Chapter 9
Chapter 9
da aka watsa mata, gilashin ta da ya k'ara mata kyau da gani, d'aurin d'an kwalin da sai kace tafiye ya ke daga k'asar waje, dare ya yi kuma an kawo amarya, tun da Khadija ta ji ayiriyiri gaban ta ya fara wani sabon dukan, haka dai aka yi duk wani abu da aka san ana yi, an kawo amarya d'akin uwar gidan an gaisa an kuma mu su nasiha, sun saka ango tsaka an sake mu su nasiha tare da hotuna, in dai har za'a fad'i gaskiya to Haseenah ba ta ko kama k'afar Khadija ba, ta kowane b'angare ma dan babu had'i tsakanin su ma, su kan su danginta da k'awayen ta sun girgiza da ganin ta a haka, sai dai kowa ya san Usman ya yi dacen mata, ganin shi d'in ba wani kyakyawa ba, shi ba hasken fata ba, haka dai aka watse aka bar su kowa ya koma d'akin shi, dan dama babban falo shine na Usman, k'ofa ya yi ta yanda kowace za ta iya shigowa daga falon ta zuwa na shi. An tafi mayar da mutane aka bar amarya da k'awayen ta kafin a zo a d'auke su, nan fa hira ta b'arke tsakanin su, Zeinab ce ta fara da "Wallahi rabin rai sai kin zage damtse, kinga wannan matar ta shi, ni fa har ta ban tsoro." *Farida* ce tace "Bari kedai, ashe haka ta ke?" Murmushi Haseenah ta yi tace " Lallai *kallon kitse ku ke wa rogo*, ni kuma ko kad'an ba ta ban tsoro ba, dan na riga da na san komai." Zeinab ce tace "Kamar me fa? Dama ku na hirar ta da shi?" "A'a, amma dai akwai wasu abubuwa da su ka nuna min ita d'in shashasha ce." "Ban gane ba k'awata, ki min gwari-gwari mana." Cikin nutsuwa tace "Na fahimci mijin ta na son girmamawa, ya na son a dinga ma sa kalaman soyayya, dan in mu na hira da shi sai mu kai k'arfe *11:00* na dare mu na waya, duk kalmar da na fad'a mi shi sai ya gode min tare da godewa Allah da ya sa zai aure ni, shi ya sa na san cewa ita ba ya samun nutsuwa a tare da ita, kyan d'an maciji ne kawai da ita, kuma wallahi na d'aura d'amarar faranta mi shi fiye da ita." Ajiyar zuciya Zeinab ta sauke sai wata daga ciki mai sunan *Jamila* ce tace "To k'awata, Allah ya sa dai ba *kallon kitse ki ke wa rogo ba*, dan wasu mazan ba kya iya gane cikin su, watak'ila ma shi d'in mai son kulawa ne kawai, shi ya sa ya ke jin dad'i kema za ki bashi farin ciki." Kallon ta Haseenah ta yi yi tace "Hum! Ba ko d'aya wallahi." Kiran Usman ne ya katse ta, ta na d'auka tace k'awayen ta su fito a mayar da su gida, nan su ka tashi su na tsokanar ta wai za su zo cin kaza da sassafe, ita kuma ta na dariya ta na fad'in ba zai yiwu ba ita da shan wahala su da cin kaza, haka su ka bar ta wasu na ganin kamar ta na son yin kuskure na gani-ganin da take wa Khadija, haka dai gida ya yi shiru ba kowa, ango kuma bai shigo ba sai da dare ya raba sosai, lokacin Khadija ta yi shirin kwanciyar ta ta na kwance a d'akin Bilal da shima ya jima da yin bacci, d'akin ta ya fara shiga bai same ta dan haka ya wuce d'akin Bilal, ta na jin shigowar shi ta rufe ido kamar mai bacci, tashin ta ya yi amma ta nuna kawai ta yi nisa a baccin ta, sai