Chapter 1
Chapter 1
13/12/2019 à 20:33 - Les messages envoyés dans ce groupe sont désormais protégés avec le chiffrement de bout en bout. Appuyez pour plus d'informations. 13/12/2019 à 20:33 - Vous avez créé le groupe “💑KALLON KITSE💑” 13/12/2019 à 20:34 - Vous avez retiré Sis Meerah 13/12/2019 à 20:35 - Vous avez changé l'icône de ce groupe 21/12/2019 à 15:34 - 💋😘💋: 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑 *KALLON KITSE* _(Ake wa rogo)_ 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑 _SAMIRA HAROUNA_ *Littatafan marubuciyar* *1* _KAUSSAR_ *2* _D'AUKAR FANSA_ *3* _BA SO BANE_ *4* _AUREN HAD'I_ *5* _SANIN MASOYI_ *6* _JIHADI_ *7* _K'ANGIN RAYUWA_ *8* _ITACE K'ADDARARMU_ *9* _KAWU NA NE_ *10* _MAATA_ *11* _KALLON KITSE..._ *SADAUKARWA GA* _MATAN FARKO_🧕🏼 *(UWAREN GIDA)* 🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S* _(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛 _Na karb'i uzurin uwaren gida wannan karan, na kuma fahimci kukan su, sun ce kullum in dai labari ya biyo tsakanin miji da matan shi biyu, to sai marubuta sun yi k'ok'ari sun nuna uwar gida ce marar kirki, a k'arshe sai amarya ta mallake mijin, alhalin kuma a zamanin nan yanzu ba haka bane, dan haka dan Allah mu gyara, zaiyi wuya ace kullum uwar gida ce marar mutunci, duba da dayawa daga cikin maza sai sun k'ara auren ma su ka gane kirkin matan su na farko, ba ma miji kad'ai ba har da dangin shi, dan haka ku share hawayen ku, *Samira* za ta cika mu ku zuciyar ku da farin ciki, a matsayin ta na uwar gida ita ma uwar katarere😉, su momyn Dady *d'ogalawa* ne😂, ku biyo ni muji wa ake wa kallon kitse ne._ ```Fatan alkairi masoya``` _Bismillahir rahamanir rahim_ *1* Cikin kuka ta cire glishin (glass) idon ta ta kalle shi tace " Abban *Bilal* me na yi ma ka? Wane laifi na aikata da har za ka hukunta ni ta hanyar yi min kishiya? Abban Bilal ka dai na so na ne ko me? Me na rage ka da shi da har za ka k'ara aure a wannan lokacin? *Shekara goma sha uku* mu na tare da kai, ba ka k'ara aure ba sai yanzu, sai yanzu da na fi buk'atar ka a kusa da ni? Me ya sa? Me ya sa za ka k'ara aure? Ka gaji da zama da ni ne? Ko kuma dangin ka ne su ka saka ka k'ara aure, saboda har yanzu ban k'ara..." Yasan me za ta fad'a, dan haka ya yi saurin rufe mata baki, manna kan ta ya yi a k'irjin shi ya na shafa bayan ta ya na fad'in "Haba Momyn Bilal, me ya sa za ki bari har shed'an ya shiga zuciyar ki ya rik'a raya mi ki wannan tunanin? Ni na fad'a mi ki kin min laifi? Ko kuma na fad'a mi ki zan k'ara aure ne saboda na dai na son ki? Haba dan Allah, ki nutsu mana, sannan ki saurare ni, ta hakane kad'ai za ki fahimce ni." Da k'arfi ta d'ago daga jikin shi tace "Fahimta? Na fahimce kama ka ke cewa? Ai ni da k'ara fahimtar ka kuma har abada, ka riga da ka ruguza yarda da fahimtar da na ke ma ka a baya, Abban Bilal, wallahi ba zan sake sauraren ka ba, ka cuceni, ka zalunce ni, tsawon shekaru na d'auka ina rayuwa a k'ark'ashin yaudarar ka, kullum ka na fad'a min ni kad'ai ka ke so, ba ka da sha'awar k'ara aure a rayuwar ka, ba ka da wani dalilin da zai sa ka k'ara aure, amma