Chapter 113
Chapter 113
guda biyu, a b'angaren Khadija kuma shiga kawai take ta na sakewa, duk da Usman ya musu d'inki iri d'aya kuma yawa d'aya amma saida kaltume da Hajia Turai suka sake mata wani d'inki, ita kanta ba ta sani ba sai ana gobe bikin kad'ai suka kawo mata su, yawan taron jama'a ya sa muryar Khadija dishewa ta shak'e ba'a ji saidai ta d'aga hannu kawai. B'angare d'aya kuma su Kaltume na sama suna gyara wajen da za'a gabatar da walimar dare wacce su ka shirya ma Usee, a haka har dare ya riske su lokacin mutane sun watse sai masu aiki da aka samu suna share gidan, nan fa aka sake sabon shiri in da Khadija ta sake d'aukar wata sabuwar kwalliya wacce ta ci kud'i sosai, Aisha da Humaira ma shiryasu akayi cikin kaya iri d'aya kuma kalar na iyayen su da Bilal, Haseenah da Khadija ma cikin wanda Usman ya d'inka mu su suka saka kala d'aya, nan suka kira Usman a waya wai ya zo gida ba lafiya, a gigice ya tambayi me ya faru? Sai kawai su ka kashe wayar suna dariya, Usman dama walima ya yi sosai shima haka ya tsallako abokan shi ya taho gidan a sukwane, d'akin shi ya nufa ya na shiga ya same su zaune sai hira suke, matsowa ya yi ya na fad'in "Lafiya? me ya faru ne?" Tare su ka taso Haseenah na cire mi shi hula Khadija kuma riga tace "Ba komai, wanka za ka yi ka yi sabuwar kwalliya." Duka da mamaki ya kalle su yace "Kwalliya kuma, kamar wata mace? Kwalliyar me?" Khadija ce ta d'ora mi shi hannu a yatsa tace "Shiiiii, ba magana." Iska ya furzar yace "Wallahi kun d'auki alhaki na, haka kawai kun tayar min da hankali." Kallon shi Khadija ta yi cike da shagwab'a tace "Ka yafe mana to." Turo baki ya yi gaba yace "Na k'i d'in." B'ata rai ta yi ta tisa k'eyar shi ta kalli Haseenah tace "Shiga da shi ciki ki wanke min shi tas, kafin ku fito zan fito mi shi da kaya." Ba musu suka shiga ban d'aki ta taya shi wanka, ita kuma kaya ta fito mi shi da su kalar na su sai dai ba iri d'aya ba, haka suka fito suka shirya shi kamar wani sarki ko kuma yaro, tsaf su ka yi da su kafin suka fito dan hallara wajen taron wanda a wannan lokacin ya samu halartar manyan bak'in da aka gayyata har daga mak'ota *nigeria* ma, Humaira na hannun Aishatu in da Aisha ke hannun Mariya, haka suka haura sama cikin shiga ta alfarma gwanin birgewa, sai lokacin Usman ya saki baki ya na kallon ikon Allah, tuni hankalin shi ya koma kan wani rubutu da akayi da manyan bak'i aka saka *HAPPY BIRHTDAY GARKUWAR MU*, sunkuyawa ya yi wajen Khadija yace "Aikin ki ne ko?" Ita ma matso da kanta ta yi tace "Ba ruwa na ni, nima gani kawai na yi." Tun kafin su isa wajen zamansu Khadija ta hango manyan bak'in da ta gayyata, nima dai baza ido na yi sosai saboda ganin wurin ya cika da mazan hajiyoyi sosai, mamaki ne ya kamani ganin wasu manyan mutane a gefe, haba ai saina bar bin bayan su Khadija na tafi da sauri wani tebur, domin tabbatarwa kaina da gaskiyar abin da na ke gani yasa na k'arasa na tsaya na ce " *Kaussar*." (jarumar littafin *Kaussar*). Ai kam da sauri ta juyo ta kalle ni, da farin ciki ta mik'e