Skip to content

Chapter 11

Chapter 11

Kallon Kitse Book One Complete Hausa Novels 1,199 words 0 views Progress saved
Download Book

_KAUSSAR_ *2* _D'AUKAR FANSA_ *3* _BA SO BANE_ *4* _AUREN HAD'I_ *5* _SANIN MASOYI_ *6* _JIHADI_ *7* _K'ANGIN RAYUWA_ *8* _ITACE K'ADDARARMU_ *9* _KAWU NA NE_ *10* _MAATA_ *11* _KALLON KITSE..._ *SADAUKARWA GA* _MATAN FARKO_🧕🏼 *(UWAYEN GIDA)* 🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S* _(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛 ```Fatan alkairi masoya``` _Bismillahir rahamanir rahim_ *7* Kasancewar Bilal zai koma makaranta yau ya sa Khadija ta shi da wuri ta nufi madafa dan shirya abin kari, (albarkacin kaza k'adangare kan sha ruwan kasko), tun da ta tunkari k'ofar ta gan ta bud'e ta ke mamakin yanda k'ofar ke bud'e, da wannan mamaki ta k'arasa shiga, turus ta ja ta tsaya ganin oga malam yallab'ai kuma alhaji Usman ya d'auki k'atuwar tasa daga kan gas ya na juye tafasashen ruwan da ya dafa a k'aramin bokiti, da sauri ta k'arasa ta na fad'in "Abban Bilal, me ka ke yi haka?" Wani abu ya ji tare da kunya dan baiso ya ganta ba ko ita ta gan shi, d'agowa ya yi bayan ya juye ruwan ya na d'an had'e fuska yace "Um, wallahi, wai wanna ce, ina jin dai, kamar dai ba ta cika wanka da ruwan sanyi bane da safe, to shine na..." Katse shi ta yi da cewa "Uhum! Na gane ma, ka kai mata to kafin su huce." D'auka ya yi cike da kunya ya fice, sai da ya b'ace ma ganin ta taji hawaye sun cika idon ta, cire gilashin ta ta yi ta share k'wallan, ji ta yi ma ba za ta iya komai ba dan haka ta juyo ta fito, ta na zuwa falon ta taga abin mamaki, da sauri ta saki murmushi tace "Wa na ke gani kamar Uwani?" Da dariya matashiyar yarinyar tace "Ni da kai na Maman Bilal." "Uwani yaushe ki ka dawo? Sai kawai na gan ki haka kamar aljana." Dariya Uwani ke yi har tace "Jiya na shigo da magriba, shi ya sa ma ban zo tun jiya ba." "Kai, amma ko na ji dad'in zuwan nan na ki, dan yanzu haka da ki ka ganni wallahi na gaji ne, har na shiga madafar kuma na fito da d'aki ne zan koma ba kwanta kuma sai gaki." Da karsashi Uwani ta mik'e tace "Maman Bilal ba ki da matsala tun da na dawo, yanzu fad'i me za'a dafa sai na shiga da kai na." "A'a ba za ayi haka ba, ai ganin ki karsashi ya k'ara min, kawai muje tare sai mu d'ora, kinga ma daga nan sai ki bani labarin abinda ya tsayar da ke." Dariya ta yi su ka nufi madafar, aiki suke su na hira ta na fad'a mata abin da ya tsayar da ita, da haka su ka kusan kammalawa Khadija ta sakar mata aikin ta tafi d'aki dan yin wanka. Da taimakon Usman Haseenah ta shirya kan ta sai shefiyar shagwab'a take zuba mi shi, shi kam yau ya na jin ya samu sabuwar hanya sai wani biye mata ya ke, ba dan yaji abin da ya saba ji ba, sai dan kawai yau sabuwar hanya ce ya bud'e da kan shi, a k'arshe ma daga d'akin ta zuwa falon shi sai da ya d'auko ta ya fito da ita, ya na zaunar da ita yace "Bara na je na samo mi ki abin da za ki ci ko, na san yanzu ki na jin yunwa." Cike da kissa da salon iskanci tace "Um, amma gaskiya ba komai zan iya ci ba." Sai da ya sumbaci hannun ta yace "Ranar