita Mummy, ciki na ciwo ya ke." Kuka ta fashe da shi ta manna kan shi a k'irji kamar za ta bashi nono tace "Bilal me ya same ka? Halan ka ci wani abu da ya b'ata ma ka ciki?" Shiru ya yi sai numfashi da ya ke saukewa na wahala, fitowar su Aziza da Haseenah ne ya sa ta kalle su tace "Na d'auka za ku kula da shi ba sai na ce na bar amanarshi a hannun ku ba, amma shine ku na kallon shi a wannan halin, ya yi kyau, ki bani makullin mota na kai shi asibiti." Ta fad'a ta na kallon Haseenah. Cike da gadara Haseenah tace "Ki yi hak'uri, gaskiya ba zan iya baki makulli ba, ko da ya bar shi a hannu na baice na ba ki ba, cewa ya yi idan buk'atar aiki ta tashi da mota sai ayi, kuma akwai wanda zai dinga fita da su." D'auke kan Bilal ta yi daga k'irjin ta cikin hushi ta mik'e tsaye tace "Ina tunanin na jima da fad'a mi ki ba na so ana min wasa da d'ana, wallahi ba ke ba ko Usman ne ba zan lamunci ya min wasa da lafiyar shi ba bare ke, domin kuwa har yanzu shine kad'ai gare ni, shi kad'ai na mallaka a duniya sab'anin Usman da zai iya haifar wasu yaran da wasu mata, misali ke, dan haka ki ban makullin mota yanzun nan kafin kisa hankali na ya bar jiki na miki dukan mutuwa a gidan nan, kinga sai ayi biyu kenan dan na fahimci so ki ke ki kashe min d'an nawa." Jin haka ya sa Haseenah juyawa ta koma falo, da sauri Khadija ta biyo bayan ta tasha gabanta ta shak'i wuyan rigar ta, janta ta yi har saida ta kai ta d'akin ta ta wurga ta kan gado tace "Maza tashi ki d'auko makullin ki bani." Haseenah da ta ji mararta ta d'aure kasa tashi ta yi sai dafe mara, hakan ne ya sa Khadija cire d'an kwalin atamfar dake kan ta ta d'aure k'ugu da shi tace "Na rantse mi ki da Allah idan ba ki tashi kin d'auko min ba ko, wallahi gidan nan sai dai ya kama da wuta amma banga wanda ya isa ya shiga tsakani na da ke ba, Haseenah yaro na ne fa kwance babu lafiya, ga abin hawa a cikin gida kuma na iya sarrafa shi amma ki ce ba za'a hau ba, ba dan larura ce ba ma ni ko kallon motar na sake yi bare har na yi sha'awar hawan ta, dallah ki tashi ki d'auko min." Jiki na rawa Haseenah ta mik'e da k'yar saboda sosai ta ke jin ciwo a marar ta,
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117