Chapter 74
Chapter 74
*1* _KAUSSAR_ *2* _D'AUKAR FANSA_ *3* _BA SO BANE_ *4* _AUREN HAD'I_ *5* _SANIN MASOYI_ *6* _JIHADI_ *7* _K'ANGIN RAYUWA_ *8* _ITACE K'ADDARARMU_ *9* _KAWU NA NE_ *10* _MAATA_ *11* _KALLON KITSE..._ *SADAUKARWA GA* _MATAN FARKO_ π§πΌ *(UWAYEN GIDA)* πΈπ¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S* _(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_π€π€ ```Fatan alkairi masoya``` _Bismillahir rahamanir rahim_ *28* Saida ya fara ganin Haseenah ya tabbatar komai lafiya kafin ya nufo wajen Khadija da nufin bala'i, ya na shigowa falon sai ya yi sanyi ganin mutanen dake d'akin, a hankali yake takawa ya na kallon Bilal dake k'afafun Mama ta na bashi magani, Khadija ma da mamaki take kallon shi kamar ba ta tab'a ganin shi ba, da sauri ya k'arasa ya zauna gefen Khadija ya na fad'in "Yarima, bashi da lafiya ne? Me ya same shi?" Shiru Khadija ta yi sai Mama ce tace "Bashi da lafiya ai tun jiya, amma da sauk'i sosai." Hannu ya zura ya kamo shi kamar d'an shekara biyar haka ya rumgume shi a k'afafun shi ya na shafa shi yace "Yarima ba ka da lafiya? Ya jikin na ka da sauk'i ko?" Da kai kawai ya ma sa alamar eh, rumgume shi ya yi a jikin shi ya kalli Khadija yace "Amma ya akayi ba ki kira ni kin fad'a min ba?" Cikin hushi tace "Saboda kai ne silar shigarshi wannan halin, kuma ma naga me za ki yi mana idan na fad'a ma ka? Tunda ba damuwa ka yi damu..." Da sauri Mama ta kalle ta tace "Khadija." Kallon Mama ta yi ta na kumburo baki, Mama ce ta d'ora da "Subhanallah, Khadija haka ki ka koma magana da mijin ki? Ki na hauka ne?" Shiru ta yi sai Usman da ke murmushi ya kalle ta yace "Me ya sa ki ka yi tunanin haka? Taya zan zama sila baya bana nan." Shiru kawai ta yi saboda Mama ta mata magana, mik'ewa Mama ta yi ta d'auki gyalenta ta yafa ta d'auki jaka ta kalli su Naseer dake gefe kamar sun zo neman aure tace "To sai ku tashi mu tafi ko, ko kuma nan za ku tabbata?" Mik'ewa su ka yi a tare da d'ai d'ai suka bawa Usman hannu su ka yi sallama kafin su ka fita, ta na ganin fitar su ta kalle shi tace "Dama na bar Bilal gida ne saboda umarnin ka, amma ka sani ba zan sake wannan kuskuren ba wallahi, tunda dai na gama lura matarka ba imani ne da ita ba, sannan daga yau wallahi ba zan sake d'agawa kowa k'afa ba, duk wanda yace zai min kan kara to tabbas sai nai masa na itace." Mik'ewa ta yi saida ta zo gaban shi ta karb'i Bilal ta d'ora a kafad'a saboda k'arfin halin kafin ta nuna shi da yatsa tace "Da nace kowa ina nufin kowa ma, ba sauk'i a al'amarin." Za ta juya ne taji sallamar su Hajia da sauren yaranta mata biye da ita, tsaye ta yi ta na kallon su har su ka k'araso su ka zauna, Hajia ce ta kalli Bilal da ke kafad'ar ta tace "Kai namijin duniya ya jikin na ka?" Wani irin mamaki ne ya bayyana a fuskar Khadija ta sunkuya ta aje Bilal ta kalle ta da kyau tace "Hajia, ya jikin shi fa ki ke tambaya? Hakan na nufin dama kinsan ba ya da lafiya amma shine bai samu kimar da za ku zo ku duba shi ba tunda