Skip to content

Chapter 68

Chapter 68

Kallon Kitse Book One Complete Hausa Novels 1,196 words 0 views Progress saved
Download Book

gida ranta ba dad'i ta na ji a ranta Khadija ta bata kunya, *Khadija baiwar Allah* ba ta san ma tsiyar da suke ba, dan ita abincin Haseenah ma idan ta aiko kullum saidai ta kira mak'wabtanta azo a d'auka, ita kuma haka za su yi ta yan dubaru ita da d'an ta. *Yau sati biyu* kenan da tafiyar Usman, kuma jibi ne komawa makaranta, hakan ya sa Usman kiran Khadija a wayar ta, ta yi mamaki dan abu ne da bata tab'a gani ba tunda ya tafi, ta na d'auka suka gaisa a gajarce ya d'ora da "Na ga yara na ta shirin komawa makaranta, amma saboda banda girma da mutumci a idon ki ban isa ki fad'a min ba ko da wani abu da ku ke buk'ata." Murmushi kawai ta yi tace "Allah huci zuciyar ka ranka shi dad'e, ai akwai hikima sosai a cikin hallitar kowane bawa da iyaye biyu, naga ba ka gari ne kuma kullum cikin aiki ka ke, ba ka da lokacin waya dani bare har mu yi magana da ta shafi d'an ka, shi ya sa ni kuma na mi shi duk wani abin da zai buk'ata, har kud'in makarantar ma na biya." Duk da ya ji wani abu a zuciyar shi a game da ita, amma basarwa ya yi yace "Uhum." Kashe wayar kawai ya yi, take ya durmiya cikin tunani, Khadija kud'in da ya bata babu abin da za su mata, amma da su take buk'atunta har ta biyawa yaro kud'in makaranta, amma kuma Haseenah daya lodawa masu yawa yanzu haka zaije ya tura mata kud'i ne dan tace suna buk'atar kud'i, dan haka ya kasa nutsuwa ya kira Aziza ya tambaye ta da gaske Haseenah ta na bata kud'in adaidaita, bud'ar bakin ta cewa ta yi "Eh yah Fodio, ta na bani na zuwa da dawowa, har da ma d'an na kashewa, kuma kullum fa sai mun siyi abinci in dai ranar girkin Khadija ne, kuma jiya masu karb'ar kud'in ruwa sun zo dole sai aunty Haseenah ce ta basu." Duk da ya yarda da Aziza dan abu d'aya suka fad'a amma Haseenah ba ta fad'a mi shi suna siyen abinci ba, haka dai ya sa Nura ya kawo mata kud'in sannan ya kira ya tambaye ta K'arin haske akan abin da Aziza ta fad'a, cikin marairaicewa tace "Kawai ba na so ne wani abu ya faru kuma ace ni ce sila." "Shikenan to ya yi kyau." Ya fad'a ya na kashe wayar, wayar Khadija ya kira dan jin dalili, amma suna gama waya ta farko Aishatu ta kira ta tace ga ta k'ofar gida mai gadi na mata iskanci, dariya Khadija ta yi kafin tace ta na zuwa, Bilal ta aika sai gasu sun shigo tare, Aishatu budurwace da ke da larura ta iska, hakan ya sa komai nata daban ne, fad'a da masifa kamar shan ruwa ne a wajen ta, tunda su ka shigo tare da Bilal ta ke zagin mai adaidaitar da ya kawota wai yace sai dai ta bashi arba'in ita kuma ishirin ta bashi, hakan ne ma ya sa sam Khadija ba ta ji kiran Usman ba saboda wayar na (vibration) ne, aifa nan hira ta b'arke suna ta yi kamar wanda aka jonawa lantarki, tunda wuri kamar yanda ta saba suka shiga girkin yamma, kuma yau ta yi niyyar yin waina dan akwai wa abokanan mahaifin ta, saboda sabo ya sa ba wani wahala tasha ba musamman kuma ga mai kamawa, sai salade da shima aka siyo mata suka gyara abinsu, Bilyamin ta kira ya kai wainar in da ta zubawa Haseenah na su tace ya kaii, da sauri Aishatu tace ya jirata su tafi tare ta ga amarya, nan fa gaban Khadija ya shiga dukan uku uku, dan ba lallai ta shiga lafiya ta fito