Skip to content

Chapter 114

Chapter 114

Kallon Kitse Book One Complete Hausa Novels 1,197 words 0 views Progress saved
Download Book

dan Allah ban..." Bai k'arasa ba saboda ganin *Saif* (jarumin littafin *Ba so bane*) sai dokan uban murmushi yake ya na kallo na, ajiyar zuciya na sauke dan nasan ba matsala, da dai sauran mazan hajjajan ne da ban san me zai faru ba, kafin ya yi magana *Zeinab* tace "Lah aunty Meera ke ce? Me ki ke anan?" Izuwa yanzu kam na fara gajiya wannan tambayar da kowa ke min ta me ya kawo ni, amma sai na dake na ce "Ni ma na zo bikin Khadija ne." Da wannan murmushi Saif yace "Ko kuma suma idon ki ka saka mu su ba kamar yanda ki ke wa kowa." Kallon shi na yi na ce "Haba Saif ya za ka ce haka, kaine fa na ke gani mai hankali a cikin sauran." Waro ido ya yi yace "Au! Wai ki na nufin sauran duk mahaukata ne?" Kau da kai na yi na ce "Ka ga ni dai bance ba kar ka ja min sharri." Juyawa ya yi bayan shi yace " Bara na ga ina zanga aboki na na fad'a mi shi kin ce mahaukata ne su." Da sauri na bar wajen ina fad'in "Shi ma dai ya lalace kamar sauran, nasan kuma ba zai rasa nasaba da wannan bigaggen *Salman* (jarumin littafin *Auren had'i*) d'..." Ai dole naja birki domin kuwa karo na yi da Salman d'in, wani kallo ya min yace "Ni ne ma bigaggen?" Murmushin dole na yi na ce "Ah haba dai, ni na isa na kira ka da bigagge, dama da Saif na ke." Dafe k'irji ya yi yace "Abokin nawa ne bigagge kenan?" Zanyi magana naji andafa ni ta baya ance "Aunty Meranmu dan Allah rabu da su, wahalar da ke kawai za su yi." Baki na.saki saboda ganin *Ummi* ta zama wata babba kuma hamshak'iyar mace, kallon Salman na yi a raina ina raya koya yake ya na iya d'aukar ta ma yanzu? Hum, kallon ta na yi na ce "Ummi na ina 'yan biyu?" Da murmushi a fuskarta tace "Yan biyu su na wajen su lamama, amma ya na gan ki anan? Me ki ke yi?" Salman ne ya juya ya zauna kan kujerar da suka tashi ya na fad'in "Me fa zai kawota da ya wuce d'aukar rahoton da ta saba, ta na nan kullum ta k'i canzawa sai tsukewa take, Allah ya sa wayar taki ta fad'i sai mu ga ta tsiya." Wata dariyar rainin hankali na mi shi na ce "Ka ji malam Salmanu, wato so ka ke na zuma b'ukekiya kamar matar ka, to ni mijina ba ya buk'atar na yi k'iba haka yake son gani na, sannan da ka ke fatan wayata ta fad'i to in fad'a ma ka ta na fad'uwa wallahi sai ka biya ni, in kuma ba haka ba zansa Ummi ta ma bore har sai an sake ma ka tiyata, ai dai ka gane tiyatar da na ke nufi ko?" Ta fad'a ta na kashe mi shi ido d'aya, baki ya saki ya na kallo na har na wuce na bar shi, saida na b'acewa ganin shi ya kalli Ummi yace "Kuma ke sai kiyi idan ta saki?" Cike da tabbatarwa tace "Sosai kuwa, me zai hana ni?" Gyad'a kai kawai ya yi ya cije leb'en k'asa, har na wuce na yi saurin dawowa baya cike da tsoro, murza ido na yi ina so na ga wai tabbas shine wanda na ke zato ko kuma dai gizo ne, da mamaki na ce " *Abbas* (jarumin littafin *Sanin masoyi*), ai kam da sauri ya juyo, amma abun mamaki ya na gani na saiya had'e rai ya sake