Chapter 6
Chapter 6
kuma ta na zuwa gida ta samu wannan kayan arzik'i, gidan su ta kira ta fad'a mu su, zuwa bayan sallah magrib kam sai ga maman ta da matan yayyun ta sun zo ganin kayan, hotunan su ta d'auka ta turawa k'awayen ta dan su gani suma ba sai sun zo ba, anan ne ma har su ka yi magana da maman ta a kan kayan d'aki da za ta canza, mahaifiyar da kan ta ta d'auki alhakin yi mata odar su daga k'asar waje, dan itama ta na so ta kece raini. Sun fito dan tafiya Usmane ya shigo gidan, da gudu Bilal ya k'arasa ya rumgume shi, har k'asa ya duk'a ya gaishe da mama, mama ce tace "Kai yanzu da girman ka har ka ke wani mak'ale shi kamar yaro." Hararan wasa Bilal ya aika mata yace "Kaji tsohuwar nan, ke ma fa idan na je gidan ki har d'auka ta ki ke." Dafe k'irji ta yi tace "Kaji min sarkin sharri, ni kuma ina zan iya d'aukar ka? Ka fad'i abin da hankali zai d'auka mana." "To ai dai Abba na ne ko." Ya fad'a ya na k'ara sarkafe wuyan Usman da har yanzu ke durk'ushe, ita ma kuma cewa ta yi "Ni ma kuma d'ana ne ba, kaga kuwa ba zan bari nima ka karya min yaro ba." A hankali Usman ya kalli Bilal ya d'an janye shi daga jikin shi yace "Mama ta fika gaskiya, kowace uwa d'an ta ta sani, dan haka kowa ya je wajen maman sa, kai ma jeka ga ta ka can." Kallon shi Bilal ya yi yace "Lallai ma Abba, za ka nemi ne ai har in da na ke, kafi kowa sanin cewa ni ne bugun zuciyar ka." Wajen Khadija ya nufa ta d'auke shi saboda k'arfin hali duk da girman shi, mama kuma kallon Usman ta yi ta k'ara da "Mun ga kaya fa, a gaskiya sunyi sosai, sai dai kuma kayan kamar sunyi yawa, Allah ya k'ara bud'i na alkairi." Ba tare da ya d'ago ba yace "Ameen ameen Hajia, ai ni ne da godiya, Allah ya saka da alkairi, Allah ya k'ara girma da lafiya." "Ameen ameen." Mama ta amsa kafin Khadija ta d'ora da "Tofa, yanzu za ka fara godiyar ko?" D'ago kai ya yi ya kalle ta yace "Ke kuma ba kya so ina godiyar ko?" Hannaye ta d'aga tace "Allah ba ka hak'uri, ga ka ga su." Mama kam wucewa su ka yi suna fad'in "Sai da safen ku." Bilal da ke bayan Khadija ne ya d'aga musu hannu yace "Sauka lafiya, ko k'ofa ba zan raka ki ba bare ki sa ran samun na adaidaita." Usman ne ya juyo ya kalle shi yace "Haihuwa maganin takaicin duniya, sai da ta haife ni kafin kai ma ka zo, dan haka da kai na zanyi dakon mahaifiyar ta har makwancin ta." Dariya kawai su ke har su ka isa k'ofar gidan, cikin shagwab'a Khadija tace "Amma fa kar ku jima, ku yi sauri ku dawo." Kafad'a ya mak'ale yace "Na k'i d'in." Hararan shi ta yi tace "Za ka dawo ai ka same ni, zan kama ka a hannu." Ba tare da ya bari mama ta gani ba ya mata gwalo yace "Ki kama ni d'in, ba zan shigo ba sai kinyi bacci." "Bayan na rufe gida na ba." Ta fad'a kamar mai son tabbatar masa da za ta iya, haka dai ya d'auke su su ka wuce, mama ta so ya yi zaman shi su k'arasa titi su hau adaidaita, dan dama ko da *Naseer* ya kawo su sun fad'a mi shi za su koma da kansu, amma bai bari ba sai da ya