Chapter 42
Chapter 42
sai ki yi ta wani mak'alewa ba kya so ki tafi." Cikin turo baki tace "Ni wallahi da ka bar ni na kwana anan ma da zanji dad'i, gidan mu ne fa." "Wai ki na nufin har kinyi kewar gidan da har ki ke so a bar ki ki kwana anan?" "Sosai ma, ai tun ranar da aka kaini gidan ka na fara kewar gidan mu." Kallon Khadija ya yi yace "Hajia ki na jin ta fa, yanzu ke dan Allah za ki yarda ace ki je gidan ku ki kwana?" Fuska ba annuri tace "Saboda ni banyi shak'uwar da zan iya kewar 'yan uwa na ba kenan? Ai ko yanzu ka ce tafi to sai dai ka aje ni na d'auki adaidaita, dan gani zanyi kamar motar nan ba ta gudu sosai." Maida hankalin shi ya yi kan tuk'i yace "Kenan idan na fahimce ku duk cikin lamarin ni ne bare, kun nuna min har yanzu ba ku d'auka ta kamar yanda na ke d'aukar ku, kun nuna min har yanau babu wacce ta ke jin za ta iya k'arar da rayuwar ta a tare da ni." Wata shegiyar harara Khadija ta masa tace "To me za mu zauna mu yi da tsoho, ka na so ne mu kai lokacin da za mu fara goge ma ka majina a hanci." Hannu ya kai ya damk'o wuyan ta ya na dariya ya na fad'in "Ni ne ma tsohon? Yanzu ke mijin na ki ne tsoho? Lallai ma yarinyar." Gwalo ta mi shi ta na fad'in "Gashi kai ma ka fad'a da bakin ka, har yanzu ni yarinya ce, tunda sai nan shekara biyu zan cika *talatin da biyar*." Juyowa ya yi ya kalli Haseenah yace "Ke kin yarda mijin ki tsoho ne?" Haseenah da haushi ya fara kashe ta ne tace " A zahiri wanda bai san ka ba zai iya kiran ka da tsoho, amma ni a wuri na ba tsoho bane, dan ni nasan k'arkon miji na." Dariya Usman ya yi ya juyo ya bata hannu alamar su bige β tare da fad'in "Ban biyar amarya ta." Bashi ta yi su ka bige su na dariya. Kallon Khadija ya yi yace "Sai yanzu ai na fahimta, ashe ke ce ki ka tsufa ba ni ba." Dariya ita ma ta yi tace "Amarya kam dole ta fad'i haka, amma da tasan waye kai lokacin da ka ke ji da k'uruciya, to fa da za ta gasgatani d'ari bisa d'ari, amma da ya ke zuwan shekaranjiya ce ita ba za ta gane komai ba, ko ba haka ba?" Ta fad'a ta na kashe masa ido d'aya, turo baki ya yi gaba yace "Za ki yi magana ne idan ki ka shigo hannu na." Bushewa ta yi da dariya tace "Yanzun haka ina matakin shekarun cikakkiyar mace ne da ke jin jini a jika, dan haka ba za ka tab'a tsorata ni ba malam Manu." Wani mayan kallo ya mata ya na d'an cije labb'an shi na k'asa, sake tsinkewa ta yi da dariya har da kai mi shi duka a hannu ta na kwantar da kan ta a kafad'ar shi ta na fad'in "Ka tuna? Ka tuna wannan ranar da ka fad'a min haka? To nima na rama, yanzu ina kan shekaru na ne, dan ni yanzu ma ji na ke kamar yanzu ne na balaga, dan haka ka zama tsoho a wuri na." Shi ma dariyar ya ke sosai yace "A ranar kam sai da na k'ara gyara tsayuwa ta sannan na ce mi ki, yanzu fa sai kinyi hak'uri da ni, dan ina ganiyar shekara talatin da biyar ne, shekarun hura wutar..." Da sauri ta rufe ma sa baki su na ci gaba da dariya, d'an k'aramin tsaki Haseenah taja da ya sa su ka kalle ta, saita nutsuwar su su ka yi Khadija tace "Yi hak'uri amarya." Take ta kalli