Skip to content

Chapter 78

Chapter 78

Kallon Kitse Book One Complete Hausa Novels 1,202 words 0 views Progress saved
Download Book

Mama, amma fa akwai matsala." "Matsala kuma? Tame?" Cikin sanyin jiki tace "Mama wannan layun da aka aje na duba su ban gansu ba, kuma gashi har yanzu ana tsorata ni a cikin dare." Da al'ajabi dattijuwar tace "Toh! Amma abun da mamaki, to ina suke? Kuma kin tabbatar an aje su in da ki ka duba?" "Wallahi Mama wajen ne, su aunty Mariya fa da kan su su ka aje su, amma da na duba babu komai a wajen." "Toh." Ta fad'a ta na girgiza kai kafin tace "Lallai wannan abu ya wuce duk in da ake tunanin shi, amma bari Baban ku ya shigo sai na fad'a mi shi komai." Sosai ta ji dad'in wannan wunin da ta yi a gida, gashi ana ta bata kulawa a matsayin ta na mai k'aramin ciki, sai abin da take so ake bata ta ci, har mahaifin ta ya zo aka fad'a mi shi abin da ke faruwa, a cewar shi ta kwantar da hankalin ta zai sake karb'o mata wasu, sannan ta ci gaba da addu'a komai zai wuce. A b'angaren Khadija kam ganin jikin ya k'i kyau ya sa Mama cewa "Khadija." "Umm." Ta fad'a ta na d'an gyara kwanciyar ta, "Khadija ba ki da ciki kuwa?" Murmushi ta yi tace "Ciki Mama? A'a, ba na da komai wallahi, kawai dai zazzab'in wahala ne." "To Allah ya tabbatar da alkairi." Cewar Mama, Bilal ne ya shigo da sallama ya na cire jakar makarantar shi, kusan maman shi ya je ya sumbace ta da fad'in "Mummy ya jiki? Kinji sauk'i?" "Na ji sauk'i yarima, har kun taso?" Saida ya fara cire rigar shi yace "Eh Mummy, kawu Ashir yace na mi ki sannu da jiki ba zai shigo ba ya na sauri." Mama ce ta katse shi da cewa "Kai d'auki tarkacan kayanka ka wuce da su d'akin ka, kar ka kuskura ka min tsirara a tsakiyar falo." Matsowa ya yi kusan ta ya yi tsaye yace "K'arasa cire min kayan ma in ki na son samun lada." Rufe fuska ta yi tace "Kai b'ace min da gani kaji ko." Fad'awa ya yi jikin ta ya sumbaci kumcinta ya na fad'in "Ina son ki Hajia ta." Rumgume shi ta yi ita ma tace "Ni kuma ba na son ka yau, dan nasan akwai abin da ka ke so waje na." Kallon ta ya yi yace "Me ki ka dafa yau?" Hararan shi ta yi tace "Uhum, nifa na san za'a rina dama, ina ka fito ci ina zaka ci, to wake na dafa." Dariya Khadija ta yi tace "Mama ta na so ta sake kumbura ma ka ciki ne." Juyowa ya yi ya kalle ta yace "Kema kin zama aunty amarya muguwa?" Daruya suka saka sai Mama ce tace "Ai ni mugunta ta ma sai tafi ta ta, dan kuwa idan ka gama ci ba ruwa zan baka kasha ba, sai dai na ba ka kwanan nan fura ka kora da ita." D'aukar kayan shi ya yi ya nufi d'aki ya na fad'in "Kuma idan na mutu ke ce za ki fara zubar da hawaye." "To ba dole ba, na rasa miji na uban 'ya'ya na, idan kai ma na rasa ka ai zan shiga cakwakiya." Usman ya je gida bayan ya aje Haseenah, Hajia kad'ai ya samu dan rana ta take sosai zaiyi wuya ka samu namiji gida a wannan lokacin, bayan sun gaisa ne Hajia tace "Amma me ya hana ka zuwa tun jiya da aka kira ka?" Cikin rashin gaskiya yace "Wallahi Hajia wani d'an aiki ne ya taso min, kuma yarinyar nan ba ta ji dad'i ba, saida ma na kai ta