Chapter 89
Chapter 89
ta so ya sani yanzu, dan ta na tsoron rashin imanin yarinyar nan matar shi. *Bayan kwana biyu* an kai kayan Nura, kuma kamar yanda ya fad'a Khadija ma saida ta halarci kai kayan, kuma da yake a dangi ma ba kowa bane yasan abin da ya faru, Haseenah dama ba ta je ba dan haka ma ba su had'u ba, anje lafiya kuma ayi duk abin da ya dace, lokaci kawai za'a jira *wata uku* mai zuwa lokacin hutun farko na yan makaranta, duk lokacin da biki ya taso irin haka akwai wanda Khadija ce ta ke mu su d'inkin anko, yanzun ma ba ta gaza ba ba ta kuma duba abin da ya faru ba, haka ta d'inka kaya kala takwas ta aikawa kowa na shi daga ciki har da Hajia da kuma k'annan ta guda uku, k'annan Baban Usman biyu sai wasu tsofaffi biyu suma, kamar yanda Nura ya yi alk'awari ya kawo Choukra ta wuni gidan su Khadija, sai dare ya zo ya d'auke ta su ka koma bayan tasha goma ta arzik'i. *Haka* abubuwan suka ci gaba da tafiya da dad'i ba dad'i, Khadija na kula da cikin ta cikin kulawa sosai, Bilal na karatun shi hankali kwance ba tare da matsala ba, ranar da babu karatu kuma Khadija na kiran Nura ya zo ya d'auke shi ya kai shi wajen su Hajia, amma basu tab'a katarin had'uwa da mahaifin shi saboda yanzu gida sai su yi sati kwana shida ko biyar basu gan shi da idon su ba, wayar ma sai da k'yar ake iya samun shi wani lokacin, kuma har yanzu bai san Khadija na da ciki ba, dan malam yace ba ya so ya sani sai in Khadija ce ta fad'a mi shi ko kuma ya gani da kan shi, a haka har aka cinye wata *uku* wanda ya yi daidai da fara shagulgulan bikin Nura, a lokacin Khadija har ta fara zuwa awo dan cikin ta na wata *biyar* ne har ya fito ta yanda duk wani mai ido zai iya ganin shi, tun kwana biyu saura Khadija ta turo Bilal ya kwana nan har zuwa ranar bikin tare da gudummuwarta da na Mama da kuma ta su Ashir, gudummuwar da suka bayar ko yan uwanshi babu wanda ya mi shi wannan bajin ta. Wajen Haseenah ma haka abin yake, abin da ranta ya so ta ke ci tasha wanda ya mata, Aziza tuni ta jima da gane kurenta, dan kuwa duk aikin gidan ne ita ce ba dare ba rana, idan ba ta yi ba Usman ya balbale ta da jaraba, Haseenah na zaune ta na gatsar 'ya'yan itatuwa, sa'a d'aya shine ba'a cika yin girki a gidan ba kusan kullum saida a siyo daga waje, wani lokacin Aziza ta ci idan an siyo ko kuma ta d'ora wani abu ta ci, duk wannan bai cika damunta ba kamar yanda ta ga Usman ya zama kamar karan farautar Haseenah, in dai ya na gari to ya na gida nanak'e da ita ko gajiya ba ya yi, duk bak'on da zai zo wajen ta to fa haka zai dinga rawar jiki ya na aikawa ana siyo musu abin tab'awa, idan sun tashi tafiya kuma ya wadata su da kud'i da sunan kud'in taxi, haka ita kan ta Haseenah kud'i yake kashe mata kamar ba gobe, a wata *ukun* nan sai Haseenah ta shirga wata murgujejiyar k'iba, masha Allah ko fa kai mak'iyinta ne ka ganta dole k'ibar da ta yi ta burge ka dan ta mata kyau, hakan kuma ya sa Usman sake narke mata dan abun har kusan haukata shi take, ga magunguna