Skip to content

Chapter 82

Chapter 82

Kallon Kitse Book One Complete Hausa Novels 1,200 words 0 views Progress saved
Download Book

"Naji Hajia, amma wallahi da gaske na le idan ki ka bani zanyi aiki da su, Hajia ki duba kiga hakan zaifi a gani na, misali yanzu na wankan nan, idan da a waje na yake da haka ba za ta faru ba, amma idan ya na nan zai zamana kullum sai na yi wanka anan kenan, sannan idan na yi tafiya za'a dakatar da maganin kenan har sai na dawo, sannan Hajia..." "Dakata dallah." Ta katse shi tare da d'aga hannu, shiru ta yi ta jima ta na tunanin abin da ya fad'a kafin ta gamsu ta d'auko duka magungunan ta bashi, saida ya karb'a ta nuna mi shi yanda zaiyi aiki da su kafin ta sake jadadda mi shi bata so ko matar shi ta sani, alk'awari ya mata babu wanda zaiji dan haka ta bashi ya tafi, aljihu ya saka su ya fita daga gidan ya shiga harkokin gaban shi, sai yamma ya dawo gida cin abinci, zai shiga wanka ne ya fito da komai na aljihun shi ya na ajewa akan gaban madubi, ya na aje ledar maganin Haseenah ta kalle shi tace "Oga wannan fa na miye haka?" Ba tare da wani damuwa ba yace "Um, ba na fad'a mi ki zan karb'o wannan maganin ba a wajen Hajia? To ai sune na karb'o d'in, da k'yar ta bani su bayan na mata alk'awarin ba zan bari kowa ya sani ba." Ya na fad'a ya shige wanka, zaune ta yi tana kallon magungunan har ya fito, cikin taushin murya tace "To yanzu ya za ka yi da su kenan? Za ka ci gaba da sha ne?" Da k'arfi yace "Wa? Ni! Haba dai Hajia, kinga kawai d'auke su ma daga nan ki zuba su shara danni ko d'aya ba zanyi anfani da su ba." Mik'ewa ta yi da wani mirmushin mugunta a fuskar ta ta kalle shi tace "Haka na ke son ji dama, dan ba na son namiji mai tsirfa kamar mace." *Da dare* Usman da malam da kuma rakiyar Murtala da d'aya abokin nashi mijin Hajia Salamatu wato *Alhaji Salisu* suka je aka nemowa Nura auren sahibar shi *Choukra*, cikin girmamawa aka yi abin da za ayi aka gama kafin abin da zai biyo baya, ko da su ka dawo har gida suka fara aje malam in da ya umarci Usman da ya shigo su yi magana, suna shiga ya bashi ruwan addu'a yasha, ganin Nura a gidan ne ya sa yace ya je gida gobe da safe ya same shi kafin ya fita, da "To yah Fodio." Ya amsa kafin ya fito suka wuce. *Washe gari* da safe Hajia Sadija ce ta yi sallama gidan surukan Khadija in da Mansur ke binta a baya, tarba ta musamman suka samun daga wajen Hajia da malam d'in kafin su ka nutsu, cikin dattako Mama tace "Nasan za ku yi mamakin gani na da sanyin safiyar nan, to ba wani abu bane dama face wani alkairi da ya tunkaro mu, shine na ce ba za mu yi farin cikin mu kad'ai ba, kuma da kuma Usman d'in ku na da hakk'in ku san me ke faruwa." Malam ne yace "To gaskiya dai ba mu yi mamaki ba, abu d'aya da na ji shine fargaba, kuma bai wuce fargaban tunanin makomar auren yaran mu ba." Murmushi ta yi tace "Malam kenan, kamar yanda na fad'a ne a farko alkairi ne ke tafe damu, kuma insha Allahu babu abin da zai shafi makomar auren yaran nan, yanzun ma k'addara ce kawai ta gifta a tsakanin su, amma komai zai daidaita da yardar Allah." "Allah