ku ka shigo gidan nan, tunda rana fa na ke iya jiyo hayaniyar ku a gidan nan, amma sai yanzu za ku zo ku tambaye ni lafiyar shi, hum, to ba ni ku ka wa ba, kan ku kuka wa." Juyowa ta yi ta d'auki Bilal za ta wuce d'aki Aziza tace "Aunty Khadija ga kayan shi in ji Haseenah." Juyowa ta yi fuska a had'e tace "Bilal na da kayan da a shekara baya saka su, ku mayar mata ta mayarwa da bokan nata tace ba ma so." "Khadija, wai baki da hankali ne? Ke kad'ai ki ka fi kowa baki anan da za ki zaunar da mu ki na fad'a mana magana, so ko ke kice dole ke ce akawa laifi kenan bayan duk abin da ki ka aikata, me ki ka d'auke ni ne da har za ki tsaya ki na fad'awa 'yan uwa na magana kuma daga ciki har da mahaifiya ta, ko kinsan da hushin ki na dawo garin nan? Amma shine za ki nuna ke ce ma akawa laifi, to ya isheki haka, maza wuce ciki zan zo na same ki." Yanda ya ke maganar ne ya sa ta yi dariya tace "To ka had'iye ni mana kaga shikenan sai ka huta." Ta na fad'a ba ta tsaya sauraren shi ba ta shige ciki da Bilal a hannu, tana shigewa Hajia tace "Haka kuma abin nata ya zama? Lallai mutum bashi da kama, yanzu waye zai iya cewa Khadija za ta yi abin da ta yi." Rabi'a ce tace "Hum, dama ai sai anyi yunwa halin kowa ke fitowa." "Gaskiya ne, yau na tabbatar da hakan." Cewar Hajia, Usman ne ya kalle su yace "Hajia ku yi hak'uri dan Allah, kar ku damu da abin da ya faru." "Ya kar a damu, ba ka ji maganganun da ta fad'a mana bane, nan gaba mu ka san me za ta fad'a ko ta yi mana, za ta iya cewa ma Bilal d'an ta ne ita kad'ai." Mik'ewa su ka yi su na fad'in "Sai anjiman ku." Tafiya su ka yi Aziza ta koma wajen Haseenah, shi kuma d'akin Khadija ya koma, ya na zuwa ta kwantar da Bilal yace "Ya kamata kisan ina d'aga mi ki k'afa ne saboda abubuwa dayawa, amma naga sam kin kasa fahimta sai ma son wuce gona da iri, Khadija wannan fa mahaifiya ta da ki ka tsaya ki ka fad'a mata magana son ran ki, me ki ke ji da shi? Rashin kunya ko fitsara?" Tsaye ta mik'e tace "Kalle ni da kyau kaga da me ya kamata ka kira ni." Da yatsa ya nuna ta yace "Na zo ne dan na fad'a mi ki wani abu, wannan ya zama na k'arshe da hannun ki zai sake tab'a jikin Haseenah, in kuma ba haka ba wallahi zan d'auki matakin da ba lallai ya mi ki dad'i ba, kinji na fad'a mi ki." "Haseenah? Haseenah fa ka ce? To in har kaga hannu na bai tab'a jikin ta ba ka tabbatar ba ta min rashin kunya ba, wallahi ko yanzu tace za ta min abinda ba zan d'auka ba ni kuma can ci uwar ta a gidan nan kuma a gaban ka." Daf da ita ya matso cikin d'aga murya yace "Saboda ki nuna min kin rainani? Ban isa na fad'a mi ki kiji ba kenan?" Kafin ta yi magana ya sake k'ure ta da fad'in "Bak'in ciki ki ke da ta samu ciki za ta haifa min wasu yaran? Shi ya sa ki ka yi k'ok'arin zubar mata da ciki, wallahi Allah ne ya ceceki cikin nan bai zube ba, da sai na sa kinyi aman duk wani abu da ke cikin ki kema." Rasa abin fad'a ta yi saboda kukan da ke son taho mata,
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117