da ya tallabo ta ya kalli idon ta yace "Ki tashi mana ki kalle ni." Ido rufe tace "To me zan maka? Amarya ce da kai fa." Sake komawa ta yi ta kwanta, ledojin hannun shi ya kalla yace "To tashi ki d'au leda d'aya anan?" Juyowa ta yi ta kalleshi duk da dai ba ganin shi ta yi da kyau ba haka tace "Tun fa a gidan mu ina ganin bak'ar leda, kuma nasan kaza ce a cikin ta, kuma ba na sha'awar cin ta, dan haka ko dai ka tafi da ita can za ku fini buk'atar ta, ko kuma ka aje watak'ila idan d'an ka ya tashi da safe ya ci kazar siyar bakin kishiyar mahaifiyar..." Da sauri ya daka mata tsawa ta hanyar fad'in "Kar ki soma Khadija, wallahi kar ki fara sakawa yaro na banbanci a cikin k'wak'walwar shi tun yanzu, sam ba zan lamunci wannan ba, ke da Haseenah yanzu duk d'aya ku ke a gurin shi." Juyawa ta yi ta d'auki gilashin ta ta mak'ala ta na murmushi tace "Tun yanzu Abban Bilal? Yaushe rabon da ka d'aga min murya irin haka? Sai yau? Saboda ka yi amarya? Yayi kyau, amma bari ka ji nima na fad'a ma ka, Bilal yaro na ne ban da wata banzar mace da ta shigo gidan nan yau, idan kai ka shirya sadaukar mata da yaron na ka, sai ka bari har a wayi gari, a lokacin ta san komai a kan ka, ma'ana ta gan ka daga ka isai fatar jikin ka, to a lokacin sai na yarda, idan ka fita ka rufe mana d'akin." Gilashin ta ta cire ta aje ta yi wanciyar ta ta rufe har fuskar ta, da k'yar ya aje d'aya ledar ya fara taka k'afafun shi ya fice daga d'akin, har k'asan zuciyar shi yana jin ba dad'i, kuma ba ya fatan auren shi da Haseenah ya zama silar fara rubuta matsala a tarihin zaman shi da ita, dan Khadija ita ce farin cikin shi, haka ya sallama d'akin amarya ya same ta, da k'yar ya tattara nutsuwar sa ganin Haseenah na neman fahimtar halin da ya ke ciki, ita kuma dad'i ne ya kusa kashe ta saboda ganin halin da ya ke ciki, sun gabatar da duk abin da shari'a ta zo da shi amarya da ango suyi sunyi, bayan nan kuma su ka kwanta dan sauke gajiya, bai yarda ya yi nesa da ita, sai dai tabbas akwai wani bak'on al'amari, in dai har ya na gari bai tab'a raba shinfid'a da Khadija ba ko da kuwa sun samu sab'ani ne a matsayin su na yan adam, dan ko haihuwar Bilal ba su raba shinfid'a ba, haka mai tsohuwar da ta zo ta ke ganin rashin kunyar ta, haka dai ya rumgume ta har bacci ya d'auke shi. Kiran sallah farko Khadija ta tashi tare da Bilal dan gabatar da sallah, d'akin ta ta koma ta na shirin kabbarawa Usman ya shigo dan ya duba d'akin Bilal bai ganta ba, ba tare da ta had'a ido da shi ba tace "Ina kwana." Marairaicewa ya yi yace "Ina aka baro sauran mahad'in da ake had'a min da shi?" "Ban gane ba?" Ta fad'a ta na gyara hijab d'in ta, kallon ta ya yi yace "Kamar Abban Bilal, babban mutum, rabin rai, sarki, jarumin ki, da dai sauran su." D'agowa ta yi ta kalle shi da murmushi tace "Ina kwana jarumin namiji." Ta na fad'a ta kabbara sallahar ta, fita ya yi cikin rashin jin dad'i ya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117