yasa haka Hajia." Cewar malam yayin da Hajia kuma tace "Allah ya yarda, ya kuma kawo mana k'arshen matsalar." "Ameen ya Rabbi." Mama ce ta d'ora da "Dama dai ba wani abu bane Bilal ne za'a wa k'ane ko k'anwa idan Allah ya amince." Da sauri duka suka kafe ta da ido kowa da mamaki, Mansur ma da kallo ya bita da mamaki, dan sam bai d'auka abin da zai kawosu ba kenan, amma ya zaiyi shiru ya yi ya na sauraren ikon Allah, Hajia ce tace "Wai Hajia ki na nufin Khadija juna biyu ne da ita?" Dariya mama ta yi tace "K'warai kuwa." Da tsantsar farin ciki tace "Kai Alhamdulillah, Allah abin godiya, Allah mun gode ma ka, gashi bayan shekaru goma sha uku za ka k'ara azurta baiwar ka da ni'imar ka wacce babu wanda ya isa ya bawa wani sai kai, baiwar da kud'i basa sayanta kuma alfarma bata bayar da ita." Malam da hak'oran shi ke waje ya na faffad'an murmushi ne yace "Tabbas hakane, arzik'i ne da imanin ka ko kafircin ka bai isa ya baka shi ba, sai mai bayarwa ya ga damar baka." "To wannan dai shine dama na ce bara mu zo mu fad'a mu ku, dan bai kamata ku kasa sani ba." Malam ne yace "Gaskiya ne Hajia, kuma mun gode da wannan girmama mu da ku ke yi, Allah ya saka da alkairi." "Ba komai wallahi." Mama ta fad'a ta na mik'ewa ta na gyara mayafin ta tana ci gaba da fad'in "Mu zamu wuce, dama zanje 'yar kasuwa ne na ce mu fara biyowa ta nan d'in." Mansur mik'ewa ya yi suka mu su sallama, har k'ofar gida malam ya rakaso in da ya sake jadadda ba su hak'uri akan abubuwan da suka faru, sannan yace a gaishe mi shi da su sosai, da haka su ka wuce shi ma ya dawo gida suka k'ara jinjina al'amarin, suna haka Nura ya sallamo d'akin tare da Aziza cikin shiri, har k'asa suka gaishe da iyayen su kafin Nura yace "Zan aje Aziza makaranta ne daga nan na biyo gidan yah Fodio, jiya yace na je gida na same shi." Malam ne yace "To shikenan Allah ya tsare, Allah ya mu ku albarka." "Ameen Baba." Su ka amsa suna mik'ewa, Hajia ma d'orawa ta yi da "Allah ya tsare, sai kun dawo." "Ameen Hajia." Cewar Aziza suna ficewa. Mansur na d'aukar hanya ya kalli Mama yace "Hajia ta, dama abin da ki ka zo fad'a mu su? Wallahi ko kad'an banyi tunanin haka ba." Ba tare da ta kalle shi ba tace "Kenan da ka sani da ba zaka kawo ni ba?" Dariya ya yi yace "Wane ni, ni d'in banza na kasa kai ku in da ku ke so." "Dan haka ka ja min bakin ka kayi shiru, in kuma ranka ya b'ace to rufe ni da duka." Ta fad'a ba alamar wasa, dariya ya sake yi shi dai yace "Allah ya huci ranku Hajia ta, ban fad'i haka dan b'ata ran ku ba wallahi, amma a gafarce ni." Shiru ta yi basu sake magana ba har ya kawo ta yar kasuwa wajen *Nasruminallah* ta fita ta lek'o tace "Zan d'auki lokaci anan, saboda akwai atamfofin da zan duba, idan ka na da aikin ke ka wuce kaje in da za ka." "To Hajia ta ame za ku koma kenan?" Kai tsaye tace "A adaidaita mana." Waro ido ya yi yace "Ah haba dai, Hajia ki na da mu a cikin garin nan mu barku ku hau adaidaita sahu, haba dai wuce nan ai wallahi, Hajia ta shiga kusha zaman ki, zan

Table of Contents

Chapters

117 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117