Skip to content

Chapter 105

Chapter 105

Kallon Kitse Book One Complete Hausa Novels 1,202 words 0 views Progress saved
Download Book

tokare mata mak'oshi ta kalle shi da murmushi ta sa hannu ta karb'i k'atuwar ledar hannun shi ta aje gefe tace "Mai jiki gashi nan da sauk'i." "To Allah ya bashi lafiya." Ya fad'a ya gyara tsayuwarsa, sake d'agowa ta yi ta kalle shi, saida ta k'are masa kallo tace "Babban mutum ka ci abinci kuwa?" Wani murmushin gefen labb'a kawai ya yi bai bata amsa ba, duk da zuciyarta na raya mata wani abun amma kuma k'wak'walwarta na hasko mata wani abun, kawai anfani tayi da abin da k'walwarta ke hasko mata ta kalle shi ta mik'e tsaye tace "Ina ga mu tafi gida kawai, ga Mama nan za su kwana a wajen shi." Da mamaki ya kalle ta ya kuma juya ya kalli Mama, mama ce tace "Kuje kawai zan zauna wajen shi, ai ni ce ke daidai dama na tsaya tare da shi tunda d'an gudaliyar mijin ne." Murmushi su ka yi kafin Usman ya fara fita ita kuma ta had'a kayanta ta same shi a mota, kallonta ya yi yace "Wane gidan zan kai ki?" Dariya ta yi tana kallon shi tace "Gidan miji na mana, ko ka manta yau ne zan dawo dama?" Lumshe ido ya yi ya kwantar da kanshi jikin kujerar motar, d'agowa ya yi ya kalle ta yace "Khadija Allah ya miki albarka, kamar kinsan ina buk'atar kulawar ki, Khadija duk duniyar nan ke kad'ai ce macen da ta iyani." Da murmushi a fuskarta tace "Muje to ka min wanka ka canza min kaya, sannan na sama mana abun da za mu ci sai muyi bacci." Wata harara ya dallo mata yace "Baccin lafiya? Yau fa kamar amarya ki ke." Dariya ta sake yi tace "To mu samu muje gidan ko." Tayar da motar ya yi su ka d'auki hanya, saida ya tsaya ya siya musu sandwichs a hanya kafin suka wuce gida, tare suka shiga wanka suka shirya cikin kayan bacci kafin suka d'an sama cikin su sandwich d'in nan, sam Khadija ta manta ma da maganar wata wai Haseenah, hakan yasa ba ta tambaye ta, shiru d'akin ya d'auka saida Khadija ta juyo in da Usman ke kwance, zaune ya ke akan gadon ya tangale bayan shi da pilow damuwa b'aro-b'aro a fuskar shi, tashi ta yi zaune ta matsa kusan shi ta d'ora hannun ta akan k'irjin shi tare da d'ora kanta a kafad'ar shi, gyara mata zaman ya yi ta yanda yake shafar kanta a hankali, cikin taushin murya tace "Bilal ka ke tunani ko?" Shiru ya yi kamar ba zai amsa ba sai kuma ya sauke ajiyar zuciya yace "Hakane, muna kwana nesa da Bilal a lokacin da ya kwana gidan su Hajia ko gidan su Mama, amma ban tab'a tunanin akwai ranar da za ta zo ba ina kwance kan gado na cikin sanyi shi kuma ya na kwance a gadon asibiti, ban tab'a tunanin haka ba ko kad'an." Zunbur ta tashi zaune tana kallon shi tace "Ba ka tab'a tunanin wannan ranar ba? Amma me ya sa? Ko ka manta da mutuwa ne?" Shiru ya yi ya tsareta da ido, d'orawa tayi da "Abban Bilal, mu gode Allah daya kasance ya na raye mana, da fa ta Allah ta kasance da yanzu ka na kwance akan gadon nan ne shi kuma ya na kwance cikin rami, zanin rufar shi shine k'asa, kaga kuwa sai mu gode Allah a hakan ma." Murmushi kawai ya yi bai ce mata komai sai kallon ta da yake, matsawa ta yi ta sake lafewa a jikin