Usman ta saisaita murya tace "Abban Bilal, munga shekaran jiya tare da kai, haka ma munga jiya da yau, insha Allahu da izinin ubangiji za mu ga gobe." Wani fari ya mata da ido alamar wai ta sumbace shi, ita ma mayar masa ta yi da idon alamar a'a, Haseenah da abin duniya ya isheta ne tace "Wai har yanzu ba'a kawo gidan ba ne?" Babu wanda ya kalle ta sai Usman da yace "Halan bacci ki ke ji?" Banza ta yi da shi daga haka har su ka isa gidan, nan ma da suka shiga wata sabuwar hira aka dasa Khadija da Usman da Issoufou da mai jego kasancewar babu kowa a gidan sai yaran su da kula mai tayata kwana, da ganin yanda suke hira kasan akwai shak'uwa da fahimtar juna da kuma mutunta juna, saida dare ya yi su ka taso su ka dawo gida, kowa d'akin shi ya nufa ya yi shirin kwanciya, sai da Usman ya zo ya wa Khadija saida safe kafin ya koma, duk da Haseenah ba ta bashi hak'uri ba akan abin da ya faru, amma da ya neme ta sai ya sa ta sake jin girman kai, hakan ya nuna mata ko ka wa namiji laifi ran shi ya b'ace dole shi zai neme ka ko dan biyan buk'atar shi, da haka gari ya waye. *Yau kuma da wacce aka wayi gari? Sai kun biyo ni.* 02/02/2020 Γ 20:58 - πππ: ππππππππππ *KALLON KITSE* _(Ake wa rogo)_ ππππππππππ _SAMIRA HAROUNA_ *Littatafan marubuciyar* *1* _KAUSSAR_ *2* _D'AUKAR FANSA_ *3* _BA SO BANE_ *4* _AUREN HAD'I_ *5* _SANIN MASOYI_ *6* _JIHADI_ *7* _K'ANGIN RAYUWA_ *8* _ITACE K'ADDARARMU_ *9* _KAWU NA NE_ *10* _MAATA_ *11* _KALLON KITSE..._ *SADAUKARWA GA* _MATAN FARKO_π§πΌ *(UWAYEN GIDA)* πΈπ¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S* _(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_π€π€ ```Fatan alkairi masoya``` *Godiya masoya, πna yi dariya sosai ganin comment d'in ku rututu, Haseenah no fan's.*π π _A sannu a hankali sai cinye shekaru na na ke tamkar yanda nake cinye abinci na, damuwa ko tunanin hakan ba shine mafita ba, domin kuwa babu abin da zai dakatar da ita idan har ta zo, fata na bai wuce na gama da duniyar nan lafiya ba, sannan na rabu da iyaye na lafiya da 'yan uwa da masoya, ba na buk'atar tsawon shekaru, na fi buk'atar k'arancin su in dai masu albarka ne da anfani, *ina taya kai na bak'in ciki*, domin ba na ce farin ciki ba, domin har yanzu banyi wani tanadi dan ranar gobe ba, amma abun mamaki dayawa su na murna ne har da shagali saboda sun k'ara shekara, basa la'akari da shekarun su ne suke tafiya basu ankara, sai sun wayi gari sun jisu cikin k'abari, Allah ka bamu shekaru ma su albarka._π _Bismillahir rahamanir rahim_ *18* Ya shirya zai fita ya shigo wajen Khadija ya same ta zaune a falo sai Uwani da ke aiki, bayan sun gaisa ne tace "Babban mutum ina neman izinin ka zanje wajen kitso da lalle?" Murmushi ya mata yace "Ko ban tambaya ba nasan za ki fara shirya min kan ki ne, dan haka kin samu izini na, sannan..." Ya fad'a ya na saka hannu aljihu ya ciro kud'i, mik'a mata ya yi yace "Ga wannan ko, sai a k'ara ayi kwalliya da kyau." Sunkuyar da kai ta yi ta rufe ido da hannayen ta,
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117