Chapter 108
Chapter 108
alhalin kuma duka mutane *kallon kitse su ke wa rogo*, ke da ake gani ba ruwanki ke ce kuma gubar." Cikin jin haushi Haseenah tace "Ni ce ma gubar? To idan ni guba ce ke kuma fa? Ai ke ce babbar guba tunda ke ki ka haddasa komai, ina zamana lafiya ban tab'a tunanin wacece matar shi ba, amma ke ki ka zo min da labarin cewa matar shi yar duniya ce ta mallake shi, sannan waya kai ni wajen malam in ba ke ba, wa yake zuwa har gida na ya na karb'o kud'in da ake kaiwa malam d'in? Ai ke ce da kan ki, amma shine yanzu za ki kira ni da guba, to ke ce babbar guba ba ni ba wallahi." Tab'e baki Mariya ta yi a ran ta tace "Sakarya kawai." A fili kuma cewa ta yi "Wannan kuma ke ta shafa, ni kinga tafiya ta sai anjima." Ta na fad'a ta mik'e za ta fita sai ga mahaifiyar su ta shigo d'akin dan kaf babu abin da bata ji ba, baya ta rumgume hannaye ta na kallonsu cike da haushi kafin tace "Abin da ku ka aikata kenan? Mariya, Haseenah, wannan ita ce tarbiyyar da mu ka baku a gidan nan? Wannan wane irin zubar da mutumci ne? Kenan mutuwar auren ki ba ya da nasaba da kishiyar ki? Haka kawai kinsa muna kallon ta a matsayin mai laifi, to rashin lafiyar da muke tunanin ki na fama da ita fa har da nemo mi ki magani? Ko dai duk k'arya ce ki ke? Dan babu yanda za ayi mata biyu a gidan miji d'aya su zama mushrikai." Sosa kai Haseenah take cikin rashin abin fad'a sai tsohuwar ce ta k'ara da "Ko ba ki fad'a ba ya nuna ba ki da gaskiya, amma Haseenah taya ki ka iya shirya makirci irin haka? Ko ni da na haife ki ba zanyi abin da ki kai ba." Kallon Mariya ta yi sama da k'asa tace "Babbar banza, yanzu idan akwai wanda ya kashe mata aure ai bayanki ya ke." K'asa ta yi da kanta sosai hakan ya sa tsohuwar juyawa ta fita ta barsu, cikin sanyin jiki Mariya ta fita sai Haseenah da ta fashe da kuka, *Asiya* kuma d'akin ta ta koma ta shirya saida ta fito za ta fita ta lek'a d'akin Haseenah tace "Zan fita yanzu, babu kowa a gidan ki fito ki d'ora girkin rana kafin yaran nan su dawo, daga yau kin bar kwanciya a d'aki da sunan wai ki na da ciki a tausaya mi ki, girki da wanke-wanke ya zama na ki." Ta na fad'a ta fice abin da har zuwa bakin ti-ti ta samu adaidaita ta hau, kai tsaye gidan Khadija ta isa, duk da ba sosai Khadija tasan ba amma dai ta gane ta, sosai ta tarbe ta kamar za ta had'e ta cikin girmamawa, dama kuma in dai ta wannan fannin ne Khadija gwana ce, hakan ya sa ma take da farin jinin al'uma, har d'akin Bilal ta rakata taga jikin shi kafin su ka dawo falo ta zauna, cike da dattako tsohuwar ta kalli Khadija tace " 'Yata Khadija, na zo ne ganin jikin yaron ki da sai jiya na ke jin bai da lafiya, sai kuma abu na biyu na zo na baki hak'uri akan abin da ya faru, 'yar nan wallahi ba mu tab'a tunanin Haseenah za ta iya cutar da wani ba, amma sai yau kuma yanzu na ke jin irin ta'asar da su ka yi ita da 'yar uwar ta daga bakin su, hak'ik'a yau Allah ya wanke ki daga zargin da mu ke mi ki, muna kallon ki a matsayin wacce take