kai su har k'ofar gida ya dire su, nan ma sai da ya fito daga motar ya sake mu su sallama kafin ya yi gaba, ya na kan hanyar shi kuma kiran amarya Haseenah ya shigo wayar shi, kashe kiran ya yi sannan ya sake kira da kan shi, ta na d'auka cikin ladabi tace "Amincin Allah ya tabbata a gare ka adali na." Cikin jin dad'i yace "Kema haka, ya amarya ta take?" Cikin siririyar murya tace "Da dad'i ba dad'i, amma daga yanda na ji karsashin muryar ka sai ya sa na ji wata tabbatacciyar lafiya na shiga jiki na." Murmushin jin dad'i ya yi yace "Allah na gode ma ka da ka sa Haseenah za ta zama tawa, kalaman ki su na fasa min kai na, shi ya sa ba na gajiya da sauraron ki, yanzu fad'a min, ko zan iya sanin in da amarya ta take? Dan ina jin hayaniyar ababen hawa a in da ki ke." "Wallahi Abban Bilal mu na wajen mai d'inki ne, amma yanzu za mu koma gida." "To in dai hakane ki ce kawai na zo na mayar da ku gida?" "A'a, ba na so na shiga lokacin aunty na gaskiya, kawai ka bar shi zamu koma da kan mu." Dariya ya yi yace "Allah sarki Haseenah baiwar Allah, a gaskiya ki na birge ni sosai ta yanda ba kya so a takura yer uwar ki, amma duk da haka ki bari zan zo na kai ku gida, dan dama ban shiga gida ba." Cikin murmushi tace "Yanda ka ce haka za ayi ranka shi dad'e." "Ina nan k'arasowa nan da d'an lokaci da zaran kin fad'a min in da ku ke." Tsaf ta kwatanta mi shi in da su ke, sai da ya wuce gidan shi kafin ya d'auki hanya zuwa in da su Haseenah su ke, hak'ik'a har zuciyar shi ya na jin dad'in mu'amula da Haseenah, duk da ta na da k'arancin shekaru amma ta na da tunani da hankali kamar babbar mace, uwa uba girman da ta ke ba shi da kuma matar shi, hakan na faranta ran shi sosai, shi ya sa yake ji baiyi zab'en tumun dare ba, za ta girmama matar shi sannan ta darajanta yaron shi da yan uwan shi, sannan ya na ji cewar za su zauna lafiya ita da Khadija, dan dukan su babu mai matsala a cikin su, dan da matsala ke sa a k'ara aure, to da shi da k'ara aure sai dai in an had'a shi da matan aljanna, amma Khadija ta gama mi shi komai a rayuwar duniya, lokaci ne idan ya yi ba makawa sai anyi. *Kallon kitse ake wa rogo* Da isar shi ya kira ta suka fito, yan mata uku ne su ka fito daga cikin shagon, kusan dukansu da ledoji a hannu, haka kuma dukan su babu mai hijab a ciki, dogayen riguna ne a jikin su sai kallabin rigar da suka yane kan su da shi, siririyar cikin su ya kafe da ido har ta bud'a gidan gaba ta shiga da murmushi a fuskar ta, sauran ma shiga su ka yi suka zauna, kallon shi ta yi tace "Sannu da zuwa adalin miji." Da murmushi yace "Barka da fitowa adalar amarya." Tayar da motar ya yi su ka fara tafiya... *A samu a addu'a.* _Duk mai son shiga grp d'ina dan samun littafi kai tsaye ya tuntub'i wannan mutanen._ *Mamienmu.* *My Heenat.* *My BK.* *Ma chΓ©rie Hakeema.* *Momyn Dady.* 30/12/2019 Γ 12:50 - πππ: ππππππππππ *KALLON KITSE* _(Ake wa rogo)_
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117