Skip to content

Chapter 30

Chapter 30

Kallon Kitse Book One Complete Hausa Novels 1,198 words 0 views Progress saved
Download Book

ni da kyau, daga yau ba na son sake ganin k'afar a madafar nan in har aiki na ne, in ba haka ba kuma zan ci uwar ki a gidan nan sannan na sa mai gida ya yi waje da ke, kinji ni ko?" Kai Uwani ta d'aga alamar ta ji, da hannu ta mata alama tace "Fitar min daga nan, k'azama kawai 'yar matsiyata." Kasancewar Uwan irin mutanen nan ne masu jin zafin magana, wanda da ka zage su yafi sauk'i ka yanke su da wuk'a, hakanne ya sa ta fito tana kuka tana jin k'una na kalmar 'yar matsiyata da ta yi da cewa za ta ci uwa ta, ta na nufowa falon Khadija ta tsinkaye ta, dan haka ta tashi da sauri ta nufe ta, sai da ta rumgume ta a jikin ta ta fara tambayar ta lafiya? Cikin kuka ta ke fad'in "Aunty amarya ce tace wai kar na sake shiga madafa in ta na aiki." Shiru Khadija ta yi tana sauke huci kafin ta d'ago Uwani daga jikin ta tace "Haka ta fad'a mi ki?" Kai kawai ta d'aga mata, d'orawa ta yi da "Shikenan Uwani yi hak'uri, yanzu ina indomien da na saki dafawa?" "Ta na can ta zube." Ta fad'a tana share hawaye da hijabin ta, da k'arfi tace "Ta zube kamar ya?" "Lokacin da ta mareni ne faranti ya sub'uce a hannu na ta zube." Da k'arfi ta dafe k'irji tace "Mari kuma? Ta mare ki fa ki ka ce?" Kai Uwani ta d'aga alamar eh, share mata hawayen fuskar ta ta yi tace "Wuce d'aki Uwani ina zuwa, zanji dalilin marin ki, in ba ta san darajar mutane ba ni na sani." Za ta wuce madafar Uwani ta rik'o hannun ta tace "Dan Allah aunty Khadija ki yi hak'uri, na yafe mata wallahi, ba na so saboda ni ku samu matsala." Fincike hannunta ta yi tace "Uwani kin tab'a ganin b'acin rai na?" "A'a." Ta fad'a har da girgiza kai, "To ki wuce d'aki kamar yanda na ce." Ta na fad'a ta nufi madafar a matuk'ar hassale, daidai lokacin kuma mai gadi ya bud'e k'ofa da motar Usman da ta motar Ashir ta danno ciki, Ashir na kusa da gidan ya ga motar usman, dan haka ya kira shi ya fad'a mi shi ya na tare da Bilal dan haka ya juyo su ka dawo. Khadija kam na shiga ta samu Haseenah ta wanke naman zabbi ta zuba a tukunya za ta kunna wuta, sai da ta tsallaka indomie da ke zube k'asa kafin ta isa gare ta, cikin gadara ta tsaya bayan ta tace "... _Wata yau za ta gane kuren ta fa._πŸ˜‰ *Allah ka sa mufi k'arfin zuciyar mu.* 21/01/2020 Γ  13:34 - πŸ’‹πŸ˜˜πŸ’‹: πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘ *KALLON KITSE* _(Ake wa rogo)_ πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘ _SAMIRA HAROUNA_ *Littatafan marubuciyar* *1* _KAUSSAR_ *2* _D'AUKAR FANSA_ *3* _BA SO BANE_ *4* _AUREN HAD'I_ *5* _SANIN MASOYI_ *6* _JIHADI_ *7* _K'ANGIN RAYUWA_ *8* _ITACE K'ADDARARMU_ *9* _KAWU NA NE_ *10* _MAATA_ *11* _KALLON KITSE..._ *SADAUKARWA GA* _MATAN FARKO_πŸ§•πŸΌ *(UWAYEN GIDA)* πŸ‡ΈπŸ‡¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S* _(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_πŸ€œπŸ€› ```Fatan alkairi masoya``` _Bismillahir rahamanir rahim_ *14* "Haseenah, Uwani ta fad'a min abin da ya faru, kuma har ta fad'a min ma wai kin mare ta, shin hakane?" Juyowa Haseenah ta yi cike da rainin wayo tace "Ki cire wai, gaskiya ne abin