Skip to content

Chapter 43

Chapter 43

Kallon Kitse Book One Complete Hausa Novels 1,198 words 0 views Progress saved
Download Book

sunkuyowa ya yi ya lek'a fuskar ta yace "Iyeee! Kunya ce wannan? Kin tuna amarcin kenan? To shikenan bara ki gani." Tsakiyar maman ta ya tusa mata kud'in tare da sumbatar goshin ta yace "Ni na tafi sai na dawo." Sai da ya ksa kaiwa ga k'ofar fita ta d'ago tace "A dawo lafiya, godiyar kuma na mik'o ta zuwa wani lokacin." Yanda ta k'arashe maganar da fari ya sa ya saki murmushi yace "Ina jira, dan nasan abun zai k'ayatar tunda ke ce za ki yi shi." Ya na fita ta tashi ta k'arasa shirin ta, tare da Uwani su ka tafi a motar ta gidan kitso da lalle da ma sauran gyaran jiki, kasancewar babu mutane a wurin ya sa aka fara mata abin da ya kai ta, sun jima sosai a wajen, dan sai kusan k'arfe biyar na yamma su ka koma gida ita da Uwani, tun a hanya ta tsaya ta siye salade dan ta ci, su na zuwa gida Uwani ta shiga gyaren shi ita kuma ta shiga wanka, ko da ta gama shiri Uwani har ta fara yankawa, zaune ta yi su na hira su na aiki har magriba, kuma har lokacin ba ta ga Haseenah sai motsin ta da su ke ji a madafa, a haka duka suka gama aiyukan gaban su suka koma d'aki. Tunda wuri ta yi shirin baccin ta yau saboda ta huta dan gobe ita ce da aiki, doguwar rigar bacci ce a jikin ta da ta sauka har k'asa haka ma hannayen rigar, sanin Usman zai shigo ya sa ta k'i saka komai daga cikin rigar, ma'ana dai babu komai daga ciki bayan rigar, ai kam ta na jin motsin shi ta yi sauri ta mik'e ta fara kai da kawon iska, ya na bud'a k'ofar da sallama a bakin shi, da sauri ya d'ora da "Wai wai wai, kar dai na shigo lokacin da bai dace ba?" Juyowa ta yi da murmushi tace "Wane lokaci ne bai dace Abban Bilal ya ga Umman Bilal ba?" Takowa ya yi zuwa gaban ta ya na kallon ta yace "Ba na tunanin akwai lokacin gaskiya." "Kuma ka fad'a?" Ta fad'a da kafe shi da ido. Hannu ya kai zai kamo ta ta janye ta zauna kan gado ta na fad'in "Dama ina son magana da kai." Zaunawa ya yi ya na fad'in "Uhum, akan me?" Satar kallon shi ta yi tace "Akan maganar kwana ne dama." Da sauri ya kalle ta yace "Me ya faru da kwanan ki? Ina ce gobe ne ko?" Ajiyar zuciya ta sauke tace " Eh gobe ne, amma kuma da matsala." Gyara zama ya yi ya na kallon ta yace "Matsalar me? Ki yi magana mana dan kinsa hankali na ya fara tashi." Mik'ewa ta yi tsaye kamar marar gaskiya ta na kallon shi ta na wasa da yatsunta tace "Eh to, gaskiya dai ba na sallah, shi ya sa na barwa amarya kwanan na wa." "Me?" Ya fad'a ya na tashi tsaye, janyo ta ya yi jikin shi yace "In dai ba b'ata na yi ba ai tunani na lokacin zuwan bak'on ki baiyi ba, me zai sa ya canza lokacin zuwa yanzun? Saboda ya san ina buk'atar ki ne a kusa da ni kome? Ko shi ma haushi na ya ke ji ya na taya ki kishi ne?" Da sauri ta janye daga jikin shi ta yi baya ta na fad'in "A'a ba ko d'aya, gaskiya na ke fad'a ma ka fa, ka yarda mana." Had'e fuska ya yi yace "Naga tafin hannun ki." Da