Chapter 59
Chapter 59
Ta kama duka nonuwan ta a hannu, "Sai kuma wannan." Ta k'arashe da nuna k'asan ta da yatsa sannan tace "Su kad'ai ne su ka mallaka min zuciyar Usman a hannu na, tabbas sihiri zai iya anfani a kan shi ta hanyar saka shi ya ci zarafi na, amma idan ki ka ce ya rufe idon shi sannan ya saurari zuciyar shi, to ko shakka ba na yi cewa sunan *Khadija* ne za ki ji ya fito a bakin shi." Hannu tasa ta ciro gilashin ta ta bushe shi da baki kafin ta mayar ta kalle su Hassana da Husseina tace " *Ku daina wa kitse kallon rogo* idan ku ka aika shi baki zai fahimtar da ku asalin me ye shi." Juyawa ta yi ta fice abinta ta na jujjuya k'ugu cikin k'arewa tafiyar da sai oga ake wa ita amma yau sun saka ta gwada mu su, har saida ta b'acewa ganin su Hassana ta sa k'afa ta ture kwanon tace "Kar wanda ya ci abincin, dan ba mu san me ta saka ba." Husseina ce tace "Kinji shegiya, wai so take ta nuna babu abin da take, to ai ko da ki ka ganmu da hak'oran mu talatin ki ka gan mu, dan haka sai ki fad'awa kaji amma zabbi hira suke." D'akin Haseenah suka shiga in da suka duba lungu da sak'o ba su ga wani abu ba, layar da mahaifin ta ya bayar Mariya ta taka kujera ta jefata bayan ma'ajiyar kaya (drower) ta kalli Haseenah tace "Ko da kin canza zaman kayan d'akin kar ki jefar da abin can ki sake mayar da shi, Baba ne yace a aje na tsari ne." K'ala ba tace ba har Mariya ta sake d'aga katifar fa a b'angaren hannun dama ta aje wata layar tace "Duk halin da ake ciki kar ki sake ki aza kan ki ba b'angaren da layar nan take ba, kinji ko?" Da kai kawai ta nuna ta ji, har suka gama aiki su na hira akan Khadija da abin da ya faru, haka suka gama ko sanin tafiyar su Khadija ba ta yi ba, Haseenah na ganin tafiyar su ta d'auke dula layoyin ta nasa su cikin shara, ana haka yamma ta yi ta karb'i girkin ta a hannun Khadija, yau ma saida ta kammala girkin ta d'auki d'an banza gishiri ta zuba ciki, ta gama shiryawa tsaf ta aje komai a muhallin shi. Kamar jiya yau ma ba su iya cin abincin ba, haka su ka yi 'yan dubaru kowa ya bar wajen, sai dai ran Usman ya b'ace sosai, hakan ne ya sa lokacin da ya shiga yi mu su saida safe, Haseenah kuma da ke son sanin me zai faru ya sa ta biyo bayan shi, ya na shiga d'akin ta tsaya bakin k'ofa ta na sauraren su, ya samu Khadija d'akin ta kwance, fuska ba fara'a yace "Dan Allah zan rok'i alfarma a wajen ki." Tashi ta yi zaune ta d'auki gilashin ta ta saka kafin tace "Alfarma kuma Abban Bilal, sanin kan ka ne kafi k'arfin kowace irin alfarma a waje na, fad'i kan ka tsaye insha Allahu zan ma ka idan da hali." Saiwa ya gyara tsayuwa yace "Ba na son sake jin wani abu a cikin abinci idan 'yer uwar ki ta dafa, tunda na lura abun akwai almubazzaranci a ciki, kar fa ki manta kud'i na ke sawa ina siyo abincin nan, kar ku ganshi a zube kamar kayan banza dan an zube mu ku na shekara, ba ku tunanin akwai wanda na safe ma sai sun nemo? To ba na so daga yau, kar a sake kinji na fad'a mi ki." Juyawa ya yi da fad'in "Saida safe." Da gudu Haseenah ta juya ta koma d'akin ta ta kwanta ta na haki, ya na fita Khadija ma shiru ta yi ta na tunani kafin daga bisani zuciyar ta ta hasko mata mafita ita ma, murmushi ta yi ta kwanta abinta bayan ta sake shafe jikinta da addu'a. Da safe ma haka Haseenah ta gama shirya abin kari sai dai a k'urarren lokaci, hakan ne ya janyo ta manta ba ta zuba komai a abincin ba, ba dan ta ji abinda ya fad'a ba sai dan ta manta, ta gama shiri za ta fito ya shigo d'akin cikin tsadaddiyar shadda bla (bleue) sai k'amshi ya ke, rumgume ta ya yi ya sumbace ta kafin ya d'ago ta daga jikin shi, hannu ya sa aljihu ya kamo hannun ta ya d'ora mata wani matashin akwati na sark'a, da mamaki ta ke kallon abun har ta bud'a, da kan shi ya d'auki sark'ar ya mak'ala mata a wuya, sannan ya cire mata yan kunnan da ta saka ya saka mata na sark'ar, hannu ta sa ta shafa tace "Kai, amma na ji dad'i sosai da kyautar nan, nagode." Ta fad'a ta na kallon shi, murmushi ya yi yace "Ba komai bane wannan, irin faranta min da ki ke ai kin wuce karb'ar sark'ar zinare." Zaro ido ta yi dan sai yanzu tasan sark'ar dake wuyanta, murna fa ba'a magana wajen Haseenah ta dangwala sark'ar zinare a wuya, haka su ka fito ta na karairaya kamar ta karye, da kan ta ta zuba mu su abincin dan tuni Bilal ya na islamiyya, Khadija da ta fahimci takunta kamar dariya ma ta bata, dan ga dukkan alama yau ta fara saka sark'a mai tsada, tab'e baki ta yi a ran ta tace "Da alama ba ki san sark'a mai tsada ba ko a ido, dan da kin sani da yanzu kin kashe kan ki da ganin kusan kullum sune a wuya na." Lafiya lau suka ci abinci su ka kammala, saida ya mik'e zai fita ya kalli Khadija yace "Nagode da alfarmar da ki ka min, sannan ki min message d'in abubuwan da ku ke buk'ata, anjima zan turo Bilyamin ya kawo mu ku." Ita kam dariya ma ya bata dan haka ta mi shi wani murmushi mai shiga rai tace "Angama ranka shi dad'e." Ya na fita ta mik'e zata koma d'akin ta, kallon Haseenah ta yi ta na murmushi tace "Sai kuma gashi yau gishiri bai shiga abincinki ba, ko ya akayi haka ta faru oho?" Kafin ta yi magana ta shige ta barta nan, ta na shiga falon ta ta tura mi shi sak'on abubuwan da suka kusan k'arewa da wanda ma suka k'are, lokacin har Haseenah ta shiga girkin rana aka kawo kayan, Usman ma gida ya dawo cin abinci dan har ga Allah ba ya so ana kai mi shi abinci waje in dai girkin Haseenah, dan ya gama fahimta tafi k'warewa wajen iya dafa shinkafa da jar miya, yamma na yi kuma Khadija ta karb'i girki, ita ma saida ta gama girkin ta lafiyayye sai kawai ta d'auki sukari (sugar) ta zuba a ciki, tsaf ta kawo shi ta jera kamar abun k'warai, sai dai yau a shirye take duk wacce za ayi ayi a gidan, dan ta lura Haseenah ba zaman lafiya take nema da ita ba. Zaune suke wajen cin abinci Khadija na zuba ma kowa abincin, k'amshin abincin ne ya sa Usman had'iyar yawu har ya riga kowa kaiwa a baki, rufe ido ya yi ya tauna ya kuma
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117