Chapter 34
Chapter 34
shegen kyau kafin ta zauna zaman jiran shi. Kamar yanda ya zamar masa jiki haka yau ma, ya na dawowa da matsananciyar yunwa kai tsaye falon Khadija ya nufa, da sallama d'auke a bakin shi, da gudu Bilal ya tare shi ya na fad'in "Sannu da zuwa Abba." Cike da rangaji ya d'an rumgume shi yace "Sannu yarima, ya ka ke?" Mik'ewa Khadija ta yi ta d'auko ruwa da kofi lokacin ya zauna in da ta tashi ya cire hular kan shi, durk'usawa ta yi gwiwarta d'aya a k'asa ta fara tsiyaya ma sa ruwan ta na fad'in "Ko ba ka fad'a ba alamun sun nuna a gajiye ka ke, sannan ka na tare da matsananciyar yunwa wacce ke neman jigata min kai, amma yanzu ka fara da ruwa ma su sanyi." Ta fad'a hakane lokacin da ta mik'o masa kofin ruwan. Da tattausan murmushi a fuskar shi ya karb'a ya kafa a baki, sai da ya shanye duka ruwan kafin ya sauke numfashi mai k'arfi ya mik'a mata ta karb'a, aje wa ta yi gefe ta janyo k'afar shi ta soma cire masa takalman sa k'afa ciki, zaunawa ta yi kusan shi ta na kallon shi, ido lumshe ya ke kallonta yace "Uwar gida na sarautar mata." Da wani tsadadden murmushi ta amsa da "Labbaika." Cike da kasala yace "Wanka na ke so na yi, amma kuma yunwa ba za ta barni ba, yanzu ki zab'a min wanda zai fara yi." Sai da ta d'an saci kallon Bilal da ya ke tsaye gaban telebijin ya na kallo sannan ta kalle shi tace "Ka k'arasa shiga mana wajen amaryarka, ita ce za ta zab'a ma ka, ko ka manta har yanzu kwananta ka ke?" Wata doguwar hamma ya yi kafin ya kalle ta yace "Wai ni ban tambaye ki ba ma, yaushe ne kwananki zai zo ne?" "Me ya sa ka tambaya?" Ta fad'a ta na shafa wuyanta, saida ya rufe ido yace "Ina so na san ranar da zan dawo hannunki ne kawai." Shiru ta yi ba tace komai ba shi kuma ya mik'e yace "Zan shiga ciki na yi wanka, amma ki tabbatar kun shigo akan lokaci dan mu ci abinci." Da kallo kawai ta bishi har ya shige ciki, takalman shi ta d'auka ta shiga da su d'akin ta, ya na shiga can ma wata tarairayar ya samu wajen Haseenah har sai da ya yi wanka ya canza kaya kafin su ka zo kan teburi, kallon ta ya yi yace "Ki saka hijab sai ki kirasu su zo mu ci abinci." D'an jim ta yi kafin ta zagayo kujerar shi ta zauna akan k'afar shi ta na shafa d'an gajeran gemunshi tace "Hubbi na, ban san ko tunanin da na yi zai gamsar da kai ba, amma ina fatan ba zai zama kuskure a gare ka ba, ka ga ni amarya ce, kuma kowace amarya ta na so taga ta more amarcinta babu takura da matsi, wallahi har zuciya ta ba na jin aunty Khadija da Bilal a matsayin takura a gareni, sai dai ina so na sati d'ayan nan mu dinga cin abinci tare da kai, amma kuma na san hakan ba zai yiwu ba saboda ka saba cin abinci da iyalinka, amma gaskiya idan ba ka min wannan alfarmar ba zai sa na ji kamar ba ka d'auke ni a matsayin..." Da sauri ya rufe mata baki yace "Wa ya fad'a mi ki ke ba iyali na bace? Ai tun ranar da aka d'aura mana aure mu ka zama iyali ni da ke, dan haka kar ki sake fad'in haka, yanzu ba dai maganar