ki ce yau amarya, ki fad'i duk abin da ki ke son ci, za'a kawo mi ki shi gaban ki." Cike da yauk'i tace "Da fari dai ruwan bunu na ke son na fara korawa a ciki na, bayan nan kuma sai na samu tuwon shinkafa." Wani kallo ya mata da murmushi yace "Eyeee, amarsu, ko dai a dare d'aya har na yi nasarar aika sak'on ke kuma kin karb'a hannu bibbiyu." K'asa ta yi da kai ta na murmushi, janyo ta ya yi ya rumgume yace "Allah ya sa haka Haseenah, zan fi kowa farin ciki da faruwar hakan, a karo na biyu Allah ya sake nuna min jini na a duniya." Jin haka ai sai ta shagwab'e tace "Yunwa fa na ke ji sosai rabin rai." Zunbur ya mik'e yace "Shikenan to, yanzu zan dawo, bara na shiga na ga auntyn ki sai na wuce." Kwab'e fuska ta yi alamar za ta yi kuka, da sauri ya dawo ya zauna yace "Me ye kuma na kuka? Ciwo ki ke ji har yanzu?" Kai ta girgiza tace "Ina tausayawa kai na ne dai kawai." "Da me ya faru?" Cikin goge ido tace "Ka ce sai ka fara zuwa wajen aunty na, kuma na san kai da aunty na kamar Roméo da Juliette ne, ban san yaushe za ka fito ba." Murmushi ya yi yace "Yanzu fad'a min ya ki ke so ayi to?" Cikin turo baki tace "Idan ka dawo ai sai ka je ku gaisa, kai kuma cinye kan ku ni dai ina daga nan ina cin abinci na." Dariya ya yi yace "Kenan ba ki damu da ni ba ko?" Hannun shi ta rik'o tana kallon idon shi tace "Da kafin daren jiya ka fad'i haka sai na iya yarda abisa wasu dalilai, amma banda safiyar da ta tabbatar min mun zama d'aya ni da kai." Murmushin jin dad'i ya yi ya sumbaci kumatun ta ya mik'e yace "Sai na dawo, za ki sha zallar ruwan madarar soyayya." Kashe mi shi ido ta yi tare da d'ora k'afa d'aya kan d'aya, Khadija ta fito cikin wata arniyar doguwar rigar shadda, kwanukan abincin ne hannun ta tare da Uwani a bayan ta, abin mamakin da ba ta tab'a ganinshi ba wai Usman ya fita ba tare da ya lek'a in da take ba, Haseenah da ta ga shigowar su ko kallo babu wanda ta ma, sai da ta aje kwanukan daga in da take tace "Amarya sannu da hutawa." "Sannu." Ta fad'a ta na wani yamutsa fuska, Uwani ce tace "Ina kwana aunty amarya." Kallon ta ta yi cikin rashin sanin wacece ita, Khadija ce tace "Sunan Uwani, mai aiki na ce, amma yanzu ta zama mai aikin mu gaba d'aya." K'ala babu wanda ta tanka ma sai ma d'auke kai da ta yi, d'an cije leb'e Khadija ta yi alamar muje zuwa d'in nan, fita su ka yi su ka d'auko sauran kayan abin karin, ta na cikin jera su Bilal ya fito cikin shirin makarantar shi, da fara'a ta kalle shi tace "Yarima har ka shirya?" Sai da ya je gaban ta ya sumbaci kumatun ta yace "Ina kwana sarauniya." Dariya ta yi tace "Ka tashi lafiya?" "Lafiya lau." Ya fad'a ya na jan kujera zai zauna, ido ta zaro mi shi tace "Kai, ba ka ga auntyn ka bane? Ka je ka gaishe ta mana." Tsaye ya mik'e yace "Ki yi hak'uri Ammie, ban lura da ita ba." Wucewa ya yi ya je har in da take, hannun shi ya d'ora a wuyan ta ya kai bakin shi zai sumbaci kumatun ta, ba zato ba tsammani ta ji abun, dan haka ta yi saurin zabura tare da ture shi da k'arfi har

Table of Contents

Chapters

117 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117