juya min baya, har zan shiga tunanin dalilin da ya sa ya min haka sai kawai na ji andafa ni, juyowa na yi sai kuwa na ga takwarata, cike da farin ciki mu ka rumgume juna ta na fad'in "Takwarata me ki ke anan?" Raba jikina na yi da nata na sake kallonta ta yi kyau sosai, murmushi na yi na ce "Na zo biki ne ni ma." Tsaki naji Abbas yaja hakan ya sa mu ka kalle shi a tare, *Sameera* ce tace "Jarumi na lafiya ka ke tsaki?" Da k'yar yake maganar saboda miskilanci yace "Kinsan ba na son hayaniya, wannan kuma ta tsaya min a kai ta na zuba kamar 'ya'yan kurna." Tabbas raina ya b'ace yanda Abbas ya nuna ni kamar ya nuna kashi, tab'e baki na yi na ce "Da ace banga lokacin da ka ke wa takwarata 'yar murya ba da sai ka zare min ido, amma tunda har na ga komai to magana ta k'are, wannan shan kunun duk birga ce wallahi." Kallon Sameera na yi na ce "Takwara idan kun koma gida lafiya ki gaishe min da su Bashir da su Abba da Mama." Da murmushi a fuskar ta tace "Za su ji aunty Meera." Har zan wuce na ji Abbas yace "Ta na nan har yanzu yanda take kamar za ta fad'i ta na fama da bibiyar rayuwar mutane." Wucewa na yi na barshi da takwarata tace mi shi "Ba fa na son haka uban yara, duk abin da za ka fad'a mata kamar ni ka ke fad'awa." Wani kallo kawai ya bita da shi kamar zaiyi bacci, ni kam ina barin nan na shiga neman mutuniya ta, ai kam bansha wahalar ganin ta ba, da gudu na k'arasa na rumgumeta ta baya ina fad'in "Ohhh, my Hajiata." D'ago kai ta yi ta kalle ni tace "Lah! aunty Meera, ke ce anan? Me ki ka zo yi wurin nan?" Saida na taushe zuciya ta kafin na ce wani abu *Umar Faruk* (jarumin littafin *Jihadi*) ya fizgoni na yi baya ya na fad'in " Dallah malam sake ta, me ye haka kin wani zo sai kin karya ta." Ba dan Umar ne ba da sai na mi shi rashin mutumci, amma saina k'yale na ce "To cinye ta zanyi da ka wani taso min haka?" A tsaurare yace "Ki yi baya ki daina tab'a jikin matata shine kawai abin da na sani." Rik'e hab'a na yi na ce "Ikon Allah, beby mijin beby, wato wai kai mai kishi ko? To Allah ya kyauta." "Ya ma kyauta." Ya fad'a ya na kallo na, *Khairat* na kalla na ce "Hajiata ina *Zubaida* ne? kinsan fa fan's sunyi kewarta." Murmushi ta yi tace "Ta na gida bata jin dad'i ne, kuma ga tsohon ciki da ke jikinta, shi ya sa ta zauna gida tunda tafiya ce mai nisa." Juyawa na yi na kalli Umar ina dariya, shi kam sai ya had'e rai ya na harare na, saida na fara takawa na ce "Lallai Umar ba dama, wato har yanzu ka na nan ka na tsula tsiyarka, daga wannan ta sauke wannan za ta d'auka, humm." Juyawa na yi zan wa Khairat magana amma sai Umar ya ciro takalman shi zai jefe ni, da gudu na bar wajen ina dariyar mugunta, kujera na samu na zauna ina sauke numfashi kamar saukar aradu daga gefena aka ce "Aunty Meera ya ki ke?" Da murmushi na juyo dan na gane mai muryar, da farin ciki na d'aga mu su hannu na ce " *Falmata* (d'aya daga jaruman littafin *Itace k'addarar mu*), lafiya lau, ya

Table of Contents

Chapters

117 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117