asibiti aka rubuto mana magani." _Daga cikin bala'in da asiri ke iya jawa mutum akwai k'arya, zai iya k'arya dan ya kare kan sa ko kuma wanda ya ke so, akwai rashin kunya ga wanda baya hayyacin shi, abune mai sauk'i miji ya tub'ewa mata kayan ta ya mata wulak'anci a gaban 'ya'yansu, kad'an ne daga aiki sihiri daina ganin girman wanda ka ke ganin girman shi, akwai wasa da addini wanda za ka ga wani ya na sakaci da shi, illolin fa dayawa yan uwa, fatan mu Allah ya k'ara tsarkake mana zuk'atanmu._ Take Hajia ta fahimci k'arya ya fad'a, amma saboda kunya ta dake tsakanin uwa d'an fari sai kawai ta share tace"Allah ya sawak'e, gashi kuma yanzu malam d'in har ya fita, sai dai in za ka same shi can shagon." Cikin sunne kai yace "Ba damuwa sai na je can d'in ai." Ba tare da ta kalle shi ba tace "To ya maganar Nura, ya fad'a min sunyi magana da Khadija kuma tace ka amince, amma a bari sai ka dawo, gashi kuma ka zo ba ka ce komai ba." "Eh Hajia, ya na ina ne Nuran?" "Ya na shago mana." "Shikenan zan kira idan na fita saiya same ni ko can shagon Murtala ne." Cikin had'e tafukan hannayenta tace "Hakan ma ya yi." Kallon ta ya yi yace"Hajia me zai hana ku je ku d'auko Bilal?" Sai lokacin ta kalle shi tace "Ban gane na je ba? Kai me zai hana ka tafiya? Kuma ma ka na nufin ba za ka je ka dawo da mahaifiyar shi ba kenan?" Cikin b'acin ran an ambaci sunan Khadija yace "Hajia ni babu in da zanje, ita ta tafi saboda ta na so, dan haka taje can ta k'arata, ni yaro na ne kawai matsala ta." Karo na farko a rayuwa da Hajia ta iya d'agawa Fodio murya, cikin jin haushi tace "To ba zan je ba, ranar da ka shirya ganin d'an na ka sai kaje ka d'auko shi da kan ka." Kallon ta ya yi shima, amma saboda ran shi a b'ace ya ke da maganar Khadija sai kawai ya mik'e cikin kumburo baki yace "Ni zan wuce, sai anjima." Da kallo kawai ta bi shi har ya fita daga gidan, girgiza kai ta yi ta na mamakin wannan canjin daga Fodio, mik'ewa ta yi ta shiga d'aki ta na fad'in "Ai kuwa da alama gaskiya malam ya fad'a, amma koma menene zan wa tubkar hanci." Daga nan wajen malam ya zame, k'ofar shagon ya samu malam zaune akan bacci shi da wani suna hira, har k'asa ya durk'usa ya gaishe su kafin malam ya sallami waccen, mayar da kallon sa ya yi kan Usman da ke durk'ushe yace "Fodio sai yanzu ka zo kiran nawa? To nagode." "Wallahi Baba..." D'aga mi shi hannu ya yi alamar ba ya son ji kafin ya d'ora da "Jiya na je gidan su Khadija, kuma naji duk abin da ya faru, Fodio ka bani mamaki sosai da na ji ance wai ka d'aga hannu ka daki Khadija, wannan abun kunyar har yaushe da irin shi, duka! Kai a matsayin ka na mai hankali da ilimi, a shekarun ku na k'uruciya haka ba ta faru ba sai yanzu da girma ya fara riskar ku, wanda ya kamata ace yanzu ne soyayya take da tausayin juna, amma ace ka dake ta akan abin da ma k'arya ake mata da sharri, kawai rud'in zuciyar ka ne ka biyewa da kuma wata banzar hud'uba da wasu sakarkari suka ma ka, kasan me ya sa ta karb'i makullin

Table of Contents

Chapters

117 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117