da take aiki da su, ga k'iba (wanda kowa yasan akwai sirrin dake tattare da k'iba ba) ga kuma ciki, duk tsiyar nan da ake tsulawa Aziza ta kasa fad'awa kowa saboda kunya, to idan ita ma tace ta mallake shi kenan tsakanin ita da Khadija wacece ta mallake shi? Hakan ya sa ta yi shiru, ko gida taje idan aka tambaye ta wai ya na nan sai dai tace eh, idan ya na nan d'in, dan yanzu ko balaguro ya yi da k'yar yake iya sati d'aya zuwa kwana goma ya dawo, shiru take yi ba ta fad'a mu su komai inda su kuma su ka damu sosai su ka fara maganganu akai. *Yau* Alhamis ya rage nan da kwana biyu za'a d'aura auren Nura, su Rabi'a sun hallara ana ta kujuba-kujuba Aziza ta shigo gidan, dukan su kallon ta su ka yi da mamakin ganin ta ita kad'ai, Husseina ce tace "Aziza ke kad'ai ki ka taho?" Saida ta nemi gurin zama tace "Ni kad'ai na taho." "Ina Haseenah?" Cewar Rabi'a, tab'e baki ta yi tace "Ta na gida, wai ba ta jin dad'in jikin ta." Hajia da ita ba wannan ne damuwar ta ba cewa ta yi "Ina shi Alhajin ya ke?" "Ya na gida na baro shi, na ji ya na cewa ko zai kai ta asibiti." Girgiza kai Hajia ta yi tace "Allah ya kyauta, gaba d'aya ta mayar da shi wani sha-katafi, ko motsi taji a cikin ta sai ta fad'a mi shi shi kuma sai yace aje asibiti." Tab'e baki Aziza ta yi tace "Ai kam ba shi da maraba da shanyayye." "To ai ba kama bace, duk alamu sun nuna shegiyar yarinyar nan ita ce mai laifi, wallahi sai yanzu ne nake na tabbatar da tun farko *kallon kitse mu ka yi wa rogo*." Nura da ke fitowa daga d'akin shi cikin sauri ne ya kalle su dukansu yace "Ku sai yanzu ma ku ka sani kenan? To mu zuba zuwa mu ga mu da ku waye zaiyi nasara, 'yan bayan Khadija ko 'yan bayan wannan mai kama da agwagwar." Hajia ce tace "Abun bak'in cikin ma wallahi ta yanda gaba d'aya ta raba shi da mutane, d'an taimakon da muke san mu mi shi bamu ma gan shi ba bare mu taimaka d'in, amma ba dan haka ba da yanzu nasan komai ya wuce, kuma kinga shi malam ya ma bar maganar kamar baisan me ke faruwa ba." Nura dai ficewa ya yi ya kama sabgar gaban shi sai Rabi'a da tace "Ai kuwa ba za mu yarda ba wallahi, ni zanje gidan na ga me ke faruwa, wallahi saina fad'a mata magana." "Ai kuwa in ban cire ki a cikin dangin shi ba to tabbas zaki sha dukan tsiya." Cewar Aziza, da mamaki Rabi'a tace "Kamar ya duka? Ba shi da lafiya?" Aziza ce tace "Lafiyar shi lau, amma babu mai tab'a ta ya yi shiru, akan haka fa ya kori Garba mai gadi." Hajia ce tace "Ni kai na da zan ganshi da sai ran shi ya b'ace, tunda aka fara hidimar nan har yanzu banga k'eyar shi gidan nan ba, kuma ni har yanzu daga Nura har malam banji wanda yace ya bashi gudummuwar bikin nan ba, akwai abubuwa dayawa wanda da shi ne mu ka dogara, ba dan Allah ya rufa mana asiri ba yanzu yarinyar nan sun aiko da wannan gudummuwar ta su da ya za mu yi." Hassana ce tace "Bai fa bayar da komai ba hajia?" "Ni dai bai bani ba, kuma Nura da malam ba su fad'a min ba, kinga
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117