tsaye ta rumgume ni tace "Aunty Meera, ke ce? Me kika zo yi anan?" Kafin na yi magana daga bayan Kaussar aka ce "Me fa ta zo yi daya wuce d'aukar shegen rahoton nan nata da ta saba yi na jaraba, ko gajiya ba ta yi ta na bi gida-gida ta na wa ma'aurata bin k'wak'waffi." Wa zan gani in ba *Ahmad* ba, k'ara waro ido na yi saboda ganin ya k'ara k'iba, sai dai ya k'ara haske sosai abinka ga jan buzu kuma balarabe, sai uban k'asumbar nan sai walk'iya take bak'i k'irin, tab'e baki na yi na dalla mi shi harara na ce "Can ta matse ma ka dai, kuma in da ba na d'auko labarin ai da ban d'auko na ku ba." Shima cikin hararan ta yace "To kin d'auka gata ne ki ka mana, bayan kin gama kalle min mata." Sama da k'asa na harare shi na ce "Ikon Allah." Kallon Kaussar na yi na ce "Wai yaushe bagwarin mijin nan naki ma ya iya haussa ne haka?" Dariya Kaussar ta yi ta koma ta zauna kafin tace wani abu yace "Ranar da ki ka zaunar da ni ki ka koya min." Nuna shi na yi da hannu na ce "Allah ka kiyaye ni ko na sa a k'wace matar ta ka sannan ka koma inda ka fito." Dariya ya yi wacce ta k'ara bayyanar da tsantsar kyawun shi yace "Bismillah idan kin isa, ke ki na ganin kin isa ki datse wannan auren? To yanzu haka yaro ta baro gida wanda take bawa nono, kinga kuwa ni da ita ba rabuwa sai mutuwa." Sama da k'asa na sake hararan shi na yi gaba ina kallon Kaussar na ce "Za mu yi magana idan mijin nan na ki ya yi bacci." Da dariya ya bini da kallo ya na fad'in "Sakaran ina ne ni zanyi bacci a wannan taron, bayan akwai irin su *Najib* (jarumin littafin *D'aukar fansa*)a wurin nan." Da sauri Kaussar ta rufe mi shi baki saboda su na kusa da su Najib, ni kuma sake ware ido na yi dan naga ina ya ke, ai kam baifi tako hud'u ba na iso ga teburin shi, kallon shi na ke sosai tare da kyawawan matan da su ka saka shi tsakiya su biyu, da murmushi a fuska na ce "Alhaji Najib barka da dare." Wani mummunan fad'uwa gaba na ya yi saboda kallon da ya watso min kamar kumurci, d'auke kan shi ya yi k'ala baice min ba dan haka na kalli *zarah* na ce "My Zarah sannu ko?" Da murmushi sosai tace "Sannu aunty Meera, ya ki ke? Me ki ke anan? Ke ma aunty Khadija ta gayyace ki ne?" "Eh...t..." Ban k'arasa ba Najib yace "Har sai kin tambaye ta me ta ke anan? Gulma mana ta kawo ta, ko kin manta anyi drima a gidan Usee watannin baya da su ka wuce?" Murmushi kawai Zarah ta yi sai *Yasmine* da tace "Ko da gulma ce ta kawo ta ai kam ta yi anfani, dan nasan akwai dayawa masu irin halin Haseenah wanda za su gyara." Kashe mata ido na yi na ce "Da kyau tawaje na kin gane, ba zan tsaya b'ata lokaci da wannan mijin na ku ba mai k'aton ciki kamar kun aza mi shi randa." Da k'arfi ya juyo zaiyi magana Zarah ta rik'e tace "Haba beby ya isa mana, rabu da ita dan Allah." K'wafa ya yi ya zauna ya na huci, ni kam ko a jiki na sai ma gaba da na yi na bar shi da masifar shi, kamar daga sama na ji na yi karo da k'afar wani, da sauri naja baya ina fad'in "Ayyah sannu ko, yi hak'uri
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117