hana 'yar mu zaman gidan aure, ashe ba haka bane komai makircin su ne, ashe har zuwa gidan da take ta nuna bata lafiya ba ta son zaman gidan duk k'arya ne, kawai d'ora mi ki laifi ne suke son yi, dan Allah ki yi hak'uri ki yafe mana kinji 'yar albarka." Khadija da ta yi jim ta na jinjina al'amarin Haseenah, sai yanzu ne take sanin wannan labarin na rashin lafiya, kenan ita ake kallo da wannan laifin ma, murmushi ta yi ta rik'o hannun Asiya tace "Mama, ke fa uwar ce a gare ni, yanda Mama na bata neman gafara na akan duk abin da za ta min to haka ke ma, wallahi na yafe mu ku dukan ku, ni dama ban tab'a rik'e kowa a zuciya ta ba saboda ina so nima Allah ya kalle ni da idon rahama, dan haka ku kwantar da hankalin ku yanzu mun zama d'aya ni da ku, kuma ita rayuwa dama haka take, wanda wautar shi ta fito fili shi ake kamawa da laifi, wanda kuma ya iya takon shi to ko shine mai laifin sai kaga babu mai gani bare ayi magana, kuma ita dama ance *fahimta fuska* ce." "Hakane kam, Allah ya mi ki albarka, Allah ya sa ki gama da duniya lafiya, Allah ya kare ki daga sharrin abokan zama irin su Haseenah." Sakin hannun ta Khadija ta yi ta mik'e tace "Ni zan tafi, dama ko mahaifinsu bai san na zo ba." D'aki Khadija ta shiga ta tarkato kaya sabulu da turaruka da turmin atamfa mai kyau, sannan ta had'o da wani k'aton mayafi da ita bai birge ta ba tunda mama ta siyo mata shi daga Dubai, haka ta had'a tsohuwar nan da su ta rakata har k'ofar gida, Rabe da ke zaune tace ya d'aukar mata kayan har saida ta samu adaidaita, Asiya kam a adaidaita har kuka ta yi ganin irin alherin da Khadija ta yi mata, ta na komawa gida ta samu mahaifinsu ya dawo zaune a tsakar gidan, tun bata gama shigowa ba yace "Daga ina ki ke Asiya?" Kai tsaye tace "Daga gidan Usman." Da sauri ya kalle ta haka ma Haseenah da ke bakin murhu ta na girki duk ta yi gumi, cikin hushi yace "Yanzu da na ce kar ki jr shine ki ka wanke k'afa ki ka tafi ba da izini na ba? Asiya yaushe ki ka fara yin watsi da maganata? Akan matar da ta kashe ma yar ki aure ne za ki wulak'anta ni haka?" Abun da bai tab'a faruwa ba shine yau ya faru, cikin d'aga murya tace "A'a malam, kar ka sake ganin laifin ta akan zunubin da 'yarka ce ta aikata shi, wannan yarinyar babu abin da ta aikata, kaga mai laifin nan gaban ka." Ta fad'a ta na nuna Haseenah wacce ta yi k'asa da kan ta, a tausashe yace "Me ki ke nufi da ba ita ce mai laifi ba Haseenah ce?" Kujerar katako ta janyo ta zauna kusa da shi ta aje jakar hannunta gaban shi, nan ta zayyane mi shi duk abin da taji sun tattauna da kuma zuwanta gidan Khadija yanzu, cikin b'acin rai ya d'auki takalman shi ya tilk'awa Haseenah a baya gashi kam ba ta san da saukar takalman ba, ji ka ke timmm a bayan ta, k'ara ta saki ta dafe baya ganin ya d'auki d'aya takalman ya sa ta shura a guje d'aki, masifa ya dinga zazzagawa takaicin shi kud'in da ya kashe wajen amso mata magani, zagi ya dinga aika mata
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117