da ta fad'a, ko za ki rama mata ne? Sai ki tabbatar min yar aikin gida tafi matar gida." Wani murmushin gefen labb'a Khadija ta yi kafin tace "Ko kinsan kin mana b'arin abincin da yarima zai ci?" Ba tare da ta juyo ba tace "Ban san wani yarima ba a gidan nan, sai Bilal kawai, wanda na ke da tabbatacin ba shi kad'ai bane yaron da zai rayu a gidan nan, k'annan shi na nan zuwa duniya nan gaba kad'an." Wata dariya Khadija ta saki har da rik'e ciki kafin tace "Nagode Allah da ki ka iya tuna Bilal shine babban yaron da ya fara zuwa duniya kuma a gidan nan, hakan ya tabbatar min da mai hankali na ke zaune." Kallon ta ta yi sosai tace "Kasancewar Bilal d'an farko a gidan nan ba shi ke nuna zaifi sauran yaran da za su zo daraja ba, kamar yanda jimawar mahaifiyar shi a gidan bai sa matsayinta yafi nawa ba, dukan mu mata ne kuma matan Usman a gidan nan, aljanna ki ke nema haka nima ita na ke nema." Juyawa ta yi ta d'auki wuk'a hakan ya sa Khadija fizgo wuyan rigar ta da ko hijabi babu a jikin ta, sosai ta shak'e ta tace "Dama abu d'aya na zo fad'a mi ki, Uwani ba wai yar aiki ba ce a gidan nan kamar yanda ki ka d'auka, kuma mai gidan ma yasan da haka, ko shi bai isa ya mata abin da ki ka mata ba, dan haka ya zama na k'arshe da kalma marar dad'i za ta shiga tsakanin ki da ita bare duka, na yarda ki mata fad'a idan har ta yi ba daidai ba, amma banda cin zarafi a ciki, ki kiyaye nan gaba." Sakin rigar ta ta yi za ta fita kawai Haseenah ta ja tsaki tace "Idan shi tsoronki ya hana ya mata magana, ni nan Haseenah zan iya, kuma ki sani shigowa ta gidan kamar shigowar rahama ne da sauyi." Murmushi Khadija ta yi tace "Ina fatan dai ki na da kud'in biyan bokan na ki, dan in ba ki shirya ba za ki sha wahala wajen karb'ar gidan nan a hannu na." Juyawa ta sake za ta fita Haseenah ta kuma cewa"Aikin banza, ai ba boka ba malam wallahi zan karb'i gidan nan, makauniyar banza makauniyar wofi, ai ba a banza Allah ya hana ki idon gani ba." Wannan maganar ta makauniya ita ce ta tsayawa Khadija a rai, da k'arfi ta juyo ta matso daf da ita tace "Me ki ka ce?" Yanda taga idon Khadija sunyi ne ya sa ta kasa cewa uffan, lumshe ido ta yi ta bud'e ta sauke su a kan ta tace "Haseenah ina da yak'inin ban tab'a yin fad'a ba tun da k'uruciya ta har zuwa girma na, sai dai ina ji a jiki na cewa fad'a na zai yi matuk'ar muni, dan haka ina so ki kiyaye, ba na so na yi abin da zai b'ata min suna ko kuma zuri'a ta." Cikin rashin gamsuwa da abin da ta fad'a tace "Wai ke Khadija me ki ke d'aukar kan ki? Mummuna ko me? Akan komai sai kin nuna ke dabance, to ba zan d'auka ba wallahi, kar ki k'ara cewa za ki nuna min izzar ki dan ba ta shafe ni ba." Matsowa Khadija ta yi ta sa hannu ta ture ta baya ta na fad'in "So ki ke kisan me na d'auki kai na? Na ce ki na so ki sani ne?" Hankad'ar da ta mata ce ta sa ta yi baya sosai har ta bige tukunyar da ke kan wuta ruwa da naman ciki ya watse, lokacin da hannun Haseenah ya bugi tukunyar ta ji zafi, hakanne ya tilasta mata sakin razananniyar k'ara har duk gidan na amsawa, Usman, Naseer da su Rabi'a da ke zaune su ka hanzarto su ka nufo

Table of Contents

Chapters

117 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117