Chapter 21
Chapter 21
su zo kafin rana mutane su zo, tun da ba ta da yer uwa mace da za ta iya zuwa kafin zuwan mutane. *Yau* ma haka aka yi shagalin damu aka gama, da dare kuma Rahama matar Ashir da *Aisha* matar Bashir su ka mata kwalliya kafin su ka bar gidan, har *11* dare ba Usman ba labarin shi, sai kawai bacci ya suri Khadija ba tare da ta shirya masa ba, ta na nan har sai da ya shigo, yanda ya same ta saita bashi tausayi, mayafin jikin ta ya fara cire mata a hankali kafin ya cire mata takalmin k'afar ta, a hankali ya tallabo k'afafun da nufin d'ora su akan gadon sai ta farka, da k'arfi taja baya ta had'e da gadon har tana neman fad'uwa, yanda ta ke kallonshi a tsora ce ya sa yace "Khadija, tsoro ki ke ji?" Girgiza kai ta yi alamar a'a, tab'e baki ya yi yace "Shikenan, ki tashi ki cire kayan jikin ki sai ki zo ki kwanta." Ganin ya juya zai fita ya sa tace "Kai fa?" Juyowa ya yi yace "Ni fa me?" "Ina nufin ina za ka kwanta kai?" Murmushin mugunta ya saki ya kalli gefen ta yace "Anan mana, ko ki na so na sake kwana a falo ne?" Shiru ta yi ba za iya cewa eh ba, saboda kar ya ji ba dad'i, kayan bacci ya d'auka ya fita falo dan canzawa, ita kuma k'in sauya kayan ta yi har ya sake samunta a haka, kashe wutar d'akin ya yi ya kwanta gefe ya na satar kallon ta, ba ta kwanta ba sai ma k'ara rakub'ewa da ta ke, kallonta ya yi yace "Ki kwanta Khadija, daga ni sai ke ne fa a gidan nan, kuma a cikin d'akin da babu wanda zai iya taimakonki, idan na so ai zan iya yin komai a d'an k'ank'anin lokaci, amma ba yanzu ba kinji, ki kwanta ki yi bacci kawai." Ya na fad'a ya juya mata baya ya na ci gaba da murmushin gefen labb'a, bacci ne kad'ai ya fizgi Khadija yasa ta kwanta ba tare da ta sani ba, sai dai baccin bai je ko ina ba Usmn ya tashe ta yin sallah. Ko da ta yi sallah ya fita a runfar nan ta samu akwai kayan abinci sosai, sassauk'an girki ta yi har ta gama bai shigo ba, akan teburi ta aje ta shiga wanka, ta na fitowa yau ma kamar jiya zaune ta same shi, d'aki ta wuce ta shirya cikin riga da siket na shadda sun mata kyau, ta gama shafe jikinta da turare za ta fito Usman ya shigo, cak ta tsaya dan ya tare k'ofar fitar, k'asa take kallo shi kuma ya na kallon fuskarta, kamar daga sama ta ji yace "Ki je ki yi kwalliya, ko da ba kya ra'ayinta ni ina so." Galala ta bishi da kallo kafin ta zauna gaban madubi, da k'yar ta iya shafa hoda (powder) da d'an jan baki ta tashi ta bar d'akin, ta na zaune akan kujera taga fitowar shi, da sauri ta mik'e ta fara zuba abincin a k'aramin farantin da zai wadaci mutum d'aya, zan kujera ya yi ya zauna ya na kallon ta har ta gama zuba mi shi, wani farantin ta d'auka za ta zubawa kan ta yace "Ba buk'atar ki zuba na ki, mu fara cinye wannan." Ta gilashi ta d'aga manyan idon ta ta kalle shi ta buntsuro faffad'an labb'an ta, zaunawa ta yi ta d'auko cokali za ta saka yace "Na fad'a mi ki ai, ba na cin abinci da cokali, zan so ki saba da hakan, dan ci da hannu ma sunna