shi tace "Yau fa dare na ne na farko, kar ka bari tunani da damuwa suyi tasirin hana ka kula da ni da kuma wannan bawan da baisan ma asalin yana da mahaifi ba har yanzu, ka bamu kulawar ka mana na wannan dare, karka damu da Bilal insha Allahu ya na cikin kariyar ubangiji tare da kulawar Mama, zaiji sauk'i." Dariya ya yi ya matse ta sosai a jikin shi yace "To yanzu me kuke so na fara mu ku, dan dole zansa wannan d'an baban farin ciki yasan cewa yau fa ya shigo hannun shi, amma ina fatan dai kin shirya karb'ar uk'ubata?" Da mamaki ta kalle shi tace "Ban gane uk'ubar ka ba?" Murmushin mugunta ya mata yace "Nasha wahala sosai kafin ki yarda ki dawo gida na, kin whalar da ni sosai, kin azabtar da ni fiye da tunanin ki, dan haka nima yanzu zan rama a daren nan tunda kin shigo hannu na." Zabura ta yi ta na neman durkuwo daga kan gadon ya yi saurin rik'o ta yana fad'in "Ai ba ki isa wallahi, ina ki ke tunanin za ki je a daren nan? Daga ni sai ke fa a gidan." Kukan shagwab'a ta saka mi shi tana zillewa tana fad'in "Allah bar ma gidan ka zanyi, ciki na fa k'arami ne, so ka ke min asarar shi bayan 'yan uwan ka har tsegumi suka fara min saboda ban k'ara haihuwa ba, Allah ni dai ka rabu da ni." Sosai ya rumgume ta yace "Mak'aryaciya kawai, na fa san komai, cikin ki ya kusa shiga wata shida, a hakanne zan zubar da shi?" "Ni dai ka sake ni na koma d'aki na kawai tunda mugunta za ka min." Ta fad'a ta na son raba kanta da shi, ya rik'e ta sosai ya rad'a mata a kunne "Na mi ki alk'awarin tafiyar da ke a hankali, abinci kawai zan baku cike da k'aunar ku." D'ago kai ta yi ta kalle shi tace "Na ga idon ka idan gaskiya ka ke fad'a." Da sauri ya sa tafukan hannayen shi ya rufe fuska ya juya mata baya yace "Um um, ban yarda ba gaskiya." Cakulkuli ta fara masa ta na fad'in "Ashe ba gaskiya ka fad'a ba, yeee Allah ya tona min kai." Da irin haka suka tafiyar da daren su cike da kewar juna, bayan komai ya kammala ma alwala su ka yi Usman na gaba ita a bayan shi su ka yi k'iyamun-laili, ana kiran sallah farko ya nufi masallaci ita kuma ta mayar da sallahnta, daga nan kan darduma bacci ya d'auke ta, ko da ya dawo ya ganta d'aukar ta ya yi ya kwantar akan gado, makullin mota ya d'auka ya fita ya samo mu su abin karyawa ya aje kafin ya shirya ya fita zuwa asibiti, duk lokacin Dije na bacci bata farka ba, ya jima a asibiti tare da Mama da malam da Hajia suna ta hira kafin ya baro asibitin, gida ya dawo kai tsaye ya samu Khadija zaune akan teburin cin abinci ta na zubawa za ta ci, k'arasowa ya yi ya zauna yace "Dijangala tame gari, Dije sarkin hutu har an tashi kenan?" Murmushi kawai ta yi tace "Na tashi, amma kuma saina nemi mijina na rasa in da ya shiga, kad'an ya rage na bayar da sanarwa a gidan radio sau kuma ga ka." Cikin dariya yace "Allah ya na son ki da rahama shi ya sa ba ki yi asarar kud'in ki ba." Zaune ta yi ta na aje farantin abincin gaban shi tace "Kuma na yi sa'a miji na ya na iya jiyo bugun zuciya ta daga duk in da yake, hakan ma ya taimaka wajen dawowar ka kusa

Table of Contents

Chapters

117 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117