lafiya ba, k'aramin aikinta ne ta k'arewa Haseenah kallo tace au dama wannan ce amaryar? Saida Khadija ta rik'e hannunta tace "Dan Allah idan ki ka je ku gaisa kawai ki juyo ki dawo, ba na son tashin hankali ko kad'an." "Wai amaryar 'yar akuya ce kenan? To ai sai ki fad'a mata ki na da irin mu 'ya'yan busurai, mu za ta wa iskanci?" Cewar Aishatu har tana gaggawar tafiya, rik'e ta Khadija tayi tace "Ni fa ban fad'a mi ki haka ba, kawai dai ku gaisa ki juyo ki dawo, kar ki ce za ki tsaya wani abun da bai shafe ki ba." Saida ta fizge hannunta tace "Naji dallah." "Kinyi alk'awari?" Cewar Khadija ta na binta da kallo, k'ala ba tace ba ta bi bayan Bilal su ka shiga, Bilal ne ya yi sallama amma shiru, bubbuga k'ofar ya yi ya sake jin shiru, sai Aziza ce ta lek'o daga sama ta hangeshi tace "Bilal ga auntyn ka nan sama." Daga nan yace "Abinci ne na kawo mu ku." "Kawo nan." Cewar Aziza, kallon Aishatu ya yi tace "Muje saman na ganta, ai ko saman bakwai take sai na ganta yau." Can suka nufa, Bilal na isa ya aje abincin sai aishatu da ke k'arewa Haseenah kallo ta hakimce akan kujera ta na latsa waya, kallon Aziza ta yi tace "Ke na ganeki k'anwar Usman ce ko?" "Eh, ina wuni." Cewar Aziza wacce ba tun yau ba tasan Aishatu farin sani, mayar da kallonta ta yi ga Haseenah ta na wani murmushi tace "... *Allah fidda A'i daga rogo.* 15/02/2020 Γ  13:58 - πŸ’‹πŸ˜˜πŸ’‹: πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘ *KALLON KITSE* _(Ake wa rogo)_ πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘ _SAMIRA HAROUNA_ *Litattafan marubuciyar* *1* _KAUSSAR_ *2* _D'AUKAR FANSA_ *3* _BA SO BANE_ *4* _AUREN HAD'I_ *5* _SANIN MASOYI_ *6* _JIHADI_ *7* _K'ANGIN RAYUWA_ *8* _ITACE K'ADDARARMU_ *9* _KAWU NA NE_ *10* _MAATA_ *11* _KALLON KITSE..._ *SADAUKARWA GA* _MATAN FARKO_ πŸ§•πŸΌ *(UWAYEN GIDA)* πŸ‡ΈπŸ‡¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S* _(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_πŸ€œπŸ€› ```Fatan alkairi masoya``` _Bismillahir rahamanir rahim_ *26* "Wai ke ce dama amaryar da ya yi? Kai, amma dai wallahi maza ba su da tabbas, yanzu shi dan Allah rufe mi shi ido ki ke kayi? Ko kuma tallarki aka mi shi?" Bilal ne ya kalle ta yace "Aunty Aishatu mu tafi ko." Bushewa ta yi da dariya tace "Bilal barni na k'are kallon amaryar Baban ka, wannan mace haka sai kace kaza ta ga wuk'ar yankanta." Wata dariyar ta saka mik'ewa Haseenah ta yi da nufin magana sai Aziza ta rik'e hannun ta, girgiza mata kai ta yi alamar a'a ta rabu da ita, ganin hakane ya sa Aishatu cewa "Da kin barta ta fad'i abin da ke ran ta ai kar ta zama ajalin ta, ni ma saboda ba zan iya yin gulmarki bane ya sa na fad'i abin da ke raina tun a gaban ki." Iza k'eyar Bilal ta yi tace "Mu tafi kai yaro ka ji, Allah ya tsigewa Babanka rigar wahala, wannan mata kafin ya sa k'asusuwanta su cika ai sai mai kampanin gidan shinkafa na *oriba* ya san da zaman shi." Ta na wucewa Haseenah tace "Ita kuma wannan mahaukaciyar fa? Wacece ita?" Ajiyar zuciya Aziza ta sauke tace "Hum! Cousine d'in Khadija ce, mahaukaciya ta sawa a gidan gaba, wallahi da kin biye mata ina tabbatar mi ki yau a gidan nan sai kinga motar masu kashe gobara." Tab'e baki ta yi tace "Kin

Table of Contents

Chapters

117 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117