cin abinci tare bane?" Kai ta d'aga cike da shagwab'a alamar eh, d'orawa ya yi da "Angama da wannan buk'atar, sai kuma wata idan akwai, zan wa Ummyn Bilal magana za ta fahimta, sai dai yanzu ki zuba mu su na su abincin sai ki kai mu su, ko ya ki ka gani? Tun da ai ba sa zauna da yunwa ba." Shiru ta yi kamar za ta fashe da kuka ta kalle shi tace "Ban san me ya sa ba, amma dai da ido na naga Bilal ya kaiwa mai gadi abincin da na ba shi su ci, watak'ila bai mu su dad'i bane." Shiru ya d'anyi kafin ya kalle ta yace "Shikenan, zuba mana abincin." Zubwa ta yi amma kuma sam ta k'i yarda ta ci wai ita ta k'oshi, ba dan ran shi na so ba ya ci sai dan kar ta ji ba dad'i, amma har ga Allah abincin bai masa ba, domin kuwa yau ma dai shinkafa ce da jar miya, shi kuma bai fiya cin shinkafa ba da dare, sannan kuma ga ya ji da abincin ma ya yi, da k'yar ya d'an tuttura ba tare da ya nuna mata ba, su na kammalawa yace su je falon Khadija, cikin shagwab'a tace "Wanka fa zan shiga yanzu na yi shirin bacci." Murmushi ya mata yace "To a shirya da kyau kafin na dawo." Cikin kwarkwasa tace "To amma fa kar ka jima sosai, wallahi idan ka jima ni bacci na zanyi." Sai da ya janyota jikin shi yace "To ki ba ni minti talatin, ya isa?" Waro ido ta yi tace "Talatin? Ai na d'auka saida safe za ka musu, ashe wajen aunty Khadija za ka je ku sha soyayyar ku." Yanda ta yi maganar da shagwab'a ya sa shi darawa, rusunawa ya yi yace "To ki ban minti ashirin, hakan ya yi?" Turo baki ta yi tace "Gaskiya sai dai in ka amince da minti sha biyar, shi ma fa daurewa ne na yi wallahi, dan ban cika son yin nesa da kai ba." Haka kawai ya tsinci kansa da kasa yi mata musu, a cewar shi kam "Angama ranki shi dad'e." D'aki ta nufa shi kuma ya nufi falon, ya na shiga ya same su a d'akin Bilal ya yi shirin kwanciyar shi, amma da littafi a hannun shi na addu'o'i Khadija na karanta masa ya na maimaitawa, Bilal na ganin shi ya yi saurin daka tsalle ya mak'ale a wuyanshi, cike da zolaya Usman ya fad'a kan gadon ya na fad'in "Wai wai wai, wannan yaron me ka ci hakane da ka yi nauyi? Kaga ka na shirin karya ni." Tsaye Bilal ya yi ya d'aga rigar shi ya na shafa cikin sa yace "Sarauniya ta cika min ciki na da kayan dad'i." Tashi ya yi zaune ya na ma Khadija wani kallo yace "Me ki ka ba shi ya ci?" Bilal ta kalla tace "Ka tambaye shi mana ga ka gashi." Jayo Bilal ya yi ya kwantar da shi ya ja zanin rufa ya rufe shi, da kan shi ya tofa addu'a a hannu ya shafa mi shi kafin ya sumbaci kan shi yace "Yi baccinka yariman mahaifin shi, safe lafiya." Kallon shi Bilal ya yi ya sumbaci hannun shi yace "Saida safe Abba." Murmushi ya masa ya mik'e, zagayawa ya yi wajen da Khadija ke zaune ya kamo hannunta yace "Muje ko kema na shinfid'e ki." Da sauri Bilal ya juyo ya kalle shi yace "Abba, yau ma ba za ka kwanta tare da mu ba?" Dukansu ne su ka kafe shi da ido, cikin rashin kuzari yace "Zan kwanta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117