Skip to content

Chapter 14

Chapter 14

Kallon Kitse Book One Complete Hausa Novels 1,202 words 0 views Progress saved
Download Book

Abban Bilal, na k'arar da rayuwa ta wajen killace ma ka kai na da mutunci na, amma kai a dare d'aya tak ka kusanci wata mace, zuciya ta bugawa take, ji na ke kamar zan mutu dan bak'in ciki wallahi." Usman kam jikin shi ne ya yi sanyi sosai, tunawa da yanda auren su ma ya kasance, duk da kusan had'a su ne akayi amma ko sau d'aya duk da matsayin Khadija na mace, ba ta tab'a nuna ma sa k'iyayya ba ko a idon ta, amma yau gashi ta na fad'in ba ta son yana zuwa kusa da ita, a hankali ya d'ago ta ya share mata hayawen fuskar ta ya na girgiza mata kai, hannayen ta ya had'e ya rufe idon shi ba tare da ya had'a ido da ita ba yace "Ki yi hak'uri Khadija, ki gafarce ni idan hakan da na yi ya b'ata mi ki rai, har zuciya ta banyi haka dan muzguna mi ki ba, ba kuma na yi bane saboda wani kaso daga cikin kason da ki ke da shi a zuciya ta ya ragu ba, babban k'arfin gwiwa ta akan auren nan shine, Nana Khadija mai halin girma da hak'uri za ta taya ni kare hakk'in da ke kai na, sannan a lokacin da aka d'ora min nauyin Haseenah a kai na wallahi zuciya ta ta fad'a min cewa Khadija na tare da kai, da izinin ubangiji za ta taimaka maka wajen ganin ba ka k'untatawa yarinyar mutane ba, amma kash! Shed'an na ta k'ok'ari sai ya kutso cikin gida na ya tarwatsa min kan su, babban abun bak'in cikin shine, ya na so ne ya shigo ta hanyar mata ta Khadija abar so da k'auna ta kuma abar alfahari na." Tafin hannun ta tasa ta goge hawayen, murmushi ta masa mai d'aukar hankali, matuk'a tasan mijin ta na son ta, kalaman shi kullum suna k'arfafa mata gwiwa da kuma sace mata gwiwa, ganin wannan murmushi ya sa ya kama kumatunta yana murmushi yace "Dariya a fuskar ki shine abin da Usman ke son gani a kullum, murmushin ki kuma shi ne silar nawa murmushin, ki ci gaba da murmushi irin haka har lokacin da zamu koma ga ubangijin mu." K'asa ta yi da kan ta tace "Kalaman ka su na sani jin kunya." Tallabo fuskar ta ya yi yace "Ke ce sarauniya, na baki zuciya, ke ce guda d'aya duniya ta masoya." Yanda ya rera mata baitin ya sa ta sake fad'awa kan kirjin shi ta na murmushi, d'agota ya yi yace "To a bani sumbata kafin na fara zanga-zanga a gidan nan." "Me ya yi zafi? Ba sai an kai ga haka ba, bani bakin ka nan." Sai da su ka gama lobayyar su kad'ai su ka fito, Haseenah da ta ji shigowar shi ta gaji da jiran shigowar ta shi kasa jura ta yi, falon Khadija ta shigo sai Bilal kad'ai ta samu ya na karatun shi, tun ta na zaune har ta fara kai da kawowa tsakiyar falon kamar za ta had'e zuciya ta mutu, ta na jin bud'a k'ofar ta juya da k'arfi, taushe b'acin ran ta tayi ta tafi a guje dama ba nauyi ba kamar ni😉, ai kuwa sai ta d'ane a jikin shi ta na fad'in "Rabin rai na, na yi kewar ka sosai, har zan fara kuka." Bilal da Khadija kallon su suke da ido, a hankali ya d'ago ta daga jikin shi da nufin mata magana, sai kawai Haseenah ta fashe da kukan shagwab'a ta na fad'in "Wallahi da k'yar na iya riskar wannan daren saboda