sauri ta mayar da hannayen baya tace "Um um." Murmushi ya yi yace "Wata kala ce kawai ki ke so ki min kuma na gano ki, dan haka ki ci gaba da min shirye shirye kawai." Juyawa ta yi ta nufi ban d'aki ta na fad'in "Ni fai na fad'a ma ka na barwa amarya kai, dan yanzu har na saba da bacci ni kad'ai." Har da gudu ya had'a wajen janyo ta jikin shi ya na shafa ta ya na fad'in "Kenan ba ki yi kewata ba ko kad'an?" Cikin narkakkun idon ta ta kalle shi ta gilashi tace "Idan ma na yi ko banyi ba, idan ka shigo hannu na za sani." A hankali ya matso kan shi ya na son had'e bakin su da sauri ta fizge daga gare shi, juyawa ta yi ta nufi ban d'aki ta na juya mazaunai da gayya, lumshe ido ya yi ya d'an cije lab'en k'asa ya bita da kallo, ta na shigewa ya matsa bakin k'ofar yace "Ni zan wuce sai da safe, ki kula min da kan ki dan Allah." Shiru ta yi har ya fice daga d'akin, ta na jin ya fita ta fito dan dama ba komai ta ke yi ba, kashe wuta ta yi ta zauna bakin gadon ta yi addu'o'in da ta saba yi kafin ta cire gilashin ta ta kwanta abin ta. ************** Bilal na zaune tare da duka iyayen shi yan uwan mahaifiyar shi da kuma kakar shi, dan har yanzu ba su daina had'uwa a falon mahaifiyar su ba suna hira, hira ce ta yi hira har ta sa Bilal fad'a mu su fad'an da mahaifiyar shi ta yi da kuma auntyn shi, rashin jin dad'in abun ya sa Naseer cewa "Ni wallahi dama nasan sai anyi haka, dan tun ranar da suka samu sab'anin nan nasan yarinyar nan ba ta da kunya, in ba rainin hankali ba taya za ki bud'e baki ki ce wai ina anfanin yaro a cikin gidan uban sa? Wallahi ta yi wasa ni sai na ci uban wanda ya d'aure mata gindi ma." Mama ce ta katse shi da cewa "Kamar ya ka ci uban ta? Matar mutane za ka daka har gidan ta? To ba na son sake ji daga yau, ku na so ace ku na taya 'yer uwar ku kishi ne?" Naseer d'in ne dai ya d'ora da "Hajia ba ki san me ta ke mata bane, ranar fa har kuka ta saka ta da hawaye, ce mata ta yi wai makauniya, ki ji fa Hajia, ni tunda na ke ban tab'a jin wanda ya kira ta da makauniya ba." Ashir ne yace "Makauniya fa? Khadijar ce makauniya?" "Wallahi haka ta fad'a mata shegiyar figaggiya." Habeeb da Bilal ke kwance kan k'afafun shi ne yace "Wallahi ni tun ran kan amarya da na ga idon yarinyar nan a tsaye da kuma k'awayen ta masu ido tsakar ka nasan dama za ayi haka, amma dai ta kiyaye b'atawa auta rai, dan ba lallai mu d'auka ba." Bashi ne ya karb'e da "Ba maganar ba lallai bane, magana ce ta ba zamu d'auka ba ko kad'an, wallahi ba za ta shiga gidan ta ba kuma ta nemi ta raina ta, dan haka dole Usman ya sake zagewa wajen tsayawa akan gidan shi, in ba haka ba kuma to zamu ziga ta ta dinga jibgar ta mu kuma a shirye mu ke da mu tsaya mata a kowace kotun duniya." Tsaki Mama ta yi ta mik'e ta nufi d'akin ta ta na fad'in "Saida safen ku, tunda naga dukan ku babu mai hankalin da zaiyi magana ta hankali har kai da ke babba a

Table of Contents

Chapters

117 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117