shine yanzu za ka zo min da wai za ka k'ara aure, lallai, sai yau na yarda da ake cewa namiji ba d'an goyo bane, kuma duk macen da ta rik'e namiji uba, to tabbas za ta mutu marainiya, gashi na ga zahiri." Ganin yanda take kallon shi ya san ba ta ganin shi da kyau saboda lalurar ta, dan haka ya d'auki glishin da ke gefe ya fara k'ok'arin saka mata, buge hannun shi ta yi ta zauna kan kujera ta na fad'in "Rabu da ni, macuci kawai." Da tsantsar mamaki ya kalle ta har ya zauna kusa da ita, ba tare da ya daina kallon ta ba yace "Dan Allah Momyn Bilal ki daina kukan nan, kinfi kowa sanin matsalar ki, dama ya lafiyar idon ki, bare kuma ki na irin wannan kukan, ki daina dan Allah, kinsan kukan ki ya na matuk'ar tab'a zuciya ta, wallahi ba na son ganin zubar hawayen ki ko da na farin ciki ne, da kinsan irin rad'ad'in da na ke jin a game da zubar hawayen nan na ki, to hak'ik'a da kin tausaya min kin share hawayen ki, sannan ki saurari mijin ki." Cikin share hawaye tace "Ai da kan ka ka je ka ciro min tikitin (ticket) kuka, sannan da hannun ka kama nawa hannun ka d'ora ni a motar tashin hankali, *Usman* wallahi ban yi tsammanin haka daga gare ka ba, ama shine har ka ke wani cewa wai na daina kuka, humm." Jingina bayan shi ya yi ga makekiyar kujerar cikr da nuna damuwa yace "Assha, ban zaci haka daga gare ki ba, gaba d'aya na ji na rasa k'arfin gwiwar da na shigo da shi gidan nan, gaba d'aya na ji na tsani kai na, na ji ina ma mutuwa ta d'auke ni kafin wannan ranar, ni *Usman*, ni ne yau na yi silar zubar hawayen mata ta, abar alfahari na, farin ciki na, kwanciyar hankali da nutsuwa ta, kuma uwar d'ana mafi soyuwa a zuciya ta, tabbas yau d'in nan na ji kamar rayuwa ta ba ta da anfani, macen da na ke matuk'ar so fiye da komai, wai yau ita ce ta ke kira na da macuci, macen da na ke d'aukar farin cikin ta da mahimmanci, yau ita ce ta ke kira na da azzalumi, macen da bayan mahaifiya ta, ita kad'ai ce na fi d'auka da mahimmanci, amma ita ce ta ke kira na da mayaudari, macen da na ke d'aukar addu'ar ta gare ni tamkar addu'ar mahaifiya ta, amma ita ce ke cewa na yankar mata tikitin kuka, matar da na ke da yak'inin rayuwa ta ba za ta tab'a moruwa ba idan babu ita a tare da ni, ita ce ke k'ok'arin ruguza farin cikin gida na." D'agowa ya yi daga jinginar ya na kallon ta yace " *Nana Khadija* ta da na sani, ta na da hak'uri, ta na yakana, ta na da fahimta, sannan ta na da uzuri wa mutane, haka ma ta na son duk abin da na ke so, da zan ce wannan abun bak'i ne alhalin fari ne, to ba musu Khadija za tace tabbas bak'i ne, ko da kuwa za'a yanka ta ba za ta sauya maganar ta ba, dan haka ni ba zan bar wannan hawayen na ki su ci gaba da zuba ba, ni mai son ki ne har kullum, k'auna kuma ba k'arya ba ce, dan haka Nana Khadija ta na fara *auren nan*, in dai har auren da zan yi shine silar fara shiga damuwar ki, to na fasa har abada." Tun da ya fara magana ta ji jikin ta ya yi sanyi, maganganun shi sun tab'a zuciyar ta sosai, amma sai ta kasa kallon shi saboda kunyar da ta rufe ta, a hankali ya dafa kafad'ar
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117