Skip to content

Chapter 40

Chapter 40

Kallon Kitse Book One Complete Hausa Novels 1,198 words 0 views Progress saved
Download Book

ta fad'a ba Khadija ta ji ba za ta iya d'auka ba, zuciya ce kawai ta d'ebe ta ta kife ta da mari, kafin ta ankara ta shak'o wuyan rigar ta cikin d'aga murya tace "In ke ba ki san zafin haihuwa ba ni na sani, in ba ki san darajar 'yaya' ba ni na sani tunda na haifa, idan ba ki san anfanin haihuwa ba, to ki bari har ki bari ki haifi na ki sai ki zuba cikin shara, dama ya fad'a min kin ce wai sai dai a dafa a bashi ya ci, to ki sani Bilal ba jinin matsiyata bane, ko gidan uban shi babu abinci ba zai rasa abincin da zai ci ba daga dangin uwar shi, ki kiyaye ni, sannan ki fita ido na." Sakin ta tayi ta juya ta fice, Zeinab ce ta yi saurin kallon Haseenah tace "Wai k'yale ta za ki yi? Jar uban nan, ai wallahi babu macen da ta isa." Wannan magana ce ta sa Haseenah d'aukar k'aramar tab'aryar da ke madafar ta fita, su na ganin haka su ka tashi da sauri su ka bi bayan ta, Khadija na daf da shiga falon ta Haseenah ta sauke mata tab'aryar nan a kai, dafe kai ta yi ta juyo ta na fad'in "Kai kai kai kai." Ta na ganin Haseenah ce sai kuwa ta cakume ta da kokawa,😂 (Allah ya kyauta, mata mu na bawa kan mu wahala wallahi, wata sai ki ga ma mijin da su ke fad'a akai kamar kalangu, amma haka za su yi ta bala'i a kan shi maimakon kwantar mi shi da hankali), k'awayen Haseenah na ganin haka su ka shigarwa k'awar su saboda tuni aka aza Haseenah ga k'asa ana shirgarta, Uwani na ganin haka ta fita da gudu zuwa gidan mak'wabtan da Khadija ke abun arzik'i da su, Bilal kam wayar shi ya d'auka k'arama ya kira mahaifin shi ya fad'a mi shi, mai gadi na daga gefe ya na dan Allah ayi hak'uri amma ko jin shi ba su yi, jin zafin dukan da k'awayen ta ke mata ne ya sa Khadija finciko wata daga cikin k'awayen ta had'a su ta taushe, wuri fa ya kaure ana ta bawa hammata iska sai ga mak'wabtan sun shigo, da gudu su ka k'arasa su ka d'aga Khadija daga kan Haseenah da *Farida*, anyi jina jina sosai kamar filin yak'i, cecekuce aka shiga yi tare da aikawa juna ashar, Khadija na k'ok'arin k'wacewa ta koma ga Haseenah amma an rik'e ta, su na haka fa gida ya kaure Usman ya baro mota waje ya kutso ciki, ganin su duk a yamutse ya sa ya tsaya ya sa hannu ya rufe fuskar shi, ya d'an jima a haka kafin ya k'araso wajen, k'awayen Haseenah ya fara kallo yace "Yamma ta yi, za ku iya tafiya." Cikin sanyin jiki duka aka watse aka bar shi da matan shi, har Uwani ma ba ta tsaya ba tafiyar ta ta yi gida, falon shi ya nufa ya na fad'in "Ku same ni a falo na." 