kewar ka, a gaskiya ba za ka sake bari na gidan nan ni kad'ai ba." Sake fad'awa ta yi jikin shi, Khadija da ta ji wasu hawayen na neman taho mata ne ta juya ta kamo hannun Bilal su ka bar falon, lallab'a ta ya yi su ka koma na su falon, duk k'ok'ari Haseenah ta yi shi ta saka shi kalar nata farin ciki, wanka ta mi shi ta saka mi shi kaya marar nauyi, har uwar d'akin ta kai mi shi abinci a bakin gado ta aza akan k'aramar kujera, sam bai iya tuna su Khadija ba haka Haseenah ta dinga yanka masa loma ta na aika masa a baki ya na wucewa da ita ta mak'ogoro, ita kam dad'i ne ke kashe ta saboda ya na sake cin abincin da ta zuba garin maganin da malam ya bata, sai da ya k'oshi kad'ai ta bar shi ta ci nata a zuwan ta k'osar da wanda yafi mahimmanci a gare ta, falo ya koma ya na kallo ita kuma ta na d'aki ta d'auko garin maganin matan ta wanda sai za'a kwanta ake sha, duk da madara ta sha su kafin ta shiga ban d'aki ta sake zaunawa a cikin tafasashen ruwan bagaruwa, sai da su ka huce ta fito ta d'auki wani arnan magani na matsi emergency, k'anana ne fari kamar k'wayar magani, matsawa ta yi haka ma miski sannan ta fito ta saka kayan bacci ta shek'a kwalliya, minti sha biyar ta koma ta kama ruwa da ruwan zafi k'a'idar maganin kenan, fitowa ta yi cikin sand'a ta rufe mi shi ido ta baya, murmushi ya yi yace "K'amshin nan da na ke ji ya sa babu abin da na ke son gani sai ke." Bud'e mi shi idon ta yi cikin karairaya ta dawo gaban shi, k'are mata kallo ya yi yace "Iyeh! Wow, wane irin kyau ne wannan? Tabarakalla ahsanul-kalik'ine, Allah abun godiya." Janyo hannunta ya yi ya zaunar da ita akan cinyar shi, k'amshin humrar ta ne ya tafi da imanin shi, tuni ya fara aika mata da wasu sak'onni wanda take ta ke karb'ar su, dan magungunan da tasha masu k'arfi ne sosai, da k'yar dai su ka iya kai kan su uwar d'aki su ka kashe wuta, surukina gyara kimtsi mana, ina fa taya 'yata kishi.😎 Abunka ga ba saban ba, sosai Haseenah ta yabawa aya zak'inta, amma dai tun da taji Usman na gurnani ya na sambatu da surutai har ya na neman shid'ewa, hakan ya sa ta ji kwalliya ta biya kud'in sabulu, dama kuma *ado gwanja* yace "Rai ba'a bakin komai ya ke ba wajen biyan buk'ata."😂 Haka dukansu su ka yi baccin gajiya rumgume da junan su, washe gari kam bai bari Haseenah ta shiga madafa ba, kuma ba ya so yace Khadija tayi, fita ya yi ya samo mu su soyayyen k'wai da dankalin turawa, ya na zuwa kuma ya samu Khadija har ta had'a abin karin da ta san d'an ta ya fi so, falon ta ya same ta suna karyawa da yaron ta, gaisawa su ka yi kafin yace "Yarima har ka shirya ne?" "Eh Abba." "To idan ka kammala sai ka fito mu wuce." Kallon shi Bilal ya yi yace "Abba yau ina so na je da d'an moto na, kaga ba sai na jira ka je d'auka ta ba." D'an b'ata rai ya yi yace "Kai Bilal, mahaukaci ne ni da zan barka ka tafi a hanyar ababen hawan nan kai kad'ai akan moton ka, bana so, kuma na fad'a maka hawan moton ka kar ya wuce cikin unguwar nan, duk da cazashi ne ake amma ba na

Table of Contents

Chapters

117 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117