Skip to content

Chapter 31

Chapter 31

Kallon Kitse Book One Complete Hausa Novels 1,200 words 0 views Progress saved
Download Book

madafar, ganin Khadija tsaye ta na kallon Haseenah da ke rik'e da hannu ta na kuka ne ya sa Usman saurin k'arasawa, rik'o hannun Haseenahr ya yi yana kallon abin da ya zube ya kalli Khadija yace "Lafiya? Me ya faru ne?" Cikin tafasar zuci tace "Kallon me ka ke min? Ka tambaye ta mana, ni ce za ka tambaya?" Rabi'a ma matsawa ta yi kusan Haseenah tace "Haseenah me ya faru ne wai? K'onewa ki kai?" Girgiza kai ta yi cikin zubar da hawaye tace "A'a, ba k'onewa na yi ba." Usman ne ya d'ora da "To me ya faru?" Fashewa ta yi da wani kukan, hakan ya sa Usman mayar da kallon shi ga Khadija yace "Khadija me ya faru, naga ai daga ke sai ita ne a madafar ko? Me ki ka mata haka?" Kallon shi ta yi cikin ido da niyyar fad'in abin da ya faru, amma ta na kallon shi sai wannan kwarjinin da haiba da rashin sabo na rashin samun matsala da ba su tab'a yi ba ta yi k'asa da kan ta, cire gilashin ta tayi ta fashe da kukan da babu sauti, ai tuni sai hankalin Naseer ya tashi, da gaggawa ya matso kusanta shima ya kalli Haseenah yace "Wai me ya faru ne? Ke ki fad'a mana." Cikin kuka Haseenah ta kalli Naseer d'in tace "Ni ban san me ya faru ba, na dai san na yiwa mai aikin nan magana kan cewa kar ta sake shigowa madafar nan in ina aiki, banji shigowar aunty Khadija sai ji na yi ta tura ni gaba kawai, shi ne na..." Sai kumata fashe da kuka. Da tsantsar mamaki Khadija ta kalle ta, kallon ta Usman ya yi yace "Gaskiya ne abin da ya faru kenan?" Mayar da gilashin ta yi ta kalli Usman tace "Babu abin da zan fad'a ma ka, ka d'auki mataki kawai." Kallon Haseenah ta yi tace "Ba zan ce ki ji tsoron Allah ba, amma zan mi ki kashedi da kar ki sake kira na da makauniya, in ba haka ba kuma wallahi zan mugun sab'a mi ki fiye da tunanin ki." Juyawa ta yi ta kama hannun Bilal da na Naseer da nufin fita, k'yam Naseer ya tsaya ya kalli Haseenah yace "Kamar k'anwa na ke kallon ki, dan Allah kar ki bari wani abu na rashin kyautatawa ya shiga tsakanin ki da yer uwa ta, ita d'in kamar rayuwar mu ce, ban tab'a jin wanda ya yi k'ok'arin kiranta da makauniya sai yau, dan haka ki kiyaye dan Allah, ku zauna lafiya sai mijinku ya yi farin ciki da ku." Juyawa ya yi su ka fita, a daidai k'ofar shiga falon Khadijar su ka tsaya, dafa kan ta ya yi yace "Ki yi hak'uri kinji yar autar mu, ina tabbatar mi ki hakan ba zai sake faruwa ba, ki daina kuka kinji ko." Cikin shashek'ar kuka tace "Shikenan yaya na, kar ka damu na dain, ka tafi gida kawai, amma dan Allah kar ka bari kowa ya ji a gida, wannan matsalar gidan nan ce." "Shikenan zanyi, amma ki min alk'awarin hakan ba zai sake faruwa ba." "Nayi." Ta fad'a da murmushi, shafa kan Bilal ya yi yace "Yaro na sai anjima ko, yaushe za ka shigo wajen matar?" Ba walwala a tare da shi yace "Tonton (uncle) da Momy za ta yarda da na bika gida, gaba d'aya yanzu gidan nan ba dad'i, Abba ma ya daina cin abinci da mu kuma ba ya..." "Bilaaaal." Khadija ta kira sunanshi, wucewa kawai Naseer ya yi su ma suka