😂 *Aiki ya samu Usmanu, yanzu ma ka fara cewa a biyo ka falo ai* Su na shiga daga zaman da Khadija ta yi zai tabbatar maka ba arzik'i, cikin b'acin rai ya yi tsaye yace "Me ku ka zama? Me ku ke son mayar min da gida? Wannan wane irin dabbanci ne?" Tsaye Khadija ta mik'e tace "Dakata malam, dakata min, a sani na irin haka ba ta tab'a faruwa ba, to akan me sai yanzu haka za ta faru? Akan me ye amaryar ka za ta nemi ta raina ni? Ni sa'ar ta ce? Ko kai ka ce ta raina ni? Saboda rashin sanin darajar mutane har ta bud'e baki tace min wai mi ye anfanin Bilal a gidan nan, bayan kin fad'a ma sa bai da anfanin komai sai dai a dafa a ba shi ya ci, to uwar ki ce ke dafa mi shi ya na ci? To ki kama bakin ki ki dinga sanin me za ki fad'a." Mayar da kallon ta ta yi ga Usman tace "Kai kuma dan Allah idan kun shiga ciki ka yi k'ok'ari ka sanar da ita mahimmancin d'an ka gare ka da anfanin shi gare ka, ni ba buk'atar sai na fad'a mata anfanin d'ana gare ni, amma ka fad'a mata shi kad'ai gare ni, dan haka bana had'a yaro na da kowa da kuma komai a duniya, a matsayi na na uwa kuma zan iya yin komai saboda shi." Ta na gama fad'a ta fice ta bar su, juyowa Usman ya yi ya na kallon Haseenah, a hankali ya furta "Haseenah, ki na tambayar anfanin haihuwar Bilal a gidan nan? Ni fa uban sa ne, duk fafutukar da na ke yi saboda shine na ke yi, amma ki bud'e baki ki ce me ye anfanin haihuwar shi." Girgiza kai ya yi cike da damuwa ya dafe k'ugu da hannu d'aya yace "Maganar gaskiya Haseenah ba na so na nuna mi ki b'acin rai na, amma ki sani ko Khadija ba na buran b'acin ran ta bare kuma Bilal da ya fito daga tsatso na, ina k'aunar iyalin nan nawa matuk'a, su ne ni, su suka mayar da ni mutum da har ki ka so ni a haka, ki kiyaye furta abin da zai iya ja mi ki matsala, sannan k'awayen nan naki in har kinsan zuwan su gidan nan ba alkairi bane, to zaifi kyau ki fad'awa kowace ba na son sake ganin k'afar su a gidan nan." Ya na gama fad'a shima ya fita ya barta, kallon shi ta yi a matuk'ar hassale ta mik'e ta nufi madafa, kashe wutar ta yi ta gyara abin da ya sawak'a ta koma d'akin ta, wayar ta ta d'auka ta kira Mariya ta fad'a mata duk abin da ya faru, nan dai ta girmama abin tare da k'ara tunzurata sannan tace ta bar komai a hannun ta, da haka su ka yi sallama ta yi wanka ta shirya, sai dai ba wata kwalliya ta yi ba dan duk jikin ta ma ciwo ya ke na tsinannan dukan da ta sha. *************** Bayan sallah isha'i Khadija na zaune tare da Bilal a falo Nura ya shigo gidan da rahar shi kamar yanda ya saba, tun daga bakin k'ofa ya ke fad'in "Dije, Dije ba ta jina ne? Na shigo amma ki kasa tarba ta tun daga k'ofar gida." Ganin Khadija zaune ta yi shiru sai kallon shi take ya sa yace "Ah lallai ma matar nan, ashe ki na jina na ke ta kwaroronton nan amma ki ka share ni? Ko dan yau ban baki kud'in cefanai ba?" Khadija da har yanzu ran ta a b'ace ya ke k'ala ba tace mi shi ba, Bilal ne ya tarbe shi da murna sosai, tare su ka zauna ya na kallon Khadija ya kalli Bilal yace "Yaro waya tab'a min maman ka ne haka ta ke ta kumbura?" Shiru Bilal ya yi ya na kallon ta, a hankali ta maido kallon ta gare shi tace "Sannu ko." "Ai na ba za ki yi magana ba, da na tabbatar mi ki mijin gaske ne ni." "Ya su Hajia?" Ta fad'a ba yabo ba fallasa, saida ya sauke

Table of Contents

Chapters

117 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117