ce." Mayarwa ta yi ta aje ta na kallon k'asa, hannu ya sa ya fara ci tare da bismillah ya kalle ta yace "Sa hannun ki mana." Kamar wacce zai cinye haka ta saka hannu ta na tsakuro abincin tana sakawa a baki, ganin haka ya sa yace "Ki na so sai na baki da kai na kenan?" "A'a." Ta fad'a da sauri ta na kai wata lomar bakin ta, d'an gyaran murya ya yi ya cire hannun shi ya na kallon ta yace "Nana Khadijatul Kubra." Kallon shi ta yi jin wani cikakken suna da ya kira ta da shi, a hankali tace "Na'am." Cikin nutsuwa yace "Kinga wani ikon Allah ko? Auren mu za mu iya kiran shi a bagtatan, domin kuwa babu wanda ya tsammani hakan daga mu har iyayen mu, amma Allah ya sa mun zama miji da mata sanadiyar had'arin da ku ka samu ke da mahaifi na, zan iya kiran haka da k'arfin da ke cikin rubutun *alk'alamin k'addara*, Khadija, tunanin hakan kad'ai ya isa ya samu mu rumgumi wannan k'addarar, dan ina da tabbacin wani babban al'amari zai faru tsakanin mu, sannan iyayen mu sun bimu da addu'ar mu da fatan alkairi, da wannan na ke rok'on ki da ki kwantar da hankali mu yi zaman aure, ina so mu yi zaman da iyayen mu za su yi farin ciki da mu, idan mu ka yi haka insha Allah Allah ba zai barmu mu wulak'anta ba, sannan maganar karatunki wannan ba matsala bane, za ki ci gaba insha Allah, sai dai kamar yanda ki ka sani ni ba mazauni bane, ba lallai na dinga sati d'aya ko biyu a cikin gidan nan ba." Cikin ladabi tace "Na yarda na yi auren nan saboda yan uwa na, dan haka zaman ba zai gagare ni ba insha Allah." "Alhamdulillah, hakan ya yi kyau, Allah ya bamu zaman lafiya, Allah ya azurtamu da zuri'a ta gari." Da sauri ta kalle shi wanda shi ma ita ya ke kallo, da azama ta sauke nata idon ta na murmushi, shi ma murmushin ya yi ya lek'a fuskarta yace "Ya dai Hajia, ko ki na mamaki ne?" Girgiza kai kawai ta yi, loma ya yanko ya nufi bakinta da fad'in "Maza bud'a bakin." Amsa ta yi cike da kunya kafin yace "Wai ni ne ba'a lele kenan?" Kallon shi ta yi cikin rashin fahimtar maganar shi, d'orawa ya yi da "Eh mana, har yanzu ke ba ki saka min a baki ba, ko kunya ta ki ke ji?" Ai kuwa kunyar ce ta rufe ta ta mik'e da sauri za ta bar wajen ya rik'o hannunta, ba tare da ta juyo ba yace "Zo zauna to na hak'ura." Janyo hannunta ya yi bai direta ko ina ba sai a kan cinyarshi, wani numfashi ta saune ta rufe idon ta ruf ta kasa ko numfashi bare motsi, shi kan shi wani sabon al'amari ne ya ziyarce shi, amma sai ya share saboda ya na so ta saki jiki da shi, dan ya lura har yarinta ma na damunta, cikin zolaya yace "Kinga ki bud'a idon nan, ko kuma dai..." Shiru ya yi ya juya bayan ta ya saka bakinshi a zip d'in rigarta ya jashi k'asa, jin ya na zame mata zip ya sa tayi wni dogon numfashi ta bud'a ido, ta so ta d'aga daga jikinshi sai ya k'i bata dama, jin ya na ci gaba da zame shi ita kuma a ganinta abun kunya ne ya ga rigar nonon da take sakawa sai kawai ta fashe da kuka, jin yanda ta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117