koma ciki, d'akin Bial su ka nufa dan ta taimaka masa ya canza kaya Uwani ta yi sallama, juyowa ta yi ta kalle tace "Uwani ki je gida kawai, ki bari sai gobe ki dawo." "To aunty, amma Abban Bilal yace wai ki same shi a d'akin shi yanzu." Sai da ta d'an kawar da kai kafin tace "Shikenan, ina zuwa." Kallon Bilal ta yi tace "Ka je ka cire wannan kayan sai ka watsa ruwa ka canza wasu, ina zuwa yanzu ka ji." Ciki ya shiga ita kuma ta wuce d'akin Usman, a falon shi su ka ci karo da su Rabi'a za su tafiya, amma ko kallon ta Rabi'a ba ta yi ba saboda a tattaunarwa da su ka fara da Usman sai kare Khadijar ya ke, Jauza'u ce tace "Sai anjima aunty Khadija." "Ki gaida gida Jauza'u." Cewar ta ta na shiga d'akin, zaune ya ke akan kujera da ke gaban madubi in da Haseenah ke zaune bakin gado, ita ma bakin gadon ta zauna kamar yanda ya nuna mata, ya na kallon fuskokin su ya gyara zama yace "Baiwar Allah, a gaskiya yau d'in nan na ji kunyar abin da ya faru a gidan nan, sai da zuciyata ta wahala kafin na yarda Khadijata ce ta aika abin da ta aika ta, saboda ni dai nasan tawa Khadijar mai hak'uri ce da kawar da kai, amma ban san ya akayi wannan karan hak'urin ta ya gaza ba, ni da na ke mata fatan ta kai k'adamin da za ta dafa dutse har ma ta shanye romonsa, amma gashi shaid'an na san min yawo da hankalin ta wajen tilasta ta yin abin da bai dace ba, Khadija, ya haka? Ya akayi ki ka bari haka ta faru? Me ya tunzura ki haka?" Tabbas a kowane lokaci kalaman mijinta su na tasiri a kan ta fiye da yankan wuk'a, hakanne ma ya sa ta kalle shi a ladabce tace "Ka yi hak'uri Abban Bilal, ni ma sai yanzu na ke jin kunyar abin da na aikata, amma insha Allah hakan ba zai sake faruwa ba, wannan alk'awari ne." Sai da Usman ya lumshe ido saboda tsabar jin dad'i, ji ya yi kamar ya rumgumota jikin shi, sai dai a yanayin da ake ciki hakan bai kamata ba saboda tsaro, murmushi ya yi yace "Hakan ya yi kyau, Allah ya ba ki ikon cika alk'awarin nan da ki ka d'auka, kuma sai a ci gaba da kiyaye saboda gudun b'acin rana, wata rana ba'a san me zai faru ba a irin haka." "Insha Allahu za'a kiyaye." Ta sake fad'a a ladabce, mayar da kallon shi ya yi ga Haseenah yace "Ke kuma Haseenah, ba wai zan tambaye ki me ya faru ko kuma waye mai laifi ba, a'a, zan fad'a mi ki wani abu ne da na ke ganin ya kamata ace tun farko kin san shi kafin ki shigo gidan nan, Haseenah." Yanda ya kira sunan ta yasa ba ta da zab'in da ya wuce d'agowa tace "Na'am." D'orawa ya yi da "Khadija dai matata ce tsawon shekara goma sha uku, shekara sha uku ba kwana goma sha uku bane Haseenah, kinga kenan k'arshen sanin juna munyiwa kan mu shi ni da ita, a wannan shekarun da mu ka d'auka Haseenah, wallahi, wallahi na rantse mi ki da Allah ba zan iya tuna ranar da zan ce mi ki wannan baiwar Allahr ta min ko da kallon raini ne bare tsaki ko bak'ar magana, Haseenah, kin ganta nan ki tambaye ta kiji yanda auren mu ya kasance, amma sau d'aya ba ta tab'a nuna min k'iyayya ko tsana ba, idan har na ce eh, to eh ne

Table of Contents

Chapters

117 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117