Chapter 52
Chapter 52
d'ora tukunya ta je madafar da kan ta ta d'auko duk abin da take buk'ata suka d'ora na su girkin. Haseenah na ganin haka ta shiga d'akin ta ta samu Usman kwance da waya ya na dannawa, cike da nuna b'acin rai ta yi tsaye tace "A gaskiya abin da ake min ba na jin dad'in shi ko kad'an domin Allah." Zaune ya mik'e yace "Me ya faru kuma? Waya tab'a min zinariya ta?" "Ba na son tashin hankali da rigima, ina so na zauna da kowa lafiya, amma aunty Khadija ta na so ta kawo wata b'araka a tsakanin mu ta hanyar raba girkin ta da nawa, saboda Allah ba dan neman magana me zaisa ta d'ora girkin ta bayan ga shi can na d'ora?" Da d'an mamaki ya kalle ta kafin yace "Amma ai na d'auka na hana ta, me ya sa ba ta ji abin da na fad'a ba." Hanyar fita ya yi yace "Je ki ci gaba da aikin ki, zan je na gani da kai na." Kai tsaye b'angaren Khadija ya nufo, ya na zuwa bai same su a wajen ba amma tukunya na saman gas, ai kuwa kamar hauka sabon kamu sai ya sa k'afa ya hanb'are tunkuyar, k'arar dungurawar tukunyar ne ya sa Khadija da ke falo suka taho a guje ita da uwani dan ganin meya faru, ganin Usman tsaye ya na huci ya sa Khadija kallon shi da mamaki tace "Abban Bilal, lafiya? Me ya faru?" Da yatsa ya nuna ta yace "Ban fad'a mi ki kar ki sake d'ora min girki a gida ba in har ana girki? Ko raina ni ne ki ka yi shi ya sa ba ki d'auki abin da na fad'a da mahimmanci ba." Cije leb'e Khadija ta yi ta rintse ido lokaci d'aya kuma ta bud'e ta kalle shi tace "Na ji, ka yi hak'uri ba za'a sake ba." "A sake ma a gani, wallahi ran ki zai b'ace, aikin banza kawai mace ba ka isa ka fad'a mata ta ji ba." Duk ya yi maganar ne ya na komawa in da ya fito, Uwani ta kalla tace "Ki gyara wuri ki mayar da komai muhallinsa." "To." Uwani ta fad'a jiki a matuk'ar sanyaye dan ba ta yi tunanin shine ba, falo Khadija ta zauna zuciyar ta na suya, wani b'angaren kuma kamar ta fashe da kuka amma ta na tausar zuciyar ta, dan in har abin da take tunani shine ke faruwa a yanzun, to fa zaifi ta adana hawayen ta dan zasu fi mata anfani nan gaba kad'an, haka suka zauna jugum da su Bilal har ya yi bacci ya tashi saboda lokacin islamiyya ya yi, har ya shirya ya yi sallah babu abinci daga wajen Haseenah, Usman kuma tunda ya gama masifa ya bar gidan har yau bai dawo ba, suna zaman jiran shigowar shi sai ga shi ya zo, Bilal ne ya fita ya same shi a farfajiyar gidan yace " Abba na shirya lokaci ya kusa." Shafa kan shi ya yi yace "Yarima har ka shirya? Gashi kuma yunwa na ke ji yanzun, amma muje na aje ka na dawo." Shiga su ka yi ya fara baya-baya ya na fad'in "Da alama sai na samar ma ka dreba (driver), dan Bilyamin ma ka ga aure zaiyi, ba za mu dinga takura shi ba wajen kai ka makaranta idan bana nan." K'ala Bilal baice ba har ya sauke shi a makaranta, juyowa ya yi ya dawo gida, Khadija na ganin mai gadi ya bud'e ma sa k'ofa ta fito, tsaye ta yi har ya fito daga mota ya kalle ta yace "Lafiya dai?" "Lafiya lau, dama akan maganar duba jikin Baba ne, ka ga har yamma tayi ba mu je ba, shine na ce ka mana izini mana idan na kammala girki sai mu tafi da ita ba sai mun jira ka ba." Cike da rashin damuwa yace "Kar ki damu, kije kawai idan kin gama, ita ta tafi tunda safe ai, ni na kai ta." Mamaki ne ya bayyana a fuskar ta tace "Ka kai ta? Amma Abban Bilal kasan tsawon lokacin da na d'auka a d'akin nan ina jiran ta?" Ta k'arashe da nuni da k'ofar falon ta. Tab'e baki ya yi yace "To sai me? Laifi na yi da na kai ta? Kinga bana son masifa, idan kema ki na so idan kon shirya ki yi magana sai na kai ki da kai na, shikenan?" Saida ya harare ta sama da k'asa ya ja k'aramin tsaki ya wuce, jiki a sanyaye ta juyo ta dawo, ta na zuwa ta samu Haseenah ta kawo abincin rana bayan sallah la'asar, ko kallon abincin ba ta yi ba tace ma Uwani "Ki ci abincin idan ki na buk'ata." Juyawa ta sake yi ta nufi madafa, aiki ta fara ba kama hannun yaro, saida Uwani ta gama cin abincin sai dai ba wani mai yawa ba, dan duk yunwar da take ji kasa cin abincin ta yi saboda ba za ta iya cewa ga abin da ya yi yawa ba, sai dai tabbas akwai abin da ya yi yawa a cikin girkin, nan suka shiga aikin su ita da Khadija kafin magriba su ka kammala, kula ya yi daidai da dawowar Bilal daga islamiyya, saida ta aje komai in da ya dace kafin ta shiga wanka ana kiran sallah, Bilal ma ko da ya dawo daga masallaci ta taimaka ma sa ya shirya dan tare za su tafi, Uwani ma saida ta sallame ta kafin suka fita tare ta aje gidan su suka wuce. Hira sosai ta b'arke tsakanin malam da Bilal, dan jiki ya yi sauk'i sosai, anso sallamar shi amma likitocin sunce su na son jinin shi ya daidaita ne, dan da aka kawo shi jinin shi ya hau kad'an, misalin takwas da rabi suna shirin tafiya sai ga Usman tare da Haseenah, sam ba ta nuna komai ba haka su ka musu sallama su ka tafiyar su. Sun koma gida, kuma tun Khadija na zuba idon dawowar Usman har ta gaji, shirin da tayi dan tarbar shi ya wartsake bacci na surarta, su kam suna can sun wuce wajen cin abinci daga nan su ka wuce 'yar kasuwa ya mata siyayya mai yawon gaske, wai ta cancanci fiye da haka ma a cewar shi, haka suka je ya siyo mata ice crime da sauran kayan k'walam da mak'ulashe, *11:56* na dare suka d'auki hanyar komawa gida. Khadija na jin k'arar bud'a gida ta fito farfajiyar, har saida ya wa mitar mazauni ya fito, da kan shi ya bud'ewa Haseenah ta fito kafin ya d'auko ledojin a hannun shi, tuni ta ankare da Khadija hakan ya sa tace "Beby ka kawo na taya ka d'auka mana." Kallon ta ya yi yace "Ke lafiyar ki k'alau? Wannan kayan ne zan baki ki d'auka salon ki ja min salalan tsiya, ba dani ba wallahi, to ma miye anfani na idan ban hidimta mi ki ba." Juyowar da zaiyi da nufin kallon gaban shi ya sauke ido akan Khadija da ta rik'e k'ugu da hannu d'aya, ajiyar zuciya ta sauke shi kam ko a jikin shi, dan har ga Allah ba ya jin wai ya yi ba daidai ba, sai ma d'aure fuska
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117